Yadda aka ƙarƙare gasar Euro 2024

Sifaniya ta zama ta farko da ta lashe gasar kofin nahiyar Turai karo huɗu a tarihi, bayan da ta doke Ingila 2-1 ranar Lahadi.

A minti na uku da suka koma zagaye na biyu ne Sifaniya ta ci ƙwallo ta hannun Nico Williams, bayan da Lamine Yamal ya zura masa ƙwallon.

To sai dai Ingila ta farke ta hannun Cole Palmer, bayan da Jude Bellingham ya ajiye masa ƙwallon a ƙasa, saura minti 27 a tashi daga fafatawar.

Saura minti biyar a tashi daga karawar Sifaniya ta ƙara na biyu ta hannun Mikel Oyarzabal.

Da wannan sakamakon Sifaniya ta lashe Euro 2024, kuma na huɗu jimilla, ita ce kan gaba a yawan ɗaukar kofin nahiyar Turai a tarihi.

Sifaniya, mai kofin duniya a 2010 ta fara ɗaukar kofin nahiyar Turai a 1964 da 2008 da 2012 da kuma yanzu a 2024 a Jamus.

Wannan shi ne wasa na 28 da suka kece raini a tsakaninsu a dukkan fafatawa, inda Sifaniya ta yi nasara 11 da canjaras huɗu, Ingila ta ci 13.

Haka kuma Ingila ta zura ƙwallo 46 a raga, ita kuwa Sifaniya ta ci 34 jimilla.

Wasan ƙarshe da suka fuskanci juna shi ne a gasar ƙasa a 2018, inda Sifaniya ta je Wembley ta ci 2-1, yayin da Ingila ta yi nasara da cin 3-2 a Seɓilla.

Sai dai wasan karshe da suka kara a Euro shi ne a 1966, inda suka tashi 0-0, amma Ingila ta yi nasara cin 4-2 a bugun fenariti.

Wannan shi ne karo na biyu a jere da Ingila ta kai wasan ƙarshe a Euro, bayan da Italiya ta doke ta a Euro 2020 a bugun fenariti a Wembley.

Haka kuma karon farko da Ingila ta yi wasan ƙarshe a babbar gasa ba a gida ba, wadda take da kofin duniya a 1966, sai dai ba ta taɓa lashe Euro ba.

Wannan ita ce gasa ta 17 da aka kara a gasar kofin nahiyar Turai a tarihi.

Sifaniya ta fara wasan da Dani Carɓajal da kuma Robin le Normand, waɗanda suka kammala hutun hukuncin dakatarwa.

Dani Olmo, wanda yana cikin ’yan wasa shida da suka ci ƙwallo uku-uku a Euro 2024, an fara karawar da shi tare da Alɓaro Morata.

Haka kuma an fara da Lamine Yamal, wanda ya yi bikin cika shekara 17 da haihuwa ranar Asabar.

‘Yan wasa 11 na Sifaniya: Simon, Carɓajal, Le Normand, Laporte, Cucurella, Rodri, Fabian, Yamal, Olmo, Williams, Morata.

Masu jiran ko-ta-kwana: Raya, Nacho, Ɓiɓian, Merino, Joselu, Torres, Grimaldo, Remiro, Baena, Zubimendi, Oyarzabal, Jesus Naɓas, Lopez.

Ita kuwa Tawagar Ingila canji ɗaya ta yyi daga 11 da take fara wasa da su, inda Luke Shaw ya maye gurbin Kieran Trippier.

Yayin da Harry Kane ke gurbin mai cin ƙwallo da taimakon Jude Bellingham da kuma Phil Foden.

Bukayo Saka yana daga gefen gaba da kuma Marc Guehi da John Stones da kuma Kyle Walker a gurbin masu tsare baya.

’Yan ƙwallon Ingila 11: Pickford, Walker, Stones, Guehi, Saka, Mainoo, Rice, Shaw, Foden, Bellingham, Kane.

Masu jiran ko-ta-kwana: Aleɗander-Arnold, Trippier, Ramsdale, Konsa, Dunk, Gallagher, Toney, Gordon, Watkins, Bowen, Eze, Gomez, Henderson, Palmer, Wharton.

Kyaftin ɗin tawagar Ingila, Harry Kane ya karɓi kyautar takalmin zinare a Euro 2024 tare da ’yan wasa biyar a matakin waɗanda ke kan gaba a cin ƙwallaye.

Sauran da suka karɓi kyautar sun haɗa da ɗan wasan Sifaniya, Dani Olmo da na Georgia, Georges Mikautadze da na Netherlands, Cody Gakpo da na Sloɓakia, Iɓan Schranz da kuma na Jamus, Jamal Musiala.

Kane da Olmo sun buga wasan ƙarshe ranar Lahadi a birnin Berlin, amma ba wanda ya zura ƙwallo a karawar da Sifaniya ta doke Ingila 2-1.

A baya a kan tantance gwarzo, idan aka duba yawan ƙwallon da ya ci da waɗanda ya bayar aka zura a raga, amma a Euro 2024 UEFA ta ce da yawan cin ƙwallaye za ta yi amfani.

Kane, mai taka leda a Bayern Munich, mai shekara 30 ya ci Denmark da Sloɓakia da kuma Netherlands a Euro 2024.

Kane shi ne ya lashe kyautar takalmin zinare a gasar Bundesliga ta Jamus da ta wuce, wanda ya zura ƙwallo 36.

Tsohon ɗan wasan Tottenham shi ne kan gaba a yawan ci wa tawagar Ingila ƙwallaye a tarihi, kuma shi ne ya lashe kyautar a kofin duniya a 2018, wanda ya zura shida a raga.

Ɗan wasan Sifaniya da Manchester City, Rodri, shi ne ya lashe kyautar fitatcen ɗan ƙwallo a Euro 2024.

Haka kuma Lamine Yamal na Sifaniya da Barcelona shi ne matashin ɗan wasan gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana.

Jerin waɗanda ke kan gaba a zura ƙwallaye a Euro 2024;

– Dani Olmo Sifaniya – ƙwallo uku

– Georges Mikautadze Georgia – ƙwallo uku

– Cody Gakpo Netherlands – ƙwallo uku

– Harry Kane Ingila – ƙwallo uku

– Iɓan Schranz Sloɓakia – ƙwallo uku

– Jamal Musiala Jamus – ƙwallo uku

Waɗanda ke kan gaba a yawan lashe gasar kofin nahiyar Turai;

– 2020 Italiya

– 2016 Portugal

– 2012 Sifaniya

– 2008 Sifaniya

– 2004 Girka

– 2000 Belgium

– 1992 Denmark

– 1988 Netherlands

– 1984 France

– 1980 Jamus

– 1976 Czechosloɓakia

– 1972 Jamus

– 1968 Italiya

– 1964 Sifaniya

– 1960 Soviet Union