Yadda ƙalubalen satar fasaha ke barazana ga cigaban adabi

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Hauwa Salisu, da ake yi wa laƙabi da Haupha, marubuciya ce daga Jihar Kaduna, yayin da ta fara aikin wani littafin ta mai suna ‘Da Aurena’ ba ta taɓa tunanin rubutun zai iya fuskantar tangarɗa ba, ganin irin yadda masu karatu suka karɓi littafin, saboda da salo na jan hankali da ta yi amfani da shi. Kwatsam, ran nan sai wata marubuciya daga ƙungiyarsu ta Kainuwa ta sanar da ita cewa ana ɗora labarin ta a wani zaure da ke manhajar Facebook, amma ba tare da sunan littafin ba kuma ba da irin bangon da ta tsara masa ba.

Ba tare da wata wata ba Haupha ta shiga bincike zaure zaure tana neman inda ake mata wannan ɗanyen aikin, cikin ikon Allah kuwa ta yi kacivis da shi a wani daga cikin zaurukan da ake ɗora littattafan Hausa a Facebook har an canza masa suna zuwa ‘Saudat’ kuma an cire sunan ta a matsayin marubuciya. Nan da nan ta nuna ɓacin ranta a kai bayan ta bayyana kanta a matsayin marubuciyar da ke da haƙƙin mallakar wannan littafin tare da nuna musu hujjar bangon littafin da ta tsara. A nan ne kuma wata ke gaya mata ai wannan labarin ana can ana cigaba da sake shi a wani zauren na daban. Haka ta yi ta jelen neman waɗanda suke da alhakin wannan satar fasaha, inda ta bayyana rashin jin daɗin ta, kuma aka yi sa’a suka amince da kuskuren su, suka canza littafin ya koma sunan da ta sa masa ‘Da Aurena’ aka kuma rubuta sunan ta a matsayin marubuciya.

Sai dai, a cewar marubuciyar, ashe bayan wannan tataɓurzar da aka yi akwai wata jiƙaƙƙiya a ƙasa, domin kuwa ba a jima ba sai ga labarin wani kuma yana can yana cinikin littafin nata a Naira ɗari biyar biyar, wannan kam sai da ƙungiyar su ta Kainuwa ta shiga tsakani kafin ya nuna nadamar sa kuma ya amince zai biya ta wani abu, duk da yake dai ta ce, ba ta karɓi ko kwabo a hannun sa ba, ganin yadda ya amsa kuskurensa sai kawai ta ce ta yafe masa.

Wannan ɗaya kenan daga cikin ɗimbin koke koken satar fasaha da binciken jaridar Blueprint Manhaja ya gano, albarkacin bukin Ranar Littafi Da Kare Haƙƙin Marubuta ta Duniya ta shekerar 2022 da aka gudanar a ƙarshen makon da ya gabata, 23 ga watan Afrilu, ranar da aka ware domin tunawa da gwagwarmayar da marubuta a faɗin duniya ke yi na samar da rubuce rubucen littattafai, domin ilimintarwa, nishaɗantarwa da faɗakar da al’umma.

A dalilin wannan matsala ta satar fasaha da ake kuka a kai, wasu marubutan sun ce gwiwarsu har ta fara sanyi kan harkar rubutu, domin suna ganin ba zai yiwu su vata hankalin dare suna ƙirƙirar labari wani ko wata a can gefe suna ɗaukar rubutun suna cin gajiyarsa babu izini ba. Kamar dai yadda ya faru da marubuciyar littafin, ‘Haka So Yake’ Rabi’atu S.K Mashi ýar Jihar Katsina, wacce wani gwanin satar fasahar ya juya labarin su na haɗin gwiwa da suka rubuta tare da wani marubuci Abdul Jega daga Jihar Kebbi, wanda ya mayar da shi nasa, ya canza sunan marubutan da na jaruman labarin. 

Dambarwar da ta biyo baya tsakanin ɓarawon fasahar da ýan ƙungiyar marubuta ta Nagarta ya sa ta ji sam labarin ma ya fita a ranta, dole ya sa ta jingine cigaba da rubutun da suke yi, ba a son ranta ba. 

Marubuciya Asma’u Abubakar Musa mai laƙabi da Jasmine, daga Jihar Filato, wacce ta rubuta littafin ‘Baƙar Tafiya’ ta bayyana ƙalubalen da marubutan yanar gizo (online) ke fuskanta, inda ta ɗora alhakin hakan kan son zuciya da lalaci da ke sa wasu ɓatagari da bai dace a kira su marubuta ba, suke sa kansu cikin wannan mummunar halayya ta satar fasaha, sai sun jira wani ya fitar da littafinsa sai su ɗauka su cire sunansa ko su sauya wani abu kamar sunayen jaruman labarin ko gari.

Marubuciyar littafin ‘Haɗuwar Zuciya’ Nana Basira Musa daga Jihar Sakkwato, wacce ake kira Momin Fadila, ita ma haka ce ta faru da ita, inda wata marubuciya (a yanzu) ta ɗauke labarinta ta juya sunayen jaruman labarin biyu, garin da suke, da kuma tsarin zamantakewar iyayen, sannan ta canzawa littafin suna. 

Marubutan da aka yi wa irin wannan kan-ta wayen suna da yawa, kowanne da irin salon yadda aka ɗauki hakkin mallakarsa aka juya ta zuwa na wani. Wani lokaci har ta kai ga faɗa wa juna baƙaƙen maganganu da cin mutunci, idan an tava littafin masu zuciya a kusa ko waɗanda suka san zafin haƙƙinsu. 

Abin mamaki ne kuma ka ji cewa a wajen satar fasaha wani lokaci har da wasu marubuta na asali da sunan su ya yi fice a harkar rubutu, inda suke ɗaukar labarin sabon marubuci ko marubuciyar da ta tuntuɓe su don neman shawara, kan yadda za ta inganta labarin, kafin sabuwar marubuciyar ko marubucin su ankara sai ka ga waccan fitacciyar marubuciyar ta yi wuf ta sake wannan labarin da aka je mata da shi don neman shawara, yayin da ta canza wasu sunaye, ko garuruwa. Wannan marubuci shaida ne na yadda wata baƙuwar marubuciya Sadiya Abdullahi daga Jihar Filato ta rubuta littafi mai suna ‘Da Kamar Wuya’, amma wata fitacciyar marubuciya a Jos ta yi mata yankan baya, bayan da ta ji salon labarin ya burge ta. 

Abin da yake qona wa marubuta irin su Nana Khadija Sha’aban marubuciyar littafin ‘Daren Aurena’ daga Jihar Kano da Rabi’atu Ahmad Mu’azu marubuciyar littafin ‘Matar Manya’ da ke Jos waɗanda suka koka da yadda satar fasaha ke gurgunta cigaban rubutun adabi, saboda yadda ake samar da ruɗani ga masu karatu a kasa gane wanene asalin mai labarin, kuma hakan na daƙile amfani da basira wajen rubutu tun da kowa ma zai iya satar labarin wannan ya mayar da shi na wancan. 

Wani salon satar fasahar kuma shi ne na ɗaukar labarin marubuci ko marubuciya a juya shi zuwa sauti, wato a riƙa karanta wa ana ɗora wa a YouTube ba da sanin marubuci ba, har ya kai wani tsawon lokaci da mai karanta labarin zai riqa samun maqudan kuɗaɗe, yana ci da gumin marubuta, ba da sanin su ba. Shi ma wannan babban ƙalubale ne da ya taso wa duniyar marubuta, kuma yake ci wa marubuta da shugabannin su tuwo a ƙwarya. 

Malam Ibrahim Indabawa shi ne shugaban ƙungiyar marubuta ta ANA a Jihar Kano, ya kuma bayyana wa jaridar Manhaja cewa, wannan mummunar halayya ta satar fasaha ita ce babbar matsalar da harkar rubutun adabi ke fuskanta a wannan zamani fiye da kowanne lokaci a baya. Kuma wannan tsarin karatun littafi da murya ya ja hankalin masu karatu sosai, tun da suna ganin ya fi musu sauƙi a maimakon ɓata lokacin karatu, ko da suna wasu ayyukan ma ba zai hana su sauraron labaran ba, kamar dai suna ji ne daga rediyo. 

Sai dai a ganin Mubarak Idris Abubakar, shugaban ƙungiyar Gamayyar Marubutan Jihar Kano, kuma marubucin littafin ‘Rumfar Kara’, satar fasaha ta hanyar karanta labarin da wani ya rubuta ba wata illa ba ce da za ta iya gurgunta cigaban rubutun adabi. Ya ce, “in dai rubutun da na yi, jigonshi babban saƙo ne na kawo gyara ga al’umma, ba na ganin koma baya ne don wani ya saci fasahata ya saka sunanshi ya yaɗa labarin. Dalili kuwa, ƙila ya fi ni ido da mutanen da za su karanta, wanda ka ga in sun karanta za su ƙaru, saboda daman don su ɗin aka yi.”

Wannan ra’ayin na Dakta Mubarak kamar yadda aka fi sanin sa, ba shi da farin jini a tsakanin marubuta, musamman irin su Hajara Ahmad Maidoya da ake kira Oum Nass daga Jihar Jigawa, marubuciyar littafin ‘Inuwar Gajimare’ wacce wani mai satar fasaha ya ɗauki littafin ta ‘Jini Ya Tsaga’ ya sa ana karanta wa a shafin sa na YouTube, sai da ƙyar aka shawo kan matsalar, inda wata marubuciya da ke da kusanci da shi ta sa ya biya Hajara kuɗin littafin ta, a matsayin ta sayar ma sa hakkin ya riƙa karantawa. 

Sai dai ba kamar Oum Nass ba, ita Aisha Adam daga Jihar Kano, mai laqabi da Ayshercool, labari ta samu na yadda wani gwanin satar fasahar ke cin kasuwar littafin ta mai suna ‘Aqidata’ wanda ta fara samun alheri a kansa, amma shi kuma gogan ya xauke ba neman izini ya je yana karanta wa a shafin sa na YouTube, a haka ta ƙaraci neman sa da takaicin abin da aka yi mata ta haƙura, don ba ta san inda za ta same shi ko lambarsa ba. Kamar abin da ya faru da marubuciya Zainab Usman Kumurya, da ita ma aka ɗauke littafinta ‘Abin Da Ka Shuka…’ aka sa a YouTube, kuma ba ta san wanda ya yi mata wannan yankan bayan ba. 

A yayin da ake koka wa da hawan ƙawara da satar fasaha da masu karanta littattafai a YouTube ke yi wa marubutan adabi wani daga cikin masu wannan harkar wanda kuma shi ma marubuci ne da ya rubuta littafin ‘Akan Novel’ Abdul Junaidu da ake yi wa laƙabi da ɗan Salma, daga Jihar Borno ya bayyana cewa, suna neman izinin marubuci ko marubuciyar littafin da suke son karantawa, idan sun san su ko sun samu lambar su, amma idan ba su samu izini ba saboda rashin samun damar yin magana ko da sun fara karantawa, daga baya mai littafin ya ji har ya tuntuɓe su ana iya sasantawa. 

Bangon litattafan Hausa

Hajaru Baba Abdullahi marubuciya kuma ýar jarida da ke aiki a tashar rediyo ta Vision FM a Jihar Sakkwato ita ma ta buxe irin wannan shafi na YouTube tana karanta littattafan Hausa, ta kuma ce ba ta karanta littafi sai da izinin mai shi. Kuma sau da dama sai ta biya marubutan daga Naira dubu uku zuwa dubu biyar, kafin ta fanshi izinin karanta littattafan a shafin ta na YouTube. A ganin ta babban kuskure ne mutum ya ɗauki hakkin mallakar wani ya yi amfani da shi ba bisa izini ba. 

A cewar Rabi’atu Mu’azu daga Jos, mai littafin ‘Sanadin Besty’, satar fasaha tamkar cin amanar marubuci ne, da ke kashe gwiwar marubuta su ji kamar cigaba da rubutun ma ba shi da amfani. Yayin da wasu marubutan ke bayyana ɓacin ransu da halayyar masu satar fasaha, ita kuwa Momin Fadila Nana Basira daga Jihar Sakkwato ƙoƙari ta yi ta gano wacce ta sace mata littafin, ‘Haɗuwar Zuciya’ ta yi mata nasiha da nuna mata muhimmancin kiyaye hakkin mallakar wani tare da ɗora ta a hanyar rubuce rubuce ta yadda ita ma za ta iya rubuta nata littafin na kanta. Kawo yanzu zumunci mai qarfi ya ƙullu tsakanin su, kuma ita ma ta shiga sahun marubuta da ke alfahari da basirarsu. 

Amma duk da haka wasu marubuta irin su shugaban ƙungiyar marubuta ta ANA a Jihar Kano, Malam Ibrahim Indabawa na ganin samar da ingantaccen tsarin da zai mayar da rubutu ko ayyukan marubutan da ke ƙarƙashin ƙungiyar zuwa salon zamani, don sayarwa ga masu buƙata, ba sai ya je hannun wani ƙato ci ma zaune ya sayar musu ba tare da sun samu komai ba, shi ne yanzu abin da ƙungiyar ANA ke kan tattaunawa a kai, domin kawo sauƙin abin. 

Shi ma shugaban ƙungiyar Gamayyar Marubutan Jihar Kano, Mubarak Idris Abubakar, ya bayyana buƙatar samar da haɗin kai tsakanin ƙungiyoyin marubuta, domin fitar da ingantaccen tsarin da zai kiyaye hakkin marubuta da fasaharsu. Ƙarƙashin haɗin gwiwar Hukumar Tace Finafinai da Ayyukan ƙirƙira ta Jihar Kano, da nufin tsaftace makomar harkar adabi. Shawarar da ta samu karvuwa a wajen akasarin marubuta, irin su Sumaiyya Babayo Abdullahi marubuciyar littafin ‘Aminta’ daga Jihar Filato da Momin Fadila daga Jihar Sakkwato da ke ganin lallai ne a samar da tsarin da zai zama karɓaɓɓe ga sauran marubuta, ba kawai na Jihar Kano ba har da ɗaukacin Nijeriya. 

Sai dai wani abin albishir ga ɗaukacin marubutan Nijeriya ba ma na Hausa kaɗai ba shi ne, a kwanan nan Babban Daraktan Hukumar Kula da Hakkin Mallaka ta ƙasa (NCC) Mr John Asein, ya sanar da wani shiri da hukumar take yi na fitar da wani tsari da zai kula da kare haƙƙoƙin marubuta da masu fasaha bisa la’akari da sabbin canje canje da ake samu a duniya sakamakon ɓullar sabbin hanyoyin fasahar sadarwa na zamani da suka mamaye yanar gizo, domin daƙile duk wasu da za su nemi tauye haƙƙin wani marubuci ko mai ƙirƙira ta amfani da yanar gizo.