Hukuma ta kama tabar wiwi na milyan 91 ɓoye cikin tifar yashi a Legas

Daga WAKILINMU

Ofishin Hukumar Kwastam da ke Seme ya kama tabar wiwi har ƙullli 3,186 da aka ɓoye cikin yashi a cikin wata tifar ɗaukar ƙasa.

Jami’an hukumar sun kama kayan ne a babbar hanyar Seme zuwa Badagry, wanda ƙyasce kuɗin wiwin ya kai Naira milyan 91,488,977.

Jami’in hulɗa da jama’a na ofishin, Abdullahi Hussain, shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Larabar da gabata, inda ya ce sun kama kayan ne da safiyar Talatar da ta gabata.

Kazalika, Hussain ya bayyana cewa sun samu nasarar ganowa da kuma kama kayan ne sakamakon bayanan sirrin da suka samu.

Bayanan Kwastam sun nuna bayan da jami’ai suka yi wa motar binciken ƙwaƙwaf a nan aka gano buhu 41 ɗauke da ƙullin tabar wiwi guda 3,186 wanda harajinta ya kai N91,488,977.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *