Yadda ƙasar Sin ta bai wa fannin lafiyar duniya tagomashi

Daga AHMAD FAGAM

Masu hikimar magana na cewa, “yabon gwani ya zama dole.” Yayin da ranar 25 ga watan Afrilu ta kasance a matsayin ranar yaƙi da cutar zazzaɓin cizon sauro wato maleriya ta ƙasa da ƙasa, ko shakka babu, duniya ba za ta taba mantawa da dunbun alheran da ƙasar Sin ta samar ga fannonin daban-daban ba, musamman fannin kiwon lafiyar bil adama. Albarkacin wannan rana ta bikin yaƙi da cutar maleriya ta shekarar 2022, bari mu yi tsokaci kan wata muhimmiyar gudummawa da ƙasar Sin ta baiwa duniya wajen yaƙi da cutar maleriya.

Ƙwayar maganin Artemisinin, wani magani ne da ya shahara a duniyar yaƙi da cutar maleriya, maganin, wanda ƙasar Sin ne ta kirkiro bisa fasahar amfanin tsirrai. A bana, ake murnar cika shekaru 50 da ƙasar Sin ta samar da tare da fara amfani da maganin Artemisinin. A sakon da ya aike, shugaba Xi Jinping ya taya murna ga dandalin ƙasa da ƙasa bisa murnar cika shekaru 50 da samar da kwayar maganin Artemisinin don gina lafiyar jikin al’umma.

Haƙiƙa, ƙwayar maganin Artemisinin ta taka muhimmiyar rawa wajen yaƙi da cutar maleriya ga duniya. A cikin kalaman shugaban, ya bayyana cewa, ƙwayar maganin Artemisinin shi ne maganin yaƙi da cutar maleriya mafi inganci da aka gano kuma aka cimma nasarar samar da shi a ƙasar Sin. Maganin ya taimakawa ƙasar Sin wajen kawar da cutar maleriya baki ɗayanta daga ƙasar a shekaru 50 da suka gabata. A don haka, artemisinin ya samu shahara da karɓuwa a duk duniya. Wani abin farin ciki shi ne, baya ga tasirin da maganin ya haifar wajen kakkaɓe cutar daga kasar Sin, sannan ya taimaka wajen ceto miliyoyin rayukan jama’a a sassan duniya, musamman a ƙasashe masu tasowa.

A cewar Deng Boqing, mataimakin shugaban hukumar bunƙasa haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa ta ƙasar Sin, daga shekarar 2012, ƙasar Sin ta taimakawa ƙasashe masu tasowa wajen yakar cutar maleriya ta hanyar samar musu da ƙwayar maganin Artemisinin, da horas da jami’an lafiyarsu, da kuma tura tawagogin ƙwararrun masana kiwon lafiya, da gina cibiyoyin yaƙi da cutar maleriya. Kawo yanzu, an aiwatar da ayyuka daban-daban na tallafawa yaƙi da cutar maleriya a kalla 300, sannan an tallafa wajen gina cibiyoyin yaƙi da cutar maleriyar a ƙasashe 30, da tura tawagogin jami’an tallafin kiwon lafiya 28,000 zuwa ƙasashen duniya da shiyyoyi 72, sannan an horas da dubban jami’an lafiya game da yaki da cutar maleriya a ƙasashe masu tasowa. Da samar da ƙwararrun masana yaki da malaria.

A yanzu, kwayar maganin Artemisinin ta zamto wani muhimmmin ginshikin kasuwanci da kuma taimako a yaki da cutar malariya, matakin da ya bayar da gagarumar gudunmawa ga shirin yaki da malariya a duniya. Koda yake za mu iya cewa, wannan batu bai zo da mamaki ba, kasancewa a ko da yaushe, mahukuntan ƙasar Sin sun sha nanata aniyar cewa ƙasar a shirye take ta yi aiki tare da al’ummun ƙasa da ƙasa, wajen karfafa hadin gwiwa a fannin kula da lafiyar al’umma, da haɗin gwiwa don tinkarar manyan ƙalubalolin dake yiwa duniya barazana da nufin bayar da gagarumar gudunmawar kiyaye lafiyar al’ummar ƙasashen duniya don a gudu tare a tsira tare.