Ya yi wa ɗiyar abokinsa ’yar shekara 13 fyaɗe

Daga WAKILINMU

Hukumar Tsaro ta NSCDC ta sanar da kama wani ɗan shekara 20 kan zargin yi wa yarinya mai shekara 13 fyaɗe a Jihar Nasarawa.

Kakakin NSCDC reshen jihar, DSC Jerry Victor ya ce, mutumin da ya yi wa yarinyar fyaɗe ya sanya ta samu juna biyu a Lafiya, babban birnin jihar.

Haka kuma, NSCDC ta ce, ta kama wasu mutum biyu daban da zargin lalata da wata ’yar shekara 13.

Da ya ke gabatar da su a gaban manema labarai, DSC Jerry Victor, ya ce, an kama mutanen ne a wurare daban-daban na jihar.

“Waɗanda ake zargi sun amsa laifinsu na yi wa yarinyar mai shekara 13 fyaɗe,” a cewarsa.

Ya ƙara da cewa, ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi da yi wa yarinyar fyaɗe abokin mahaifinta ne.

Yarinyar ta shaida wa manema labarai cewa, mutumin ya yi lalata da ita ne bayan ya kira da zummar zai aike ta.