Ya zuwa yanzu Amurka tana rura wuta tsakanin Rasha da Ukraine

Daga CMG HAUSA

Ranar 14 ga wata, an cika wata guda da fara yin musayar wuta a tsakanin ƙasashen Rasha da Ukraine. Shugaban ƙasar Afirka ta Kudu Matamela Cyril Ramaphosa, da sauran al’ummun ƙasa da ƙasa suna ganin cewa, ainihin dalilin da ya sa ake zaman dar dar a tsakanin Rasha da Ukraine shi ne shigar da ƙasashe tsoffin mambobin Soviet, da ƙasashen tsakiya da gabashin Turai cikin ƙungiyar tsaro ta NATO a shekaru da dama da suka wuce. Ƙasashen yammacin duniya, musamman ma ƙasar Amurka sun dauki alhakin yaƙin.

Duk da suka da aka sha yi, amma Amurka tana ƙara rura wutar yaƙin, a yunƙurin ganin Rasha da Ukraine sun ci gaba da yaƙi a tsakaninsu.

Kwanan baya, shugaba Joe Biden na Amurka ya fara ziyara a ƙasashen Turai. Amurka ta yi shelar cewa, a yayin ziyararsa, za a tabbatar da sabbin matakai kan Rasha, ciki har da sabbin matakan sanya wa Rasha takunkumi. Yanzu an cika wata guda da yin musayar wuta a tsakanin Rasha da Ukraine. Idan Amurka ta haɗa hannu da ƙawayenta na yammacin duniya, wajen tsananta takunkuman da za su sanya wa Rasha, to, za a ƙara rura wutar yaƙin, kuma kowa zai fahimci maƙarƙashiyar Amurka ta haifar da tashin hankali a duniya.

Abin da ya kamata a lura da shi shi ne, Jake Sullivan, mai ba da taimako ga shugaban Amurka kan harkokin tsaron ƙasa, ya ambato ziyarar Biden a Turai da cewa, rikicin da ke tsakanin Rasha da Ukraine ba zai kawo ƙarshen cikin hanzari ba. Lallai wannan shi ne manufar da Amurka ke neman cimmawa.

Tana ingiza ci gaba da yin yaki a tsakanin Rasha da Ukraine, a yunkurin muzgunawa Rasha, da dakile Turai, da kawo wa rukunonin masana’antun aikin soja riba, da inganta yin danniya a duniya.

Fassarawa: Tasallah Yuan