Ya zuwa yanzu Amurka ta kau da kai daga abin baƙin ciki da ke faruwa a cikin gidanta

Daga CMG HAUSA

Kwanan baya, shehun malama a fannin ilmin doka Amy Wax daga jami’ar Pennsylvania ta ƙasar Amurka, ta soki Amurkawa ‘yan asalin Indiya a cikin wani shirin gidan telibijin na Fox News, inda ta ce, ƙasarsu ta kasance abin kunya. Kalamanta sun girgiza mutane sosai, kuma wani misali ne na yadda ake nuna bambanci ga Amurkawa ‘yan asalin ƙasashen Asiya a ƙasar Amurka.

Sin kullum Amurka ba ta kan yi shelar nuna daidaito a tsakanin kowa da kowa ba? Me ya sa Wax ta nuna wariyar launin fata a fili? Yau Jumma’a hukumar nazarin haƙƙin dan Adam ta ƙasar Sin ta kaddamar da rahoto mai taken “yadda ake nuna bambanci ga Amurkawa ‘yan asalin ƙasashen Asiya, ya nuna ainihin gaskiyar zaman al’ummar Amurka mai cike da wariyar launin fata”, wanda ya ba mu amsa.

Rahoton ya yi amfani da bayanai da misalai masu tarin yawa wajen bayyana cewa, ƙasar Amurka, wata ƙasa ce dake rinjayen fararen fata. Ana cin zalin Amurkawa ‘yan asalin ƙasashen Asiya da sauran ‘yan kananan ƙabilu a fannin haƙƙin ɗan Adam.

Cikin shekaru fiye da ɗari 2 da suka wuce, Amurka ta samu bunƙasar tattalin arziki bisa ƙoƙarin da Amurkawa ‘yan ƙasashen waje. Amma gwamnatocin ƙasar ba su kula da su ba. ‘Yan siyasan ƙasar suna iƙirarin kiyaye haƙƙin dan Adam da cimma mafarkin Amurka, ta hanyar cin zalin Amurkawa ‘yan ƙananan ƙabilu.

Mai fassara: Tasallah Yuan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *