Yadda aka tirsasa ni tafka maguɗin zaɓe don APC ta samu nasara – Farfesa Yakasai

Daga WAKILINMU

Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai na Jami’ar Bayero da ke Kano, ya bayyana yadda aka tilasta masa tafka maguɗi a sakamakon zaɓe a matsayinsa na Baturen Zaɓe a yankin Tudun Wadah, Kano, yayin zaɓen da ya gudana.

Cikin wasiƙar da ya aika wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, Ibrahim Yakasai ya aibata sakamakon zaɓen da ya bayyana bayan kammala zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya.

A cewarsa, tilasta masa aka yi kan ya tafka maguɗin zaɓe bayan da aka jefa rayuwarsa cikin haɗari a zahiri.

Ya ce galibin sakamakon zaɓen da jami’an zaɓe suka bayyana ba na gaskiya ba ne.

Jaridar Jungle Journalist ta rawaito Farfesan ya jaddada cewar a shirye yake ya faɗi gaskiya ko da kuwa a bakin ransa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *