Ya kamata marubuta su kafa ƙungiyar yaƙi da rubutun batsa – Hafsat A. Garkuwa

“Bincike ne zai samar wa marubuci kaso 50 na labarinsa”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Hafsat A. Garkuwa ba baƙuwa ba ce a tsakanin marubuta littattafan Hausa musamman waɗanda suke onlayin, kasancewarta ɗaya daga cikin haziqan marubuta da suke ba da gudunmawa ga wajen bunqasa harkar adabi da cigaban harshen Hausa. A hirar ta da wakilin Blueprint Manhaja, Hafsat ta bayyana tarihin yadda ta samu kanta a harkar rubutun adabi da kuma burinta na ganin gwamnati da shugabannin marubuta sun samar da wani haɗin gwiwa na yadda za a tsaftace harkar rubutu daga matsalar marubutan batsa. Ga yadda hirar ta su ta kasance.

MANHAJA: Ina son ki gabatar mana da kanki.

HAFSAT GARKUWA: To, Salamu alaikum. Ni dai asalin sunana Hafsat Ayuba, amma a yanar gizo an fi sanina da Hafsat A. Garkuwa. Ni marubuciya ce, sannan kuma ina tava kasuwanci, ina saye da sayarwa. Har wa yau kuma ina harkar soye-soyen kayan ƙwalama da girke-girke, wato catering. Ina da aure da yara biyu.

Ko za ki gaya mana tarihin rayuwarki a taƙaice?

Ni dai ƴar asalin Jihar Gombe ce, daga cikin garin Gombe. Na yi karatun haddar Alƙur’ani, har na yi sauka. Na kuma samu ilimin addini daidai gwargwado, har yanzu ma dai ina kan neman ilimi. Sannan na yi karatun boko tun daga matakin firamare har zuwa sakandire. Daga nan kuma na yi karatun neman ilimin malanta, inda na samu shaidar ilimi ta NCE, duk a cikin garin Gombe. Daga nan aka yi min aure, kuma Alhamdulillah. Ina da ƴaƴa biyu, mace da namiji.

Wanne abu ne ya faru a rayuwarki lokacin tasowarki wanda ya taimaka wajen inganta tarbiyyarki da tunaninki?

Tarbiyya da irin tsananin da mahaifiyata ta nuna min yayin tasowata, ta sa har a lokacin ina ganin mahaifiyata tana takura min sosai. Sai daga baya na gane ashe ƙoƙari take wajen ganin ta bani ingantacciyar tarbiyya, kuma Alhamdulillah, wannan burin na ta ya cika. Domin kuwa kulawar da na samu a wajen iyayena ita abin alfaharina a yanzu. Kuma duk abin da zan yi na rayuwa, ita nake tunawa.

Wanne abu ne ya sa ki ka fara sha’awar rubutun adabi?

Tun tasowata na kasance ni ma’abociyar karance-karancen littattafan Hausa ce, wanda shi ne ya ba ni sha’awa har na fara yin nawa rubutun ina yasarwa. Har kuma da na shigo yanar gizo sai na ga yadda ake wasa alƙalami sai hakan ya bani ƙwarin gwiwar shigowa a dama da ni nima.

Ko za ki iya tuna labarin farko da ki ka fara rubutawa?

E. Labarin da na fara rubutawa shi ne ‘Ƙuncin Rayuwa’.

Wane ne ya fara koya miki yadda za ki yi rubutu, ko nuna miki yadda za ki kiyaye ƙa’idojin rubutu?

Waɗanda suka dafa min a farkon fara rubutuna su ne Aisha Ali Garkuwa da kuma Ummu Affan su suka koyar da ni yadda zan yi rubutu da yadda zan saka kowacce kalma a muhallinta.

Wacce shekara ki ka fara fitar da rubutunki kuma kawo yanzu littattafai nawa ki ka rubuta?

Na fara fitar da rubutuna na farko a shekarar 2018, kuma zuwa yanzu na rubuta littattafai aƙalla za su kai 15.

Gaya mana sunayen littattafanki, kuma ki yi mana bitar fitattu uku a cikinsu.

Na farko kamar yadda na faɗa shi ne ‘Ƙuncin Rayuwa’, sai ‘Zamantakewa’, ‘Gidan Mijina’, ‘Doctor Hisham’, ‘Abinda Aka Gasa’, ‘Na Yarda In Mutu’, ‘Izaya’, ‘Taufeeq’, ‘Baqar Tukunya,’ ‘Girman ƙauye’, sai kuma ‘Ke Nake Gani’.

Littafin ‘Abinda Aka Gasa’ yana ɗauke ne da labarin wata yarinya da yayanta. Babansu ya kasance boka ne, sai ya sa shi wannan yayan nata ya yi wa mahaifiyarsa ciki aka haifeta. Amma sai ga shi jama’a gari ba su duba rashin laifinta a cikin wannan aika aikar ba sai suke nuna mata ƙyama da tsangwama, wanda hakan ya sa ko makaranta ba ta iya zuwa balle kuma a zo ga batun aure.

‘Izaya’ kuma labarin wata matashiyar yarinya ce da Allah Ya haɗa ta da wata muguwar uwar riƙo, wacce take gallaza mata, wannan ya sa ta yi nesa da duk wani farincikin duniya, hatta abincin da za ta ci sai ta je ta nemo leda ake zuba mata.

Shi kuwa littafin ‘Taufeeq’ na rubuta shi ne akan wani matashi wanda gigin kuɗi ya ruɗe shi har ya afka shan taba sigari, wanda a dalilin shaye-shaye har ya gamu da cutar da ta yi ajalinsa.

Shin kin tava buga wani littafi a cikin littattafanki ko dukka a onlayin ki ke sakewa?

Duk a onlayin nake fitar da su, sai dai ina sa rai nan gaba in sha Allahu zan buga wani ko wasu ma.

Wacce ƙungiyar marubuta ki ke, kuma wanne taimako ƙungiyar ke miki a rubuce-rubucenki?

Ina qungiyar ‘Women Writers Association ne ta mata zalla. Kuma babu shakka ƙungiyar na taimaka min da abubuwa da dama, musamman ma wajen yaɗa labarina zuwa wasu sassan na yanar gizo.

Waye a cikin marubuta ya zama miki madubin kwaikwayo a salon rubutunsa ko gogewarsa?

Aisha Aliyu Garkuwa ita ce allon kwaikwayona, don babu shakka rubutunta na birgeni matuqa.

Yaya alaƙarki take da masu bibiyar littattafanki, kuma ta yaya ki ke hulɗa da su?

Muna da kyakkyawar alaƙa a tsakanin mu babu kyara ko wulaƙanci, cikin girmamawa. Ina kuma ƙoƙari wajen ganin na basu duk wani lokaci na sauraresu tare da mutunta juna.

Shin wani makarancin littattafanki ya tava baki wata shawara da ta sa har ki ka canza wani tsari da ki ka yi wa labarinki?

E, to. Zan iya cewa haka ne, domin ko a cikin yadda suke sharhi kan wasu littattafaina ina riskar wasu shawarwari da suke sa na sauya akalar labarina, ko da ba ta hakan naso yi ba. Don ganin na basu abin da suke so, kuma zai ƙayatar da su har su cigaba da karanta littattafan da nake yi.

Yaya ki ke samun jigo ko basirar yin rubutunki?

A ko’ina basirar rubutu tana iya zuwa min. Ko da kuwa a cikin magana ne ana hira na kan iya samun jigon yin rubutu, ko ba da ni ake hirar ba.

Me za ki ce kan muhimmancin bincike ga marubuci?

Bincike wani abu ne mai kyau ko ma ba ga marubuci ba. Muddin kana marubuci bincike yana da matuƙar muhimmanci a gareka, domin shi ne zai samar maka da kaso 50 cikin cikin 100 na labarinka. Bincike shi zai fito maka da abin da ke ɓoye, wanda zai ƙara taimaka maka wajen isar da saƙon ka.

Wanne littafi ne rubutunsa ya fi baki wahala, kuma wanne ne ya fi miki sauƙin kammalawa, mene ne dalili?

‘Ƙuncin Rayuwa’ shi ne littafin da ya fi bani wahala, kasancewar shi ne littafina na farko. Don a lokacin ba komai na sani a kan rubutu sosai ba. Sai kuma in ce littafin ‘Taufeeq’ shi ne littafin da ya fi min sauƙin kammalawa, saboda labarin ya ɗarsu a zuciyata, kuma na samu duk wani abinda da nake buƙata na bincike akan labarin. Ina rubuta shi cike da shauqi, domin ɓangare ne na masoya mu ko duk inda soyayya take mu na wajen.

Yaya harkar rubutun adabi take a Jihar Gombe, akwai marubuta sosai ko ƙungiyoyin marubuta?

Gaskiya zan iya cewa har yanzu harkar rubutun adabi ba ta yi ƙarfi yadda ya kamata a Gombe ba. Na san dai akwai marubuta sosai da suka yi fice aka san su a duniyar adabi, amma samun haɗin kai da kusantar juna ya sa harkar ba ta bunƙasa. An sha yin ƙoƙari a baya don kafa ƙungiyar gamayyar marubuta, kamar na baya bayan nan akwai ƙoƙari da wasu marubuta suka yi na samar da ƙungiyar Gamayyar Marubutan Jihar Gombe ta GAMJIG, amma abin bai ɗore ba, saboda rashin haɗin kai. Akwai dai wasu marubuta da na sani, irin su Adamu Yarma, Rufa’i Abubakar, Sa’adatu Wazir Gombe, Aziza Gombe, Milhat wato Fadeela Yakubu, sai

Mrs Abdul, da kuma Sadiya Gombe. Waɗannan duk marubuta ne ƴan Gombe da suke ba da gudunmawa a harkar adabi. Ina fatan watarana za mu dunƙule mu zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya, kamar marubuta na sauran jihohi.

Su waye aminanki da ku ke zumunci sosai a cikin marubuta?

Ni dukkan marubuta nawa ne, muna zumunci da girmama juna. Sai dai an ce wata kusan ta fi wata. Daga cikin aminaina, ƴan hannuna da muke zumunci koyaushe akwai, Aisha J.B, Safnah Sani Jibiya, Fadeela Yakubu, Surayya B. Abdul, da Leemart Pinky.

Shin tun bayan fara rubutunki na kanki, kina samun damar karanta littattafan wasu marubutan?

E, ina ware lokaci musamman don yin karatu. Yanzu ma haka akwai littafin da na ke bi na Aisha Ali Garkuwa mai suna ‘In Da Rai.’

Wacce rawa manhajojin kasuwancin littattafai irin su Hikaya, arewabooks da YouTube ke taimakawa wajen inganta kasuwancin littattafai?

Gaskiya suna taka muhimmiyar rawa a gare mu, kuma suna taimaka mana wajen yaɗa littattafan mu har wasu ma su so su gani su zo, kuma su saya a wajen mu. Sai dai mu ce Alhamdulillah kawai.

Wanne alheri za ki iya cewa kin samu a dalilin rubutu wanda ba za ki manta ba?

To, zan iya cewa na samu alkhairai da dama, ko iya mutuntawa da kuma karramawa ma ina ganin babban alheri ne a gareni. Sai dai mu ce Alhamdulillah, Allah Ya kawo mana babban rabo.

Wane ƙalubale ne ya fi ci miki tuwo a ƙwarya a harkar rubutu, kuma yaya ki ke tunanin kawo gyara?

Babban ƙalubalena su ne masu rubutun batsa. A gaskiya wannan abu yana ci min tuwo a ƙwarya. Da so samu ne a buɗe wata ƙungiya ta haɗakar marubuta da haɗin gwiwar gwamnati, wacce riqa sa ido kan duk rubuce-rubucen da ake yi. Za ta kuma tilasta cewa duk wanda ya yi rubutu sai ya tura ƙungiyarsa an duba masa sannan zai fitar da shi. Idan an ga da kuskure kuma a umarci marubucin ya je ya gyara ko a hana fitar da shi.

Menene babban burinki nan gaba a harkar rubutu?

Ina son duniya ta sanni, in zama babbar marubuciyar da za ta iya tallafawa sauran marubuta na bayana.

Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarki?

Nan gani nan bari…

Na gode.

Masha Allah. Ni ma ina godiya ƙwarai da gaske.