Ya maƙale a tayar jirgin sama daga Afirka ta Kudu zuwa Holland

’Yan sandan Holland sun ce, sun samu wani mutum da ya maƙale a tayar wani jirgin sama da ya tashi tun daga Afirka ta Kudu ya sauka a Amsterdam da ke ƙasar a raye.

Jiragen sama dai na tafiyar sa’a 11 daga Johannesburg zuwa Amsterdam, kuma wannan jirgin na dakon kaya ana ganin ya yada zango sau ɗaya ne kawai a Nairobi a ƙasar Kenya.

“Abu ne mai wuyar gaske ga mutumin da ya maƙale a tayar jirgin sama ya rayu a doguwar tafiya, saboda tsananin sanyi da kuma ƙarancin iskar shaƙa a sama. Ba a riga an gane shekaru da ƙasar mutumin ba,” inji ’yan sandan.

Kakakin ’yan sandan Holland, Joanna Helmonds ta bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, “sn samu mutumin da ransa a ramin tayar gaba na jirgin, kuma an ɗauke shi zuwa asibiti cikin hayyacinsa.

Ta ce, “abu ne mai matuƙar ban mamaki ganin cewa mutumin yana raye, yanzu dai ana kula da shi a asibiti.”

Ta ƙara da cewa, ana sa ran mutumin zai nemi mafaka a Holland, amma dai abu mafi muhimmanci a yanzu shi ne kula da lafiyarsa.

Kakakin Kamfanin Jirgin Saman Dako na Cargolux na Italiya, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa, jirgin wanda ya taso daga Johannesburg zuwa filin jirgin Schiphol da ke Holland ya yada zango a Nairobi.

Abin da ba a sani ba shi ne ko a Afirka ta Kudu mutumin ya maƙale a jirgin ko a Kenya, yanzu dai ’yan sanda suna gudanar da bincike a kai.