Yadda al’adar gaisuwa ke ƙarfafa zumunci

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Gaisuwa, musabaha ko kuma sallama wata halayyar ɗan Adam ce wadda ya kan yi ta hanyar yin amfani da wasu kalmomi ko wata inkiya, da sauti ko da gaɓar jiki, da nufin marabtar baƙo ko sada zumunci da girmamawa.

Akwai yanayin gaisuwa iri-iri da ƙabilu ko addinai, da zamantakewa kan sa su rungumi wata halayya ta gaisuwa da nufin mutunta juna. A wajen wasu al’ummar akan bambanta irin gaisuwar da ake yi wa babban mutum, basarake, ko talaka. Mace ko namiji, yaro ko babba. Wasu na gaisuwa ne a tsaye, tare da haɗa kafaɗar hagu da ta dama, yayin da hannun dama ke shafar ɗaya ɓangaren kafaɗar. A wajen wasu sai an goga fuskokin juna, ko sumbatar wani sashe na fuska. Akwai kuma masu rungumar juna gaba da gaba, ko kuma haɗa tafin hannu.

Idan basarake ne ko wani mutum da ake girmamawa, wasu kan dunƙule hannun dama su yi jinjina tare da xan rusunawa kaɗan. Akwai ma masu tsugunawa ko kifuwa a ƙasa a shimfiɗa jiki. Duk waɗannan nau’o’in gaisuwa ne daban-daban, ya danganta ga ƙabila ko addini, ko kuma nahiyar da mutum ya fito.

Mutane na bai wa gaisuwa matuqar muhimmanci, don yadda take ƙarfafa zumunci ko yabawa da kyawun halayya ko tarbiyyar mutum. Ana kuma jingina gaisuwa da wasu kyawawan kalmomi masu nuni da farin ciki ko kyakkyawan fata. Kamar irin gaisuwar da Musulmi ke yi ta amfani da kalmomin, ‘As Salamu Alaikum’, da kuma gaisuwar Yahudawa ta ‘Shallom’ ko ta Turawa masu cewa, ‘Hello’, ko ‘Good Morning’ idan safiya ce, ko kuma wani yanayi na cikin yini.

Idan aka yi amfani da kalmomin da ke ƙunshe a cikin gaisuwa, waɗanda ke nuni da aminci da ƙauna, a tsakanin mai tarba da mai amsawa, ana ayyana cewa, dukkan ɓangarorin sun bai wa juna ’yancin sa ta hanyar girmamawa. Amma idan kalmomin suka bambanta, abin da ake ƙudurtawa shi ne na cewa, babu cikakkiyar yarda da amincewa.

Tarihin Musulunci ya zo da cewa, a farkon bayyanar saƙon ma’aikin Allah Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata gareshi) a garin Makka, kafiran zamaninsa ba sa yarda su mayar masa da kalmomin da ya yi amfani da su na sallama ko gaisuwa da ke nuni da cewa, ‘Amincin Allah Ya Tabbata Gare ku’, amma sai su amsa masa da akasin abin da ya ambata, inda suke ce masa, ‘Mutuwa Ta Tabbata Gare ka’. Ma’ana idan ya ce, ‘Salamu Alaikum’, sai su ce masa ‘Samu Alaika’.

Akwai mutanen da ke ɗaukar cewa, duk wanda ya yi gaisuwa ko ya mayar da gaisuwa ba yadda al’adar mai sallamar ta ke ba to, akwai raini ko rashin girmamawa. Kamar misalin inda ake gaisuwa a tsugune sai wani ya yi a tsaye, ko ya canja kalmomin da ake amfani da su cikin rashin sani ko da gangan. Yayin da ambatar kalmomin ko gaisuwar yadda aka saba kuma aka amince da ita daidai, ko da kuwa ga wanda ya fito daga wata kabila, harshe ko nahiya daban ne.

Wani abu ya tava faruwa a shekarar 2011, yayin da tsohon shugaban ƙasar Amurka Barack Obama ya ziyarci qasashen Musulmi a Gabas ta tsakiya, inda a farkon jawaban sa yake farawa da sallama irin ta addinin Musulunci, abin da ya faranta ran da dama daga cikin masu sauraronsa. Haka ma yayin wata ziyara da ya kai ƙasar Isra’ila, ya yi amfani da kalmar gaisuwar Yahudawa ta ‘Shallom’, abin da ya jawo tafi da sowa mai ƙarfi daga dandazon jama’ar da ke sauraronsa.

Amma a yayin da Obama ya ziyarci ƙasar Japan inda ake amfani da al’adar rusunawa wajen gaisuwa da girmamawa. bayan musabaha ta tafin hannun dama, tsohon shugaban na Amurka ya kuma rusunawa tsohon babban sarkin al’ummar ƙasar Japan Akihito, gaisuwar da ta jawo kwakwazo da mita daga wasu manazarta a Amurka da ke ganin wannan rusunawa ba ta dace da shugaban babbar ƙasa irin Amurka ba.

Ka gani kenan, a yayin da al’ummar ƙasar Japan ke murna da girmamawar da aka yi wa shugabansu, sai ga shi hakan ya nemi zubar wa da Obama mutunci a idon ’yan ƙasarsa, saboda ganin hakan da ya yi ƙasƙantar da kimar ƙasar sa ne a wajen Japan. Dama kuwa ƙasashen biyu sun taɓa gwabza yaƙi a tsakaninsu, lokacin yaƙin duniya na biyu. Abin mamaki, sai gashi kuma an sake kwata shigen hakan a yayin da babban mai arziƙin duniyar nan ɗan ƙasar Amurka, kuma mai kamfanin Manhajar na’urar kwamfiyuta na Microsoft, wato Bill Gate, ya kai ziyarar aiki ƙasar Koriya ta Kudu cikin wannan shekara ta 2013 inda ya gana da tsohuwar shugabar ƙasar Park Geun-hye.

Nan ma ga waɗanda suke iya tunawa da labarin ziyarar tasa, an yi ta tsegunguma game da yanayin gaisuwar da shigabannin biyu suka yi, inda ‘yan ƙasar Koriya ta Kudu ke korafin cewa, a yayin da tsohon shugabar ƙasar ke musabaha da Bill Gate ta hanyar haɗa tafin hannun dama, a maimakon ya naɗe hannun sa na hagu a baya sai ya soke shi a cikin aljihun wandonsa, abin da ‘yan ƙasar da dama suka fassara da cewa, rashin girmamawa ce da nuna isa ga shugaban ƙasar ta su.

Idan muka lura da waɗannan misalai da na kawo, da ma wasun su da mai yiwuwa ta taɓa faruwa a kan idanunka ko kuma ka ji, za ka yarda da ni idan na ce maka gaisuwa jigo ce mai muhimmanci a zamantakewar al’umma. Don haka mu kula da kyau, a duk lokacin da muka haɗu da wasu baƙin al’umma, waɗanda al’adunsu da halayyar su ta saɓa wa irin tamu, lallai mu lura da yadda suke girmama junansu, da sadar da sallama ko gaisuwa a tsakaninsu ta hanyar yin koyi da su, matuƙar dai bai saɓa wa imanin mu ba.

Ko da a tsakanin mutane masu addini, aƙida, da al’ada iri ɗaya, gaisuwa cikin girmamawa tana da matuƙar tasiri da muhimmanci wajen ƙarfafa zumunci, da ƙara wa mutum daraja da kima a idon sauran jama’a. Nuna girman kai ko faɗin rai da wasu ke yi saboda tunanin sun mallaki wata dukiya ko matsayi a cikin al’umma, babban kuskure ne, kuma yana sanya katanga da nesanta mutum daga samun duk wata alfarma da za su iya nema ko buƙata. Gaisuwa, girmamawa, karramawa, halaye ne da suke da kyau, kuma ya kamata mu mayar da hankali a kai, don kyautata zamantakewar mu.

Hakan zai kara mana mutunci, aminci, da yarda a tsakanin mu. Sallama na raunata zuciyar da ƙiyayya da tsana suka yi wa qatutu. Salamu Alaikum!