Ya lakaɗa wa lauya duka a kotu bisa tambayar ƙwaƙwa

Daga WAKILINMU

An ɗaure wani dattijo ɗan shekara 69 mai suna John Edward Njeru a gidan yari na tsawon kwana ɗaya, saboda ya lakaɗa wa lauya duka yayin da lauyan ke gudanar da tambayoyi a cikin kotun.

An bayar da rahoton cewa, tsohon Daraktan Ayyuka a ofishin ‘yan sandan Kenya ya bar lauyan, Alex Kimani, da munanan raunuka bayan da ya buge shi a ciki. An ce ya fusata cewa Kimani yana yi masa tambayoyi da yawa a cikin shari’ar da ya kasance mai shaida.

An ce, ƙarar tana tsakanin wani dattijo ne wanda ya zargi wani ɗan kasuwa, Gabriel Njoroge Mbuthia da laifin damfararsa ta hanyar yin jabun takardar shaidar mallakar fili a ƙaramar hukumar Nanyuki. Ana zargin ɗan kasuwar ya aikata laifin ne a ranar 21 ga Yuli, 2009.

An tattaro cewa, lamarin ya faru ne bayan da lauyan ya roƙi kotu da ta ba shi damar kusantar shaidan da ke zaune don nuna masa wasu takardu. An tilasta wa kotun ta bada umarnin tsare shaidan yayin da ya nakaɗa wa lauyan duka har ta kai kai shi asibiti domin duba lafiyarsa.

Abokin aikinsa, Waweru Benson wanda ya bayyana a gaban kotun a ranar Talata 28 ga watan Satumba, ya shaida wa babban alƙalin kotun Bernard Ochoi cewa, Kimani ba zai iya zuwa kotu ba tun da har yanzu yana fama da matsanancin ciwon ciki.

Benson ya ce, “Bayan abin da ya faru jiya, abokin aikina (Kimani) ya sami rauni sosai a cikinsa. Ya ziyarci asibiti domin a duba lafiyarsa inda na ke tsammanin yau ma za a yi masa scanning da safe don gano musabbabin ciwon.

Wanda ake tuhuma yana da damar gabatarwa kuma babu wanda zai iya dakatar da wannan wakilci ko ta baqin baki ko hari kamar yadda ya faru jiya. Babu wanda ya fi ƙarfin doka. Ina da bayanin cewa mai ƙarar ya yi amfani da kalaman ɓatanci ga mai gabatar da ƙara a wata kotun da ta gabata.”

Benson ya buƙaci masu gabatar da ƙara da su shiga cikin masu ƙare kansu wajen yin Allah wadai da matakin sannan kuma ya nemi kotun da ta bayar da umarnin tsare Njeru na tsawon kwanaki har sai an kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda.

Alƙalin kotun ya ce, “Bayan mummunan abin da ya faru jiya wanda wani mai shaida ya fuskanci lauya a zahiri, na umarci a tsare shaidan na kwana ɗaya. Na lura cewa lauyan ba shi da lafiya saboda abin da ya faru kuma ina roƙonsa da ya kai rahoto ofishin ‘yan sanda mafi kusa don jami’an su gudanar da bincike tare da gabatar da rahoto a kotu.

“Ba za a yarda da wannan matakin ba a wannan kotun kuma an hukunta shi sosai.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *