Yadda ƙungiyoyin manoma suka tafka asarar kayan amfanin gona

Daga MUHAMMADU MUJITABA

Ƙungiyoyin Manoman shekafa, dawa, masara da sauransu sun tafka sarar kayan amfanin gona mai ɗumbin yawa na billiyon naira da ba a tantance yawansa ba a wannan shekara sakamakon ƙarancin ruwa da aka samu a wasu wuraren na jihohin arewacin Nijiriya, wanda suka bayyana wa duniya domin dai sanar da hukumomin da sauran masu ruwa da tsaki domin ɗaukar mataki kamar yadda ya dace.

Alhaji Samaila Abdullahi Wali shi ne shugaban masu sayar da kayan amfanin gona na zamani kuma ɗaya daga cikin ’yan ƙungiyar manoma da safarar kayan gona, ya ce, babu shakka a bana manoma sun tafka asara mai yawa musamman shinkafa da masara da makamantansu, haka kuma sun tafka asara mai yawa a bana sakamakon wannan fari da ruwa bai kai ba.

Ya ce, yanzu haka sun fara tatara alƙaliman na kiyasi akan kayan amfanin gonar da aka yi asara wacce ta shafisu kai tsaye don miƙa wa Gwamnati da nufin neman tallafin ta a matsayinta na uwa maba da mama ga talakawan Nijeriya.

Har ila yau, ya ce, da zarar sun tattara asarar kayan gonar, za a ƙiyasta kuma sannan a sanar wa Gwamnati ta hanyar da yadda ce kuma ya kamata, don haka ya ya yi amfani da wannan dama wajen jajanta wa manoma kan wannan asara inda kuma ya yi nasiha ko shawara kan a ririta ɗan abun da aka samo da kuma rage hidimar da ba dole ba domin da saman sauƙi a rayuwa, ganin yadda wannan shekara ta zo da haka kuma a yi noman rani a himmatu wajen yin shuka da wuri kada a raina ruwan shuka a ko wacce shekara da ta zo ga mai yawan rai.

Shugabar ƙungiyar mata manoma da safarar kayan amfanin gona ta Kano, Hajiya Sidiya Fatima Sharo Gambo Yako, ta ce, aƙalla suna noma hekta guda a kowace ƙaramar hukuma 44 da ke Kano wanda ya zo haka su tafke asarar shinkafa na buhuna ɗaruruwa wannan shekara da ake magana yanzu.

Fatima Sharo Gambo Yako ta ce, akwai buƙatar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya raba wa jihohin da aka yi asarar nan tallafin noma don manoma su rage raɗaɗin asarar da suka yi na noma a bana.

Honarabul Hambali Yunusa shi ne kakaki Majalisar ƙaramar hukumar Aginji wanda ya shaida wa manema labarai a madadin shugaban ƙaramar hukumar Honarabul Murtala Uba ɗanbayye cewa, duk matsayin Ajingi a harkar noma a matsayin ta uku cikin ƙananan hako momi 774 A Nijeriya ya tabatar da cewa ƙungiyoyin manoma na Ajingi sun samo kayan amfanin gona kamar gero, maiwa, dawa, gyaɗa da wake, wand aba don fari da suka samo ita ce ɓangaran shikafa wacce bata kai ba duk wasu manoman sun duƙufa wajen ba shikafar ruwa a ma dai anyi asarar shikafa bana.