Yadda ƴan bindiga suka yi garkuwa da mutune 20 a hanyar Ijebu-Ode zuwa Shagamu

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

A ƙalla matafiya ashirin ne ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a kan babban titin Ijebu-Ode/Sagamu a ranar Lahadi, kusa da ofishin rundunar ‘Yan sanda na birnin Ileshan da ke Shagamu.

Kakakin rundunar Ƴan sandan yankin, Omolola Odutola ya ce an samu wani mutum da ake zargin ƴan bindigan sun harbe shi a gwiwa wanda a halin yanzu ya ke karɓar kulawa daga jami’an lafiya.

Omolola ya ce sun tabbatar da batun garkuwa da mutanen inda ya ce suna ƙoƙarin gano inda ƴan bindigan su ke tare da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.