Daga CMG HAUSA
Jiya Laraba hukumar gudanarwar ƙungiyar tarayyar Turai wato EU ta kai ƙarar gwamnatin Birtaniya saboda rashin mutunta wasu tanade-tanaden da ke cikin yarjejeniyar Arewacin Ireland.
Madam Michelle O’Neil, mataimakiyar shugaban jam’iyyar Sinn Féin ta Arewacin Ireland, jam’iyyar da ke goyon bayan rabuwar Arewacin Ireland daga Birtaniya, ta nuna cewa, abun da gwamnatin Birtaniya ta yi ya ƙara tada ƙura a yanayin siyasar yankin Arewacin Ireland. Kwanaki 2 kafin wannan kuma, madam Nicola Sturgeon, babbar jami’in mahukuntan Scotland ta sanar da cewa, ko gwamnatin Birtaniya ta yarda ko a’a, za ta ƙara azama kan jefa ƙuri’a kan ficewar Scotland daga Birtaniya a shekara mai zuwa a Scotland.
Lallai abubuwan da Arewacin Ireland da Scotland suka yi sun ƙara damun gwamnatin Birtaniya, wadda ta dade tana fuskantar matsaloli da dama. Duk da haka, ‘yan siyasan Birtaniya suna tada zaune tsaye inda suke goyon bayan ƙasar Amurka, a yunƙurin ta da rikici a Turai da nahiyar Asiya da tekun Fasifik. Abin da suke sha’awa shi ne ta da rikici a duniya. Abun da suke yi, ya sa ƙasashen duniya na yi musu dariya.
Mai fassara: Tasallah Yuan