Yadda aka fafata muƙabala tsakanin Sheikh Abduljabbar da malaman Kano

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Muƙabalar da aka daɗe ana jira tsakanin Sheikh Abduljabbar da malaman Kano an yi ta a safiyar jiya Asabar a Hukumar Shari’a da ke Unguwar Nassarawa, Kano,

Tun da farko dai malaman sun bijiro da wasu tambayoyi da ba su ne suka kai wa gwamna ba, inda nan take Malam Abduljabbar ya yi ƙorafi ya ce lallai sai an kawo haƙiƙanin murya (audio) da aka kai wa gwamna ƙorafi a kai, inda ya tabbatar da cewa matuƙar ba a kawo wancan ba to ba zai ƙara amsa tambaya ko ɗaya ba.

Daga nan ne shugaban hukumar kula da sha’anin addini ta Kano, Dr. Tahir Baba Impossible ya bada umarnin ɗauko muryar da aka bai wa Gwamna tuntuni,

Muƙabalar wacce aka shafe tsawon sa’a biyar ana yi, Farfesa Salisu Shehu ne alƙalin da ya jagorancin muƙabalar.

Sheikh Abduljabbar ya bayyana cewar bai gamsu da hujjojin da aka gabatar masa ba a yayin muƙabalar.

“Abin da duk na kawo babu wanda aka warware min, da an warware min da ni da kaina zan amsa faɗuwa”, inji Sheikh Abduljabbar.

Da ya ke jawabin rufe muƙabalar shugaban zaman Farfesa Salisu Shehu, ya ce Malam Abduljabbar ya ƙi tsayawa a kan maudu’i ɗaya don samun matsaya a tsakaninsa da sauran malaman.

Ya ce, “Duk tambayoyin da aka gabatar wa Malam Abduljabbar ba ya tsayawa a kansu ya ba da amsoshinsu.

“Na farko yana cewa babu isasshen lokaci, na biyu yana cewa a tsaya a kan maudu’i guda ɗaya a yi magana, amma idan ya zo bayani sai ya dinga kewaye ba ya tsayawa a kan maudu’i guda ɗaya kamar yadda ya buƙata.”

Su ma ɗaliban Abduljabbar da muka zanta da su sun shaida mana cewa ba a yi adalci ba inda aka bari mutane da yawa su ka shiga zauren muƙabalar yayin da mutanensa aka hana su shiga, sun ce hatta masu ɗaukar masa hoto an hana su shiga,

Sun ƙara da cewa alkalin gasar ɗan Izala Salafiyya ne inda suka ce ba sa zaton da ma zai yi masu adalci.

Abin da ke nuni da zaman da aka yi ba a cim ma wata matsaya ba wadda ita ce madubin tafiyar wannan zaman, an tashi ne kowane ɓangare na nashi bayani kan zaman da aka kasa samar da daidaiton da ya kamata, domin rufe wannan ce-ce-ku-cen.

Saura da me? a yanzu dai al’umma na jiran hukuncin da gwamnati za ta yanke kan wannan zaman, sakewa za a yi ne kamar yadda Malam Abduljabbar ya nema koko dai an kammala ke nan?

Wuƙa da nama dai na hannun gwamnati wajen ganin ta samar da wata maslaha da za ta kawo haɗin kan al’umma da tafiya tare cikin mutunta juna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *