Wasu matasa da ake kyautata zaton ‘yan daba ne sun fasa wani sabon ofishin ‘yan sanda da aka gina a unguwar Ugbineh da ke ƙaramar Hukumar Ovia ta jihar Edo.
An bayar da rahoton cewa, maharan sun kwashe muhimman kayayyaki da wayoyin lantarki.
An ce an gina ofishin ne ta hanyar haɗin gwiwa, kuma har zuwa faruwar lamarin ba a ƙaddamar da aikin ba.
Wani dattijo a unguwar Ugbineh, Pa. Sunday Iyoha, ya yi Allah-wadai da ɓarnar da aka yi, inda ya ce an gina ofishin ‘yan sanda ne domin magance rashin tsaro a yankin.
Iyoha ya ƙara da cewa: “A yayin da muke shirin kaddamaraddamar da aikin, wasu masu laifi sun mamaye ofishin ‘yan sanda tare da lalata kayayyakin da ke cikin ginin.”
A fusace da faruwar lamarin, inda dattawan yankin suka shiga aikin bincike domin gano mutanen da ke da hannu a cikin wannan aika-aikar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Edo, SP Moses Yamu, ya ce jami’an ‘yan sanda sun samu rahoton faruwar lamarin, inda ya ce an fara gudanar da bincike.
A cewarsa, “muna ganawa da shugabannin yankin kan wannan mummunan lamari yayin da aka tura tawagar dabaru domin a kamo waɗanda ake zargin.
Sai dai kakakin ‘yan sandan ya kai ƙara domin neman bayanai daga jama’a da za su taimaka wa jami’an su kamo waɗanda suka aikata laifin.