Ya kamata matasa su himmantu wajen neman ilimi – Ƙungiyar masu motocin haya

Daga DAUDA USMAN a Legas

Shugaban ƙungiyar masu motocin haya da ɗaukar ma’aikata ta ƙasa wadda aka fi saninta da ‘Road Transport Employer of Nigeria’, Alhaji Musa Mohammed Mai Takobi Kano, kuma shugaban ƙungiya ta a birnin Legas, ya nemi matasan ƙasar nan da su zama masu ƙoƙarin neman ilimi tare da sana’o’in dogaro da kai domin kaucewa yawon gararanba a duk faɗin ƙasar nan.

Alhaji Mai Takobi ya nemi hakan ne a birin Kano a lokacin da yake zantawa da waɗansu wakilan kafofin yaɗa labarai na ƙasa kuma yake bayyana masu abin da ya zama wajibi ga matasan ƙasar nan dama al’ummar ƙasar baki ɗaya.

Mai Takobi ya ci gaba da cewar, samun ƙarin ilimin matasan ƙasar nan da sana’o’in dogaro da kai a daidai wannan lokaci zai taimaka wa ƙasar nan a wajen nema wa matasan aiki tare da kawo cigaban ƙasar nan gaba ɗaya.

Haka zalika nan, ya ci gaba da shawartar al’ummar ƙasar nan da su cigaba da gudanar da addu’o’in neman samun ƙarin zaman lafiya a Nijeriya da kewayenta baki ɗaya.

Sannan kuma ya bayyana irin nasararorin da ƙungiyarsa ta samu aƙarƙashin jagorancinsa a cikin ƙanƙanin lokaci, a cewarsa a halin da ake ciki yanzu ƙungiyar tana da shekaru arba’in da biyu da ƙirƙiro ta kuma tana da tsofafin shuwagabanni guda goma sha biyu waɗanda suka jagoranceta a Nijeriya a matakin shugabancin ƙasa, amma ƙungiyar ba ta taɓa samun ɗaukaka ko cigaba ba sai a wannan lokacin da yake jagorantar ƙungiya, inda a cewarsa a cikin watanni takwas kacal ƙungiyar ta samu ɗaukaka da cigaba.

Ya ƙara da cewa, baya ga ofishin da ƙungiyar ta mallaka na zamanta na dindindin a Abuja tare da katafariyar sakateriya wanda a cewarsa a yanzu haka suna ta shirye-shiryen kiran taron buɗewa a cikin watan Janairun 2022, mai zuwa.

Sannan ya ƙara da cewa, akan hakan ya ke ƙarayin kira ga shuwagabanin ƙungiyar a matakin shugabacin jihohin ƙasar nan da sauran mambobin ta da su ƙara ƙoƙari a wajen haɗa hannuwansu domin cigaba da gina harkokin ƙungiyar da ma ƙasar nan baki ɗaya.

Ya cigaba da cewa, kuma su kasance masu bin doka da odar ƙasar nan a kowanne lokaci tare da girmama jami’an tsaro alokacin da suka zo gudanar da aikinsu tare da sanya ido a wajen tantance kayan fasinja domin tabbatar da ƙarin tsaro a Nijeriya gaba ɗaya.

Sannan kuma ya shawarci fasinjoji masu ra’ayin hawa motar haya a wajar tasha da su kaucema hawan motocin haya a haramtattun wurare domin kare rayuwarsu, lafiyarsu da dukiyinsu bakiɗaya.