Kwanan nan ne wani bidiyo na wani mutum ɗan ƙasar Philippines ya ɗauki hankalin jama’a a intanet.
A cikin bidiyon, mutumin ya shafa sufa-gilu a laɓɓansa a matsayin wani ɓangaren na wasan barkwanci, amma lamarin ya sauya zuwa wani abun daban.
Mai wasan barkwanci ya liƙe laɓɓansa bayan da ya shafa musu gam ɗin sufa-gilu a yayin da yake yin bidiyo kai-tsaye domin ƙayatar da masu bibiyarsa.
Mutumin ya shafa gilu ne, inda ya manne laɓɓansa, wanda cikin dakika kaɗan, mannewar ta kama fatar laɓɓan kamar yadda ya so, inda hakan ya sa yabar laɓɓansa a rufe sosai.
A zamanin da ake amfani da shafukan sada zumunta na zamani, mutane sukan yi iyakacin ƙoƙarinsu don samun mabiya da sakonsu zai kai gare su a intanet.
Raye-rayen zuwa abubuwan barkwanci, suna yin tasiri a shafukan sada zumunci na zamani.
Bidiyon da tashar Talabijin ta Badis TV ta yaɗa a shafin Insitagaram ya nuna wani mutumi zaune a cikin shago, riƙe da robar sufagilu kuma cikin wasa yana nuna kansa a kyamara.
Yana shafa shi, yana mannewa a leɓɓansa, amma cikin daƙiƙa kaɗan, mannewa ta kama fatun laɓɓansa yadda yake so, hakan dole ya sa ya bar laɓɓan a rufe sosai.
Da farko, mutumin ya bayyana yin hakan a matsayin nishadantarwa, yana dariya kamar ya yi nasara. Sai dai dariyarsa ta koma kuka, inda ya yi ta ƙoƙarin buɗe baki.
Nishadantarwarsa ta rikiɗe zuwa firgici lokacin da ya gane laɓɓansa ba za su rabu ba, duk ya yi ƙoƙarin yin hakan.
Bayan wani lokaci sai hawaye hawaye suka fara gangarowa a fuskarsa yayin da yanayin ya yi tsanani, wanda hakan ya sa shi cikin damuwa.
Bidiyon ya sami ra’ayoyi sama da miliyan 6.7 na mabiya shafin kuma ya haifar da martani da yawa daga masu amfani da kafofin sada zumunta na zamani.