Yadda Ɗangote ya wuce ƙasashen Afirka fiye da guda 30 a arziki

Daga AMINA YUSUF ALI

A halin yanzu dai arzikin attajirin biloniyan nan ɗan asalin Nijeriya, Aliko Ɗangote ya ƙara haɓaka inda a yanzu haka ma ya zarce fiye da ƙasashen Afirka guda 30 a arziki.

Al’amarin ya faru ne bayan attajirin biloniyan wanda kuma shi ne mutumin da ya fi kowa arziki a Afirka ya ci ribar Naira biliyan N968 a cikin watanni goma sha ɗaya kacal.

Jaridar Bloomberg ta rawaito cewa, a yanzu haka ƙarfin arzkin Ɗangote ya kai dalar Amurka $20.1 billion wato Naira tiriliyan takwas da biiyan huɗu a kuɗin Nijeriya (N8.4 trillion).

Majiyarmu ta ƙara da cewa, bunƙasar arzikin biloniyan mai shekaru 64 a Duniya ba ya rasa nasaba da yadda farashin sumunti da na taki da kuma man fetur duk suka yi tashin gwauron zabi ba. Domin wannan shi ne layin kasuwancinsa. Zancen da ake yi ma tuni attajirin ya fara fitar da taki yana sayarwa a ƙasashen Amurka da Barazil, bayan kammala masana’antar da a ƙalla take samar masa da ton miliyan uku na taki kowacce shekara.

Hakazalika, ana sa ran nan da wani lokaci kaɗan biloniyan zai kammala gina matatar mai wacce za ta dinga samar da man da ya wuce buƙatar ‘yan Nijeria. Wajen da aƙalla ake sa ran zai lashe Dalar Amurka biliyan 19.

A yanzu haka dai bincike ya tabbatar da, idan aka ɗebe ƙasashe guda 54 kaf a faɗin Afirka, Ɗangote ya zarce dukkan sauran ƙasashen Afirka ta fuskar ƙarfin arziki.