‘Yan sanda sun cafke waɗanda ake zargi da kai wa tawagar Gwamnan Kaduna hari

Daga WAKILINMU

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta cafke wasu da ake zargin mabiya Shi’a ne da ake zargi da kai wa tawagar Gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, hari.

Sanarwar da Kakin rundunar, DSP Mohammed Jalige, ya fitar ta ce jami’an da ke bai wa tawagar Gwamnan kariya ne suka tsaftace yankin Bakin Ruwa da ke Rigasa, Babban Hanyar Nnamdi Azikiwe bayan da mabiya Shi’a suka kai hari tare da hana wa jama’a zirga-zirga a yankin.

Ya ce an kama ‘yan dabar ne yayin da suke takura wa mazauna yankin a daidai lokacin da tawagar gwamna ta isa yankin da misalin ƙarfe 3 na rana a ranar Alhamis.

Ya ƙara da cewa, ‘yan dabar sun shiga harbi da makamai da duwatsu ne bayan da suka hangi isowar tawagar Gwamnan.

Ya ce a wannan hali, cikin ƙwarewa jami’an tsaro suka daƙile su ba tare da amfani da ƙarfin makami ba, sannan an tsare wasu da ake kyautata zaton mabiya Shi’a ne, kuma an fara bincike kan batun.