Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Bayan makonni biyu da wani ɗaurin aure a jihar Jigawa ya rikiɗe zuwa tashin hankali, wanda ya yi sanadin mutuwar baƙo guda, angon kuma aka kwantar da shi a asibiti, lamarin ya ɗauki sabon salo inda aka damƙe amarya da tsohon masoyinta.
An rawaito cewa lamarin da ya faru a ƙaramar hukumar Jahun ta jihar ya ɗauki sabon salo ne biyo bayan kama amaryar da tsohon masoyinta da jami’an ‘yan sanda suka yi.
Shaidun gani da ido sun shaida cewa, mai yiwuwa an yi zargin cewa wani ɓata-gari ne ya saka amaryar aikata wannan aika-aika.
Ko da yake rundunar ’yan sandan ba ta tabbatar da dalilin da ya sa waɗanda ake zargin suka aikata wannan abu ba a hukumance, an tattaro cewa ana ci gaba da bincike kan lamarin.
Sai dai binciken share fage na ’yan sanda ya nuna cewa amaryar, Zahra’u Dauda, mai shekaru 15, da tsohon masoyinta, Lawan Musa, mai shekaru 22, sun haɗa baki ne wajen zuba guba a abincin ango.
Binciken da ‘yan sanda suka gudanar ya zuwa yanzu ya ƙara da cewa, “Angon Kamisu Haruna mai shekaru 29 da abokansa biyu sun ci abincin tare, wanda hakan ya haifar da ciwon ciki. An tabbatar da mutuwar ɗaya daga cikin abokanan a asibiti.”
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Shi’isu Lawan Adam, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ƙara tabbatar da kama mutanen biyu tare da bayyana sunayensu.
“Mun kama amaryar da tsohon masoyinta bisa zargin guba guba a abinci,” inji Adam.
“Wata Zahra’u Dauda ‘mace’ ‘yar shekara 15 a ƙauyen Bagata Gabas ta haɗa baki da tsohon masoyinta, Lawan Musa, ‘namiji’ ɗan shekara 22, shi ma ɗan ƙauyen Bagata Gabas Yamma, duk a ƙaramar hukumar Kiyawa don kashe Kamisu Haruna mai shekaru 29 da haihuwa a ƙauyen Albasu, ƙaramar hukumar Jahun,” inji kakakin ‘yan sandan.
“Mijin da abokansa biyu sun ci abincin tare, kuma a sakamakon haka, dukansu biyu sun kamu da ciwon ciki.
“An garzaya da waɗanda abin ya shafa asibiti, inda wani abokin angon ya rasu. Ana gudanar da bincike kan lamarin,” inji sanarwar SP Adam.
Don haka Adam ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike, kuma ‘yan sanda suna bakin ƙoƙarinsu wajen bankaɗo gaskiyar lamarin.
“Za mu yi duk abin da za mu iya don tabbatar da cewa an yi adalci,” inji shi.
“Al’amarin ya faru ne makonni biyu da suka gabata, kuma tun daga lokacin ne ‘yan sanda ke gudanar da bincike kan lamarin. A halin yanzu amaryar da tsohon masoyinta suna hannun ‘yan sanda kuma sashen binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sanda na yi masa tambayoyi,” inji shi.
Kakakin ‘yan sandan, Adam, ya buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu, ya kuma ba da tabbacin za a yi adalci, ya kuma ƙara da cewa, “Muna ƙoƙarin bankaɗo gaskiyar lamarin, kuma za mu yi karin bayani da wuri-wuri.
Hakazalika, kakakin rundunar ‘yan sandan ya tabbatar da cewa an sallami dukkan ma’aikatan zaurin auren da suka ci gubar daga asibiti, sai dai mutum guda da aka tabbatar ya mutu.
A halin da ake ciki, hukumar ‘yan sanda ba ta bayyana sunan abokin angon da ya rasu ba.
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta buƙaci duk wanda ke da labarin faruwar lamarin da ya fito ya taimaka wajen gudanar da bincike.