Yadda ƙungiyoyon zakirai da sha’irai suka nuna basira a maulidin sharifan Nijeriya

Daga MUHAMMADU MUJITABA

Ƙunyoyin zakirai ma’abutan ambatun Allah da shairai mawaƙan Ma’aikin Allah mai tsara da amincin Allah da ahalinsa da sahabansa da sauran bayin Allah tsarkaka, sun nuna basira wajan yabon shugaban halita manzun rahama da abunta Allah maɗaukakin sarki a maulidin shariifan Nijiriya wanda aka gabatar a garin Ali Wanbai Jangargari garin mai saje, a kirarin Garin Ali, kenan, wanda aka gabatar ƙarƙashin shugaban mai shirya maulidin, Alhaji Haruna Sharo Abba Garin Ali wanda ya gudana a garin Garin Ali da ke ƙaramar hukukomar Garko jihar Kano Nijiriya.

Maulidin sarifan Nijiriya wanda ya sa muhalata sharifai aƙalla 17 akwai manya manyan sharifai daga sassa daban-daban na jihohin Nijiriya da suka halatar haka kuma akwai ƙungiyoyin zakirai da kuma ƙungiyoyi ko ayarin sha’irai masu yawa a wannan maulida na sharafa’u jikokin ma’aikin Allah da ake kira da Ahli Baiti Rasullallahi.

Baya ga sharifai, zakiri, shairai da suka yi cikar kwari, a wannan maulida kuma akwai manya shehunnai, malamai, ’yan kasuwa daga Kano da sauran jihohi haka kuma gwargozun muraidai, da ɗalibai duk ba su yadda an barsu a baya ba a wannan maulidi na sharifan Nijiriya a garin Ali Garko ta Kano ba, Nau’in jama’a a wannan maulidi ba zai lisafu ba domin suna da yawa ana abu guda aka haɗu akansa shi ne ambaton Allah da yabon Manzon Allah (SAW) da jiddada farin cikin hafafuwarsa da kuma karatun tarihinsa da ɗabi’unsa abun ko yi ga ma’abota rabon duniya da lahira shi ne abinda wannan mulidi na sharifai ya kasance a garin Ali Garko.

Kaɗan daga cikin sarakona sharifai akwai sarkin sharifai da suka sanya albarka a wannan maulidi akwai sarkin sharifan Gaya, akwai na Jos, Bichi, Tofa, Karaye, Gwale, Jigawa akwai wakilin Larabawa, haka kuma wakilin sharifan Bolari daga jihar Gambe da Sauransu.

Inda a Jawabin Sarkin Sharifers na masarautar Gaya ya yi dogon Jawabi da tarihi shugaban halitta da kuma darasin da ke ciki da ya kamata Jama’a ko yi domin amfaninmu a duniya da kuma lahira inda kuma ya bawa Alhaji Haruna Sharo Abba kan wannan gagarimin aikin Allah da masoyan manzonsa da a halinsa a madadin sarakunan sharaifai da ɗaukacin al’ummar da taro don girmama shugaban halitta.

Haka kuma manyan sharifai da kuma fitatto duk sun halacin taron maulidin kamar su sharo Muktari Gabari Sharo Maaro, Giwar Sharifai da dai sauransu daga sassa daban-daban a wannan maulidi karo na 30.

Baya ga cinciron don sharifai akwai manya malamai da shehunnai irinsu, Sheikh Usuman Kasfa Zariya, Sheikh Abubakar, Sheikh Nura Wudil, Sheikh Abubakar, Shehu Malam Sale Mai dala Ilu Unguwa Uku Kano, da dai sauran shehunnai da malamai da muradai ko kuma ɗalibansu a wannan maulidi na shaifai haka akwai ƙungiyar ko a yaran ’yan kasuwa ƙarƙashin shugabancin Alhaji Sani Kabiru Sani Kwangila wanda ya yi wanda ya yi Jawabi mai tsawo da misali ƙarfe biyu na dare.

Inda ya jawon hankali jama’a su yawaita addu’a duk lokacin da aka yi sallah jam’i a yi addu’a a matsayin maganin masifa da kuma girmama malamai da sauransu bayam Allah sai kuma buƙatar gagarimi gyara a shugabancin ƙasar nan domin jama’a ta samu sauƙin rayuwa haka kuma akwai ’yan kasuwa da da ma irinsu Alh, Ibrahim Dan Canji Alhaji Muhamad Fagge Halifa Yahaya sai tsofofin ma’aikatan gwamnati Irinsu Alhaji Ali Nuhu Wali Yakasai, Darkata da sauransu wanda suka bayyana gamsuwarsu da taron.

A ƙarshin taron maulidi ne shugaban taron Alhaji Haruna Sharo Abba ya ra ba kyautukan yabo ga shairai maza da mata irin su Fatihu Rabi’u da Fati Rayuwa, Bashir Ɗan Musa da sauransu kan basira da suka nona na yabon manzon rahama da a halinsa da sahabbansa da sauran bayan Allah na gari a wannan maulidi.

Sharo Haruna kuma ya kuma yaba wa sha’iraifi da zakirai da Shehunnai da su kinsa masu maulidi wato sharifai Ahalilibati kan samu nassarar wannan muhimmin taro mafi girma da daraja wanda ake yinsa don jaddada murna da farin cikin haihuwar shugaban halitta, kuma ya yi godiya ga Allah kan wannan dama da Allah ya ba shi na shirya wanan maulidi ba tare da ya nemi taimakon kwaban kowa ba, inda ya yi nasiha ga jama’a kan riƙo da ma’aikin Allah da ahalinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *