Yadda ɗa ya yi wa matar mahaifinsa ciki a Nasarawa

Daga WAKILINMU

Wata matar aure a jihar Nasarawa ta bayyana cewa, ɗan mijinta ne ya ɗirka ma ta ciki.

Matar ta ɗora laifin kan mijin nata da ta ce, ya gabatar ma ta da ɗan nasa ne a matsayin ɗan uwansa ba ɗan cikinsa ba.

Ta ƙara da cewa, “auren saurayi da budurwa muka yi ni da mijina, wanda yanzu ya rasu. Mun fara samun matsala ne bayan na shafe shekara biyar ba tare da na yi ko ɓatan wata ba. Hakan ne ya sa surukata ta dinga tsangwama ta har shi ma ya goyi bayanta saboda rashin samun ciki da na yi.”

Ta ci gaba da cewa, “wannan halin da nake ciki ne ya sanya ni jan hankalin ɗan mijina ba tare da na san cewa ɗansa ba ne.

Ta ce, “sai bayan na samu ciki, lokacin yaron ya samu gurbin karatu a Kwalejin Ilimi ta Akwanga ne na san cewa ɗan cikinsa ne. Bayan yaron ya rasu a haɗarin mota a kan hanyarsa ta zuwa Kwalejin Akwanga ne ’yan uwan mijina suke sanar da ni cewa ɗan cikinsa ne.”

“A lokacin ne fa na gano cewa ai cikin da nake ɗauke da shi na ɗan mijina ne,” inji ta.

Ta ce, ta shafe shekara 19 da ta yi da aure ba tare da haihuwa ba ne ya jefa ta a halin da ta tsinci kanta a yanzu.

Matar tana bayyana yadda mijinta ya kawo wani matashi mai shekara 17 a matsayin ɗan uwansa, alhali kuwa ɗan cikinsa ne.