Yadda aka kuɓutar da ɗaliban Jangeɓe da aka yi garkuwa da su

Daga FATUHU MUSTAPHA

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya bayyana cewa tubabbun ‘yan fashi ne suka taimaka wa hukumomin tsaro wajen ceto ɗalibai mata na makarantar Jangeɓe da ‘yan bindiga suka kwashe kwanan nan.

Bayan kuɓutar da su ba tare da biyan wata diyya ba, Matawalle ya karɓi ɗaliban su 279 da asubahin Talata a birnin Gusau.

A cewar Matawalle, “Wannan shi ne sakamakon shirinmu na ƙoƙarin dawo da zaman lafiya tare da kunyata waɗanda ke ra’ayin cewa babu tsaro a ƙasa.

“Tun Juma’a muke tattaunawa da ‘yan fashin inda muka cim ma yarjejeniya ranar Litinin da yamma har aka kai ga sako yaran.
 
“Mun yi murnar ganin cewa duka yaran su 279 sun dawo lafiya ƙalau, za a binciki lafiyarsu sannan a ba su abinci mai gina jiki kafin a miƙa su ga iyalansu.

“Ina roƙon iyaye kada su cire ‘ya’yansu a makaranta sakamakon abin da ya faru, za mu tabbatar da ƙarin matakan tsaro a duka makarantu.

“Sannan muna godiya ga dukkan kafafen yaɗa labarai bisa rawar da suka taka yayin wannan ibtila’in.”

Matawalle ya yi amfani da wannan dama wajen taya iyayen yaran da lamarin ya shafa da ma ‘yan Nijeriya baki ɗaya murna dangane da dawowar ‘yan mata.

Idan dai za a iya tunawa, a Juma’ar da ta gabata ‘yan bindiga suka sace ɗaliban a Sakandaren Mata da ke Jangeɓe, jihar Zamfara.