Yadda ƙungiyar KAHOSSA 97 ta tallafa wa mambobinta marasa ƙarfi

Daga ABUBAKAR M. TAHIR a Jigawa

Ƙungiyar Tsofaffin Ɗaliban Makarantar Sakandaren Kimiyya da Fasaha da ke garin Kafin Hausa aji na shekarar 1997 ta gudanar da babban taronta na shekara a makarantar koyon jinya da ke garin Haɗejia.

Taron da ya samu halartar ’yan ƙungiyar daga jihohi Kano, Jigawa, Yobe da Bauchi ya samu halartar Shugaban Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa (NITDA), Malam Kashifu Inuwa da ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Gumel.

Da yake jawabi ga manema labarai, Shugaban hukumar NITDA, Malam Kashifu Inuwa ya bayyana cewa, sun saba gudanar da irin wannan taro duk shekara wanda suke yin zumunci da junansu su kuma tallafi marasa ƙarfin cikinsu.

Malam Kashifu Inuwa ya ƙara da cewa yaji daɗin taron na bana ganin irin tallafin da suka bawa ’yan ƙungiyar masu qarafin ƙarfi.
Kashifu ya qara da cewa, ƙungiyar KAHOSSA 97 ba ta tsaya nan ba, domin ta kan lura da halin da makarantar ta ke ciki ta kuma tallafa ma ta.

Da yake jawabi, Sakataren ƙungiyar, Malam Isa Umar Muhammad Bulangu ya zayyano irin nasarorin da suka samu wanda ya haɗa da samar da haɗin kai ga ’yan ƙungiyar.

Isar Umar ya ƙara da cewa, sun gabatar da kyautar naira dubu ɗari ga mambobin guda tara da suka fito daga garuruwa domin inganta sana’o’insu.

Da yake jawabin godiya, Shugaban ƙungiyar, Mallam Muhammad Bashir Dauda Haɗejia ya bayyana matuƙar farin cikinsa ga yadda taron ya gudana lafiya.

Malam Dauda ya ƙara da cewa, tunda aka kafa makarantar Kimiyya da ke Kafin Hausa babu wata ƙungiya da ke gudanar da ayyukan cigaba kamar ta su.

A ƙarshe ya yi addu’a Allah ya sakawa kowa da alkairi ya maida kowa gida lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *