Yadda ƙabilanci zai yi tasiri a zaɓen 2023 a Nijeriya

Daga DATTI ASSALAFIY

A yanzu haka, zancen da ake yi dai haɗakar ƙungiyar Yarbawa ta Duniya sun fitar da sharuɗɗan ƙabilanci masu tsauri da suke so ɗan takarar APC Bola Tinubu ya ɗauka ya yi musu alƙawarin zai cika kafin su goyi bayansa a zabe mai zuwa. Sharuɗɗan su ne:

  1. Tabbacin samun tsaron yankin Yarabawa ta hanyar ba wa ƙungiyarsu ta tsaro mai suna AMATEKUN makaman tsaron da za su yi amfani da shi.
  2. Gyarawa ko rusa tsarin shiyya-shiyya guda 6 na ƙasar Nijeriya (Geo Political zones), tsarin da zai fitita yankinsu na Yarbawa.
  3. Haɗe yarukan da suke da dangantaka da Yarbawa mazauna jihar Kogin Arewacin Nigeria da sauran jihohin su shige cikin daular Yarbawa ta ‘Oduduwa People’s Congress’ (OPC).
  4. Hanyoyin ruwa da ƙasa mallakin shiyyoyi sai an ba su tsaro da kulawa ta yadda kowanne ɗan ƙasa zai samu ‘yancin amfani da su babu ɓangaranci.
  5. Sai an ƙirƙiri kotu mallakin Yarbawa (Southwest Area Court) wacce za ta kare muradu da martabar Yarabawa zalla.
  6. Sai an ƙirƙirar musu hukumar tattara haraji ta shiyyar yarabawa zalla (Southwest Inland revenue).
  7. Sai an ƙirƙirar musu hukumar kula da wutar lantarki mallakin kansu, Yarbawa zalla (Southwest Electricity Power Generation).
  8. Sai an ƙirƙiri hukumar tattara bayanai mallakin yarabawa zalla (Southwest Database).
  9. Sai an ƙirƙiri hukumar sadarwa ta yankin Yarbawa (Southwest Communication Network).
  10. Ajiye tsarin addinai a gefe wajen zaɓen shugabanni, babu maganar idan Musulmi ya yi, sai Kirista ya yi, kowa zai iya yi babu adadi.
  11. Tabbacin kowanne yanki a Nijeriya sai sun bi tsari, dokoki, yarjejeniya da ƙa’idar da hukumomin duniya (United Nation ) Suka gindaya.

Waɗannan su ne sharuɗɗan da gamayyar qungiyar Yarabawa na Duniya ta gindaya wa ɗan uwansu Bayarabe, Bola Tinubu Kuma ta miƙa tare da sharaɗin sai ya amince ya saka hannu, kafin su goya masa baya.

A taqaice, idan aka cika musu waɗannan sharuɗɗa shikenan gamayyar ƙasashen Yarbawa sun zama ƙasa mai cikakken iko.

Duk ɗan Arewa mai tunani ya kamata ya yi duba na tsanaki a kan wannan yarjejeniyar domin gudun faɗawa hannun ‘yan mulkin mallaka.

Haƙiƙa, duk wanda ya ba da goyon baya a zaɓi Tinubu, to ya kwana da sanin cewa, ya amince a mayar da yankin Arewacin Nijeriya saniyar ware, ya amince a danne wa ‘yan Arewa dukkan ‘yancinsu da walwala
‏‏
Bambanci tsakanin takarar Atiku da Tinubu

Haka a wani labarin kuma, Tinubu ya ziyarci gidan jagoran Ƙungiyarsu na Dattawan Yarbawa (Afenifere), inda jagoran ya tabbatar da cewa, duk wani jinin Yarbawa a duniya Tinubu zai zaɓa, ba su yarda wani Bayarbe ya zaɓi wanda ba ƙabilarsu ba.

Abin mamaki, sai ga Gwamnan jihar Oyo wanda ɗan jam’iyyar PDP ne, ya ba da saƙo ta hannun mataimakinsa cewa, Tinubu ɗanuwansu Bayarabe za su zava, wato za su yi ‘anti-party’ kenan saboda ƙabilanci.

Don haka, zaɓen 2023 zaɓe ne na ƙabilanci zalla, duk wanda yake ganin ba haka ba ne, to yana yaudarar kansa ne.

Akwai bambanci tsakanin Atiku da Tinubu, Atiku ya tsaya takara ne don ya kare muradin ‘yan Nijeriya da kowanne yanki da ƙabila, shi kuma Tinubu ya tsaya takara ne don ya kare muradin ƙabilarsa kaxai, sannan don ya shiga jerin tarihi.

Kafin zaɓen fitar da gwani, Tinubu cewa yayi “it’s my turn”, ma’ana yanzu lokacinsa ne ya mulki Nigeria, mulki ne kawai burinsa. Da ya fahimci fadar shugaban ƙasa Rotimi ko Osibanjo suke so a tsayar, sai hankalinsa ya tashi, ya tsaya gaban ‘yan uwansa Yarbawa yana magana da yare ya yi wa shugaba Buhari gori da rashin kunya.

Idan ba ku manta ba a lokacin har sai da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Sanata Abdullahi Adamu ya yi wa Tinubu martani a BBC Hausa, ya ce wa Tinubu yana magana kamar ba ya hayyacinsa

Ba burin Tinubu gyara Nijeriya ba, ya faɗa, ya ce burinsa kawai ya shiga cikin tarihin waɗanda suka shugabanci Nijeriya. Kar mu yi tsammanin ganin wani abu a tare da shi na cigaba.

Muna ganin Atiku ya cancanta ne saboda zai iya yi wa kowacce irin ƙabila da yanki a Nijeriya adalci Insha’Allah.

Allah Ka mana zaɓi mafi alheri.

Datti Assslafiy ɗan ƙasa ne mai bayyana ra’ayi.