Ya kashe maƙwabcinsa kan wurin ajiye mota

Wani mutum ya soka wa makwacinsa wuƙa har lahira saboda gardama kan wurin ajiye mota.

Lamarin ya faru ne a yankin Ajah na Jihar Legas, kamar yadda kakakin ’yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin ya tabbatar.

Ya ce, rundunarsu ta tsare wani mutum mai shekara 41 da ya caka wa maƙwabcinsa wuƙa a ciki, ya kashe shi nan take, bayan sun samu saɓani kan wurin ajiye mota a kan layin Gbadamosi da ke Rukunin Gidaje na Badore a daren Asabar.

Hundeyin ya ce, an kai rahoton abin da ya faru ofishin ’yan sanda na Langbasa kafin wayewar garin Lahadi.

“’Yan sanda sun je sun ɗauki hoton abin da ya faru, kuma an kai gawar mutuwarin IDH da ke Yaba domin gudanar da bincike,” wanda ake zargin kuma ana tsare da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *