Yadda Abdulsamad Rabi’u ya ture Mike Adenuga daga matsayin mutum na biyu mafi kuɗi a Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI

A halin yanzu dai Biloniya Abdussamad Rabi’u ya ture Adenuga ya ɗare kujerar matsayin mutum na biyu a arziki a faɗin Nijeriya.

Wannan ya faru ne a yayin da Attajirin ya samu cinikin sama da kimanin Naira biliyan N87 wato dalar Amurka biliyan biyar da rabi, a cikin sa’o’i kaɗan a ranar Larabar da ta gabata.

Abdulsamad Rabiu Rabiu ya samu damar ture tsohon mai kuɗin nan Adenuga wanda kafin ranar Larabar nan shi ne mutum na biyu ma fi kuɗin a Nijeriya.

To amma yanzu wannan ya zama tarihi tunda Abdussamad ya yi masa juyin mulki. Yanzu shi ne na biyun Ɗangote a kuɗin a Nijeriya. Dangote dai har yanzu shi ne ma fi kuɗin a Afirka da Nijeriya ma bakiɗaya.

Shi dai Abdussamad shi ne mamallakin kuma shugaban rukunin kamfanoni na BUA.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *