Yadda ƙungiyar Kiristoci ta yi wa Bankin Ja’iz bore don hana shi gyara kasuwar Terminus ta Jos

Daga AMINA YUSUF ALI

Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) reshen jihar Filato tare da Gamayyar qungiyoyin ƙabilu ‘yan asalin jihar da sauran ƙungiyoyi makamantansu sun yi kira da a dakatar da aikin gyaran da za a fara a kasuwar Terminus ta Jos saboda abinda suka kira da fuska biyu wajen rubuta yarjejeniyar kwantiragin aiki.

A cewarsu, bai kamata a ce yarjejeniyar kwantiragin ta kasance a tsakanin gwamnati da masu ɗaukar nauyin aikin (Bankin Ja’iz) kawai ba.

Ƙungiyoyin sun yi wannan kira ne a yayin wani taro wanda shugaban ƙungiyar Kiristoci (CAN) Rabaran Fr. Polycarp Lubo ya kira a ranar Litinin wanda aka gudanar a gidan gwamnatin jihar Filato dake garin Jos.

Shugaban na CAN shi ne ya bayyana matsayar masu ruwa da tsakin a taron manema labaran da aka gudanar bayan kammala taron ganawa tsakanin ƙungiyoyin da kuma jami’an gwamnatin jihar ta Filato.

Idan ba a manta ba, a baya gwamnatin jihar Filato ta amince da haɗa gwiwa da Bankin na Ja’iz domin sake gyaran kasuwar Terminus ɗin wacce gobara ta lalata. Kuma ana ƙiyasin gyaran zai ci Kimanin Naira biliyan 9.4.

Jami’in CAN ɗin ya ce sun kira wannan taro ne saboda irin ce-ce-ku-ce da wannan aiki ya jawo a kan bayanin da suka samu cewa, gwamnati jihar Filato ta ba da jinginar rayuka da dukiyoyin matasan jihar na shekaru arba’in a cikin wannan yarjejeniyar.

Ya ƙara da cewa, ƙungiyoyin ba su ji dadin yadda aka qi tuntuvarsu ba a matsayin masu faɗa a ji yayin da za a gudanar da yarjejeniyar aikin gyara kasuwar.

Ya shawarci gwamnati a kan ta dakatar da wannan aiki na gyaran kasuwa a yanzu har sai an tuntuɓi dukkan waɗanda suka dace.

A yayin jawabinsa wanda ya yi a maimakon gwamnatin jihar, Mista Chrysanthus Ahmadu, Antony Janar na Jihar ya musanta wannan maganar tare da nuna damuwarsa a kan yadda aka ba wa al’ummar Filato labaran ƙarya.

Mista Amadu ya ƙara da cewa, shekaru arba’in da ake zance shi ne za a ba wa masu rumfuna damar cigaba da zama a rumfunan nasu amma bayan shekaru arba’in gwamnati za ta karɓe kayanta.

Don haka a cewar sa, duk wanda ya sayi rumfar na tsawon shekaru arba’in take tasa ba wai Bankin Ja’iz za a a ba wa shekaru 40 ɗin ba.

Kuma a cewar sa, har yanzu gwamnatin tana kan tattaunawa ne da bankin kuma ba su samu damar cimma matsaya ba. Amma sun samu fahimtar juna a kan yadda za a gudanar da aikin.

Mista Amadu ya ƙara da cewa, Bankin Ja’iz dai ba wani abu ba ne illa mai ɗaukar nauyin aikin gyara kasuwar. Bankin zai ba da kaso 60 na aikin, yayin da gwamnatin jihar za ta ba da kaso 40, a cewar sa.

Daga ƙarshe ya bayyana cewa, gwamnati za ta yi wa al’ummar Filato adalci wajen sayar da rumfunan sanann za ta sa ido sosai ganin bankin bai sayar musu da su a tsawwalallen farashi ba. Kuma gwamnatin ta saurari kokensu kuma za ta tuntuɓi waɗanda suka dace don kyautata wa al’ummarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *