Yadda ƙabilar Toraja ke daraja gawa fiye da mutum mai rai

A wannan mako, jaridar Manhaja ta kewaya duniya, inda ta yada zango a ƙasar Indonesiya da ke yankin Asiya. A yau filin namu ya yo tattaki na musamman ne zuwa yankin Gabas ta Tsakiya, inda mu ka yi nazarin al’adar wata ƙabilar mai suna Toraja.

Wani abu mafi ɗaukar hankali ta yadda har idon duniya ya ɗarsu a kan waɗannan al’umma shi ne yadda su ke tafiyar da sha’anin gawa ko kuma mu ce mamaci. Su dai waɗannan mutane su na rayuwa ne a cikin duwatsun da ke Kudancin Sulawesi na Ƙasar Indonesia, Kalmar ‘Toraja’ ta samo asali daga yaren ‘Buginese’ ‘Riaja’, wanda ya ke nufin mutanen kan dutse.

Addininsu:
Akasarin waɗannan bayin Allah suna koyi ne da addinin Kiristanci, yayin da wasunsu kuma suka kasance Musulmi, bayan waɗannan addinai biyu kuwa wasu daga cikin mutane sun yi imani da addinin bautar dabbobi, wanda aka fi sani da ‘Aluk’ (hanya). Wani abin al’ajabi kuwa shi ne, mutanen sun yi imani cewa, Ubangizansu sun sauko ne daga sama, da taimakon tsani, a cewarsu. A wannan lokacin shi ne hanya mafi kusanci ko kuma sauƙi wajen sadarwa tsakanin al’ummarsu ta Toraja da kuma Ubangizansu.

Mutanen Toraja suna auren mace ɗaya, duk da kasancewar a wani zamani da ya shuɗe masu sarauta ko mulki suna da damar auren mace fiye da ɗaya. Ita ma macen tana da damar auren namiji fiye da ɗaya. Sukan yi aure na haɗa ka, ma’ana haɗin iyaye ko wasu manya, sannan namiji yana da damar ya ga mace ya ce, yana so. Wato ma’ana sukan yi kuma auren zaɓi. Ba su amince da auratayya tsakanin ’yan’uwa na kusanci ba, sai dai na nesa. Amma a wani zamani can baya sukan yi auratayya tsakanin ’yan’uwa mafi kusa, ta hanyar sadaukar da jinin dabbobi. Sun yarda da saki a cikin aure kuma wanda ya yi saki ko wacce aka saka za ta iya yin sake aure.

Wani abin ban mamaki dangane da wannan al’umma shi ne yadda suke tafiyar da mamaci. Su dai waɗannan al’umma babu abin da suka fi karramawa kamar gawa. Sukan ɗaukaka mamaci fiye ma da wanda yake raye. Idan mutum ya mutu akan share sati, wata ko ma shekara ba tare da an bisne shi ba. Duk tsawon lokacin mamaci zai ɗauke su tare da iyalansa kamar lokacin da yake raye. Hikimar yin haka, shi ne, domin su sami wadataccen lokacin da za su tara abin da za su yi bikin bisne mamacin da shi. Sukan yi amfani da wani sinadari nasu da zai hana mamacin ruvewa ta hanyar zubawa mamacin.

Biki ne ake yinsa gagarumi na gani na faɗa wanda ke samun halartar ’yan’uwa, abokan arziki, da kuma iyalan mamacin. Sukan ɗauki tsawon kwanaki ko satattaki domin gudanar da wannan biki da suke kira ‘Rambu salong’ ya yi gudanar da bikin za a yanka manya-manya bijimai da aladu. Bayan an yayyaanka sai a sarrafa naman sannan a rarraba wa mutanen da suka halarci bikin bisa la’akari da matsayinsu.

Rana ta goma sha ɗaya da wannan biki ita ce ranar da ta yi daidai da lokacin da za a binne mamacin. Za a tona cikin duwatsa a bisne gawar, sannan sai a yi amfani da ƙaho irin na dabbobin da aka yanka wajen bikin, wajen ƙawatar da kabarin, yayin da wasu kuma daga cikin ake jerewa domin kwalliya a ƙofar gidansu mamacin. Yawan ƙahonin da aka yi amfani da su domin ƙawata gurin shi ke tantance iya matsayi ko girman mamacin.

Sai dai kuma ba a nan gizo ke saƙar ba, ɗaya daga cikin al’adarsu ita ce tono mamaci daga inda aka bisne shi bayan kowacce shekara ɗaya, yayin da duk shekara ta zagayo za a tono gawar sai a dawo a sake wani gagarumin bikin. Yayin da aka sheƙa wa mamacin kwalliya ta musamman, daga bisani a mai da shi makwancinsa a rufe.

Daga cikin waɗannan ƙabilar kuma akwai waɗanda su sam ba sa bisne gawa, a madadin haka kuwa, sai a tabbatar an zuba masa wannan sinadari ta yadda ba zai ɓaci ba. Kana a sanya shi cikin wani ɗaki da aka tanadar dominsa bayan an yi masa kwalliya ta kece raini. Yayin da lokaci bayan lokaci akan buɗe ɗakin a ciro mamacin sannan a sake yi masa kwalliya a mayar da shi, Ikon Allah ikon gaske!

Haka dai rayuwar wannan ƙabila ta Toraja ke kasancewa a duniyar nan. A yayin da wasu ke ganin da zarar ran mutum ya fita daga jikinsa gawarsa ba ta da wani amfani illa a yi sauri a binne ta, su kuwa gawar ita ce mafi alfanu a wurinsu bisa la’akari da irin gatan da suke ma ta. Wannan shi ne babban abin al’ajabi.