Yadda aka ingiza Ganduje ya ƙi halartar zaman sulhu da Shekarau

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, bai halarci zaman sulhun da Shugaban Riƙon Ƙwarya na APC na Ƙasa kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya haɗa ba.

A Talatar wancan makon da ya wuce ne aka yi zaman sulhun na farko tsakanin ɓangaren da Ganduje ya ke jagoranta da kuma tsagin da Sanata Ibrahim Shekarau ke jagoranci.

A ranar sai aka ɗage zaman domin bai wa ɓangarori biyun damar zuwa da wata hanya ta kasafta muƙamin jam’iyya a Kano domin a samu zaman lafiya.

A zaman da a ka sake yi a Talata a gidan Gwamnan Yobe ɗin da ke Asokoro A Abuja, Shekarau ya jagoranci Sanata Barau Jibrin, Sha’aban Sharaɗa, AbdulƘadir Jobe, Haruna Dederi da dai sauran ’yan ɓangaren nasu zuwa wajen zaman sulhun.

Sai dai kuma Sanata Kabiru Gaya; Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa da ɗan Majalisar Wakilai na Wudil, HON. Ali Wudil, daga ɓangaren Ganduje sun ce sun halarci zaman ne a raɗin kansu, ba wai su na wakiltar gwamnan ba.

Sai dai kuma Daily Nigerian ta jiyo cewa, rashin zuwan Gwamna Ganduje ko kuma bayar da tashi hanyar da za a kasafta muƙaman jam’iyya ko ya aika wakili shi ya janyo tsaiko a zaman sulhun na ranar Talata.

Daga bisani ne sai jagororin zaman sulhun, waɗanda su ka haɗa da Buni, Yakubu Dogara da Sanata Abba Aji, su ka ɗage zaman sai baba-ta-gani.

Sai kuma suka bai wa Ganduje zuwa ranar Alhamis da ya sanya sabuwar ranar da za a sake zama.

Sai dai kuma wasu majiyoyi sun shaida wa Daily Nigerian cewa, Ganduje, a ranar Asabar ya kira taron gaggawa ya kuma ɗauki shatar jirgin sama zuwa Abuja, domin yanke shawarar ko ya halarci zaman sulhun ko akasin haka.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Shugaban Jam’iyyar APC na ɓangaren Ganduje, Abdullahi Abbas, sai Murtala Sule Garo da kuma dattijon jam’iyya, Alhaji Nasiru Aliko Koki.

Daga cikin manyan batutuwan da aka tattauna a zaman sun haɗa da kasafin muƙamai na jam’iyya da ɓangaren Shekarau da kuma batun qarar da suka shigar a Kotun Ɗaukaka Ƙara.

Majiyar ta ƙara da cewa, an bai wa gwamnan shawarar cewa, kar ya halarci zaman sulhun ko ya aika wakili, “saboda suna da yaƙinin samun nasara a Kotun Ɗaukaka Ƙara”.

Majiyar ta ƙara da cewa, an bai wa gwamnan shawarar cewa, bai kamata a matsayinsa na gwamna a ba shi zaɓin rabon muƙaman jam’iyya ba bayan sauran gwamnoni su ne suke juya jam’iyyar a jihohinsu.