Yadda ƙananan hukumomin Katsina suka raya yankuna karkaka ƙarƙashin Gwamna Raɗɗa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

A cikin shekaru uku da suka gabatar, ƙananan hukumomin Jihar Katsina sun yi rawar gani wajen samar ma al’umomi mazauna yankunan karkara romon dimukraɗiyya ababen more rayuwa, kama daga ta hanyar inganta rayuwarsu da samar musu ababen more rayuwa a fannoni daban-daban, kamar kiwon lafiya, ruwan sha, ilimin da bunƙasa fannin noma da kiwo, da gina hanyoyi da magudanan ruwa da samar da wutar lantarkin da sauransu.

Samar da waɗannan ayyuka, manyan da ƙananansu, sun taimaka gaya wajen bunƙasa tattalin arzikin yankunan karkara da samar da ayyukan yi da rage fatara da inganta sufiri da lafiya da cigaba mai ɗorewa, wanda hakan ya taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.

Waɗannan ayyukan sun yiwu ne, saboda kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin gwamnatin jihar da na ƙananan hukumomi, inda ake haɗa hannu a aiwatar da wasu ayyukan tare, kamar samar da tallafi ga mabuƙata da ciyarwa a watan Ramadan da ayyukan samar da tsaro da makamantansu.

Har ila yau, gwamnatin Jihar Katsina da ƙananan hukumomin suna da wani tsari na tafiyar da ayyuka bai-ɗaya ta yadda al’ummar kowane yanki a jihar za su samu tagomashi a duka muhimman fannoni na rayuwa. Alal misalin; a ƙarƙashin irin wannan tsarin an gyara asibitoci uku-uku a yankunan karkara a kowace ƙaramar hukuma a faɗin jihar.

Waɗannan gyare-gyaren kuwa sun haɗa da sauya rufi da ƙofofi da tagogi da rufi na silin da daɓen ƙasa da flastar bango da fenti da kuma samar da magunguna da muhimman kayayyaki na yau da kulkum da ake buƙata a aikin asibiti, irin allurai da takunkumin fuska da safar hannu da magunguna da sinadarai iri-iri.

Haka zalika aikin gyara asibitocin ya haɗa da gina gidaje uku-uku na likitoci da sauran malaman asibiti, domin su samu wajen zama da walwalar da suke buƙata, don su gudanar da aikinsu cikin sauƙi. An ƙawata waɗannan sabbin gidajen likitoci da malaman asibiti da suka muhimman kayayyakin da ake buƙata, domin su samu sukunin gudanar da aikinsu.

Har ila yau, a wajen gyara waɗannan asibitocin an yi la’akari da yawan al’umma da wasu manyan ƙananan hukumomi suke da shi, kamar ƙaramar Hukumar Katsina da Daura da Funtua da Kankia da Mani da Malumfashi da Dutsinma, waɗanda su ne tsoffin ƙananan hukumomi. A waɗannan ƙananan hukumomin an gyara asibitoci biyar-biyar, inda daga baya za a gyara sauran asibitocin da ke sauran mazaɓun. Aka misali; a ƙaramar Hukumar Mani an gyara ƙarami asibitin Bagiwa da Randawa da Tsagem da Bujawa da Magami.

A halin yanzu, ƙaramar Hukumar ta Daura an gyara asibitin Duwan da Kwatta da Durbi Ta Kusheyi. Har ila yau, karamar hukumar tana shirya gangami da duba marasa lafiya kyauta, inda ake musu aikin yanar ido kyauta gami da ba su magunguna. A karon ƙarshe, an gudanar da irin wannan aikin a garin Bagiwa, inda jama’a masu ɗumbin yawa suka halarci wajen duba marasa lafiyar.

A ƙaramar Hukumar Jibia kuwa, saboda irin gyaran da aka yi wa waɗannan asibitocin har al’umma ke tururuwa daga Jamhuriyar Nijar zuwa waɗannan asibitocin, domin su samu irin kulawar da al’ummar Jibia suke samu. Waɗannan ‘yan ƙasar ta Nijar, musamman mata masu juna biyu da masu shayarwa, suna zuwa asibitocin da aka gyara ne a Daddara da Magama da garin Jibia.

Aiyukan da ake yi musu sun haɗa da duba lafiyar jariransu, musamman masu fama da zawo da cutar Tamkwa. Mahukuntan asibitin suna ba su madarar Kwamaso da magunguna kyauta.

Jami’i mai kula da asibiti na matakin farko a Jibia, Dahiru Magaji, ya shaida wa Blueprint Manhaja cewa, a asibitin suna amsar haihuwa daga mata da dama daga Jihar Maradi ta Jamhuriyar Nijar.

“Galibi waɗannan matan suna zuwa ne daga Dan Isa da Faru da Mada-Rumfa da Kale da Hirji da Mairaga da sauran ƙauyuka da yawa na Jihar Maradi, saboda kusancinmu da su kuma ’yan uwanmu ne. Saboda haka tun da mun samarwa da mutanenmu ingantattun asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya, har maƙwabtanmu sun shaida haka, bai kamata mu hana su zuwa ba.

“Karamar hukuma ta gyara wannan asibitin kuma ta ƙawata shi da duk kayan asibiti da ake buƙata. Alal misali; tun kafin gwamnatin jihar ta fara waɗannan gyare-gyaren, ita gwamnatin ƙaramar hukuma ta riga ta fara yin gyare-gyare a nata matakin.

“An gina gidan da likitan da ke aiki, wanda zai riƙa zama, an gyara ɗakin tiyata, ana samar da sirinji da magunguna da safar hannu da sauran muhimman kaya asibiti a kodayaushe, sannan kuma an yi fenti, an inganta asibitin.

“Amma su ma gyare-gyaren da gwamnatin jiha ta yi sun taimaka wajen inganta kiwon lafiya a asibitin,” inji Magaji.

Wani abin ban sha’awa shine, yadda wasu ƙananan hukumomin suka gudanar da ayyuka da kuɗaɗen shiga da suke samu. Alal misali; a ƙaramar Hukumar Sandamu, Shugaban ƙaramar Hukuma, Alhaji Usman Nalado, ya bayyana yadda ya inganta kuɗaɗen shiga, kuma ya aiwatar da ɗumbin ayyuka daga kuɗaɗen shiga da ƙaramar hukumar ke samu.

“Mun gyara manyan motocin ƙaramar hukuma kuma muna samun ɗumbin kuɗi daga motocin hayarmu. A cikin kuɗin ne mu ka gina sabuwar kasuwa a garin Sandamu, kuma muka gyara asibitin da ɗakunan bada magani, har ma muka farfaɗo da masana’antar yin alli da ke garin Sandamu.

“Daga cikin sauran kuɗaɗen da muke samu mun aiwatar da ayyuka sama da ɗari biyu a faɗin ƙaramar hukumar. Ayyukan sun haɗa da gyaran matatar ruwa da ke garin Sandamu, mun kashe Naira miliyon 85 akan wanna aikin kuma mun gode wa Allah cewa, wadataccen ruwan ya samu a Sandamu.

“Mun kuma gina da gyara masallatai 25, kuma mun gina hanyoyi masu jimillar tsawon kilomita biyar a faɗin ƙaramar hukumar. Baya ga ayyuka a ɓangaren noma da bada gudunmawa ga makarantu da masu ƙaramin ƙarfi da gina cibiyar horar da matasa da ɗalibai akan ilimin na’urar zamani, wato kwamfuta da sauransu,” inji Usman Nalado.

Shi ma Ahugaban ƙaramar Hukumar Zango, Alhaji Ahmed Aminu Babangida, ya bayyana yadda ƙaramar hukumar ta samar da na’urar samar da wuta mai ƙarfin KɓA 300, gami da samar da tankunan ruwa da fanfuna masu amfani da hasken rana ga masallatai da islamiyyu a faɗin ƙaramar hukumar.

A ƙaramar Hukumar Daura, Shugaban ƙaramar Hukumar, Alhaji Bala Musa Daura, ya bayyana yadda ya gyara manyan motocin ƙaramar hukuma guda biyar, domin bunƙasa kuɗaɗen shiga da ƙaramar hukumar ke samu, wanda ya ba su damar gudanar da manyan ayyuka, har da samar da ƙari ga matasa da mata, domin su kama sana’a.

Haka zalika a ƙaramar Hukumar Mai’adua, Shugaban ƙaramar Hukumar, Alhaji Mamman Salisu Na-Allahu, ya bayyana yadda ƙaramar hukumar ta gudanar da ayyukan hanya da magudanan ruwa makarantun firamare da asibitoci da sauransu, don inganta rayuwar al’umar ƙaramar hukumar.