Yadda ɗan shekara 18 ya sace ɗan makwabcinsa a Sakkwato

Rundunar ’yan sanda reshen jihar Sokoto, ta cafke wani ɗan ƙungiyar masu garkuwa da mutane, inda ta cafke babban wanda ake zargi, ɗan shekara 18, Abba Aliyu, wanda makwabci ya shigar da ƙara daga unguwar Badon Hanya a jihar Sokoto.

Wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Ahmed Rufa’i ya raba wa manema labarai a jihar a ranar Asabar, ta ce a ranar 16 ga Oktoba, 2024, da misalin ƙarfe 1200 na safe, Ibrahim Shehu ya kai rahoto ga sashin yaƙi da garkuwa da mutane da ke sashin binciken manyan laifuka na Sakkwato, inda ya ce ɗansa, Saidu Ibrahim, mai shekaru biyu ya ɓace tun ranar 13 ga Oktoba, 2024, da ƙarfe 1800.

“Duk da ƙoƙarin gano shi, har yanzu ba a san inda yake ba, har sai da wanda ya sace shi ya buƙaci kuɗin fansa har Naira miliyan 2 ta wayar tarho, inda aka biya shi Naira dubu fari biyar kafin ya saki yaron.

“Jami’an tsaro sun haɗa kai cikin gaggawa wajen gudanar da ayyukan leƙen asiri, inda suka gano wurin da wanda ake zargin yake a Badon hanya da ke bayan tashar Zamson wanda ya kai ga kama shi.

“A yayin gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa ya yi garkuwa da yaron da nufin karɓar kuɗi daga hannun iyayensa, yayin da kira waya ta wata wayar salula ta Tecno domin karɓar kuɗin fansa,” inji rundunar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ahmed Musa, ya jaddada ƙudirin rundunar na yaƙi da miyagun laifuka tare da yaba wa ƙoƙarin jami’an wajen ganin an samu nasarar cafke wanda ake zargin.

CP Musa ya kuma ba da wasu alamu kan yadda iyaye za su iya kiyaye ‘ya’yansu daga abubuwan aikata laifuka waɗanda suka haɗa da ilmantar da yaran kan ƙa’idojin aminci.

“Koya musu su gano manyan amintattu kuma su ba da rahoton abubuwan da ba su gane musu ba, guje wa tafiya su kaɗai tare da ƙarfafa yara su yi amfani da tsarin abokantaka.

“Wasu sun haɗa da zama a wurare masu haske, gujewa keɓancewa a wurare masu duhu, ƙin karɓar kyauta daga baƙi, faɗakar da su game da abubuwan da za su iya lalata rayuwarsu,” inji shi.