Yadda aikin hanyar Abuja zuwa Kano ke janyo asarar rayuka a Zariya

Daga MOHAMMED BELLO HABIB a Zariya

Al’ummomin Gwargwaje dake cikin Ƙaramar Hukumar Zariya cikin Jihar Kaduna, sun koka a kan yawaitar haɗurra a yankinsu.

Mai magana da yawun al’ummomin, Alhaji Shagari Mai Nama a tattaunawar shi da wakilin Manhaja a Zariya, ya koka akan yawaitar haɗurran, inda ya ce a duk rana ana samun haɗurra 2 zuwa 3 a yankin waɗanda kuma suke haifar da asarar rayukan al’umma akan wannan babban hanyar saboda yawan ababen hawa da suke ƙaruwa a kodayaushe, kuma hanya ce da ta haɗe Kudanci da Arewacin ƙasar nan.

Alhaji Mainama ya ƙara da cewa tunda a ka maida hanyar tagwaye lokacin mulki tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mairitaya) zuwa yanzu suke fuskantar wannan matsala ta haɗurra a yankin.

Shugaban al’ummar ya yi ƙorafin cewa mafi akasarin waɗanda haɗarin ya fi rutsawa da su mata ne da yara ƙanana da kuma masu babura, sakamakon tsallaka hanyar; inda ya ƙara da cewa yanzu da ke ƙara wa hanyar faɗi inda za ta ɗauki sahun motoci uku-uku, wanda a cewarsa babu wani tanadi da gwamnati ta yi domin rage yawaitar haɗuran.
Ya ce al’umomin dake yankin za su kai kimanin dubu 500.

Shugaban al’ummar ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kaduna da su taimaka su samar da ko da gadar sama ta motoci ko kuma ta masu tsallaka titi a yanki.

WaKilinmu ya ruwaito cewa ko a makonnin da suka gabata wata babbar mota maƙare da kwal ta markaɗewa wani mutum ƙafafu, sakamakon haka aka ce za a yanke ƙafafunsa, kafin aka ga hakan ma ya ce ga garinku nan.