Yadda ɗan uwana ya cika a gabana – Aliko Ɗangote

Daga BASHIR ISAH

Hamshaƙin ɗan kasuwar nan
Alhaji Aliko Ɗangote, ya bayyana yadda ƙaninsa, Marigayi Sani ya cika a gabansa a asibitin Amurka.

Ɗangote ya ce likitoci sun sanar da shi cewa ɗan’uwasa zai cika cikin sa’a guda, kuma abin da ya faru kenan da lokacin ya cika, “Inda na ga na’aurar da aka maƙala masa take taimaka masa ta rinƙa ja da baya da aiki har ta kai ga ta tsaya.”

Ɗangote ya bayar da wannan labari mai cike da tausayi ne a lokacin da jagoran jam’iyyar APC na ƙasa, Alhaji Bola Tinubu, ya kai masa ziyarar ta’aziyya a Kano a Juma’ar da ta gabata.

Ya ci gaba da cewa, “Da ma abu ne da muka sani cewa akwai rayuwa da mutuwa, a matsayinmu na Musulmi ba mu san wane ne na gaba ba, ka iya faruwa yau ko gobe, kai ko ma yanzu.

“Wannan shi ne dalilin da ya sa ya kamata mu kasance masu kyautatawa a kowane lokaci ta yadda ko da mutum ya tafi can zai tarar da ya aikata abin da ya kamata a rayuwarsa ta duniya.”

Ya ce rasuwar ɗan’uwansa wani mawuyacin lokaci ne ga ahalinsu, musamman gare shi saboda yadda suka shaƙu da junansu.

Attajirin ya ce, “Samun ɗan’uwa irin wannan, yana da matuƙar ciwo idan ka rasa shi, saboda a gabana tare da mahaifiyarmu da dukkan ‘ya’yansa ya rasu.

“Abu mafi raɗaɗi shi ne idan aka sanar da kai cewa ɗan’uwanka zai cika nan da awa guda yayin da kai kuma kana tsaye kana kallon yadda na’urar da ke taimaka masa take daina aiki a hankali har ta kai ga tsayawa baki ɗaya.”

Tun farko, Tinubu ya shaida wa Aliko Ɗangote cewa ya yi matuƙar kaɗuwa da samun labarin rasuwar Marigayi Sani.

Tinubu ya bayyana marigayin da mutum kamili a halin rayuwarsa. Daga nan ya yi kira ga ahalin marigayin da su yi haƙuri da juriya dangane da rashin, kana su ci gaba da yi wa mamacin addu’a.

Haka nan, ya ce sun zo ne domin su taya jimamin rasuwar ɗan’uwansu. Yana mai cewa, “Ni ba mai wa’azi ba ne, amma na san zafin irin wannan mutuwar musamman ma idan ta faru a kan ɗan’uwa.”

Kazalika, Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ga kakan marigayin, wato Alhaji Aminu Ɗantata. Tare da addu’ar Allah ya jinƙan marigayin da rahama Ya kuma sanya Aljanna ta zamto makomarsa.

A nasa ɓangaren, Ɗantata ya nuna godiyarsa ga ziyarar ta’aziyyar da Tinubu ya kai musu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *