Yadda faɗuwar Peter Obi ta hana jarumi Kanayo O. Kanayo bikin zagayowar ranar haihuwar sa

Daga AISHA ASAS

Sanannen jarumi a masana’antar finafinai ta Kudu, wato Nollywood, Kanayo O. Kanayo, ya bayyana tsabar baƙin cikin sa kan yadda Peter Obi bai amshi mulkin ƙasar nan a zaɓen da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Jarumin ya bayyana lamarin a matsayin abin kunya, sakamakon yana layin waɗanda suke iqirarin an yi murɗiya a zaɓen, domin Peter Obi, na Jam’iyyar LP ne ya samu quri’u mafi rinjaye.

Kanayo ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a jiya, wanda ya yi daidai da ranar mauludin haihuwarsa cewa, zuciyarsa cike ta ke da ɓacin rai duk da zaman ranar ranar farin ciki sakamakon ƙarin shekara da ya samu, sai dai ba zai iya bayyanar da farin cikin nasa ba, sakamakon faɗuwa da ɗan takarar da yake goyon baya ya yi.

“Ba zan yi bikin murnar zagayowar ranar haihuwata ba, saboda abin kunyar da Hukumar INEC ta tabka. Ina godiya da kulawar ku masoyana, na gode da tarin saƙonnin taya murna da ku ke aiko min,” inji Kanayo O. Kanayo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *