Yadda abubuwa ke ƙara taɓarɓarewa Guardiola a Man City

Alamu masu ƙarfi na nuna cewa Man City ta fara kakar wasan bana da ƙafar hagu, inda kocinta, Pep Guardiola ya ce abubuwa na ƙara yin tsauri a wasannin da suke dokawa.

Ranar Asabar, Man City mai riƙe da kofin firimiyar Ingila ta yi rashin nasara 2-1 a gidan Bournemouth, kafin nan aka yi waje da ita a Carabao Cup a hannun Tottenham 2-1, sannan a daren Talata kuma ta sha kashi hannun Sporting a gasar Zakarun Turai.

Karon farko da aka ci Man City a firimiya, wadda ta yi wasa 32 a jere ba tare da an doke ta ba a babbar gasar ƙwallon ƙafa ta Ingila.

Man City tana fama da fitattun ’yan wasanta da ke jinya, ciki har da Rodri tun daga watan Satumba, wanda gama wasannin kakar nan – shi ne ya lashe ƙyautar Ballon d’Or ta bana.

Guardiola ya ce, Man City tana tsaka mai wuya a bana, bayan da take fama da ‘yan wasa da ke jinya da ya haɗa da John Stones da Ruben Dias da kuma Kevin de Bruyne.

City tana mataki na biyu a teburin Premier League da maki 23 da tazarar maki biyu tsakani da Liɓerpool mai jan ragama, bayan karawar mako na 10.

Ya yanzu dai haka Man City za ta ƙara fuskantar Tottenham a babbar gasar tamaula ta Ingila ranar Asabar 23 ga watan Nuwamba a Etihad.

Ya ce, ba zai yi gaggawar saka Keɓin De Bruyne a wasan Manchester City ba, bayan jinya da ya yi.

Dan ƙwallon tawagar Belgium ya yi zaman benci ranar Asabar a gasar Premier League da Bournemouth ta doke City 2-1 a ɓitality.

Guardiola ya ce bayan jinyar mako bakwai da De Bruyne ya yi, yana son ya tabbatar da cewar ɗan wasan ya murmure sarai kafin ya saka shi a wasan City.

Ya ƙara da cewa, a bara ya yi jinyar wata biyar, wanda ya koma buga wa City wasanni da kafar dama, har ya bayar da gudunmuwar da ƙungiyar ta taka rawar gani.

Man City mai riƙe da Premier League ba ta kan ganiya tun bayan da Rodri ya fara jinya, wanda ya ji rauni a karawar da suka tashi 2-2 da Arsenal a Etihad.

Tun kafin wasan da City ta yi rashin nasara a hannun Bournemouth ranar Asabar, tuni kuma Tottenham ta yi waje da ita a Carabao Cup na bana.

Bayan shan kashi a hannun Sporting a Zakarun Turai, Man City za ta kece raini a gidan Brighton a Premier League ranar Asabar 9 ga watan Nuwamba.

Man City tana ta biyu a teburin Premier League da tazarar maki biyu tsakaninta da Liɓerpool mai jan ragama, wadda ta doke Brighton a Anfield a ƙarshen mako.