Yadda Gasar Hikayata ta bana ta bambanta da saura

*Abu mafi burgewa da mutumta rubutu game da gasar Hikayata shi ne kyautar da ake bayarwa – Amira Souley

*Rubutu ba abu ne mai sauƙi ba, don haka ya kamata marubuta su dangwali arziƙin rubutu – Hassana Ɗanlarabawa

*Hikayata dama ce ga mata na bayyana abinda ke ci masu tuwo a ƙwarya – Maryam Muhammad Sani

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Za a daɗe ba a manta da gasar 2022 ta gajerun labarai na Hikayata da Sashin Hausa na BBC Hausa ke shiryawa marubuta mata daga faɗin Afirka duk shekara ba, musamman ma dai ga gwarazan matan da suka samu nasara a wannan shekara da makusantan su. Ba don komai ba kuwa sai don shekarar ta kasance abar tunawa ce ba ga masu shirya gasar na tashar BBC Hausa kaɗai ba, har ma da duniyar marubuta adabin Hausa.

An fara wannan gasa ne a shekarar 2016, inda duk shekara ake fitar da gwaraza uku da labaran su suka yi fice a gasar, tare da karrama su da kuma ba su kyautar kuɗaɗe da nufin tallafawa harkokin su na rubutu.

Amira

Duk shekara gasar Hikayata na ƙara samun karɓuwa sosai, musamman a wajen marubuta mata. Waɗanda ke ganin gasar a matsayin wani matakin ɗaukaka da shahara a fagen rubutun adabi. Wani abin ƙayatarwa ma shi ne, akasarin waɗanda suke samun nasara a gasar matasan mata ne, da shekarun su ba su kai 30 ba.

A bana Gasar Gajerun Labarai na Hikayata ta karɓi labarai guda 25 waɗanda marubuta mata suka aika don shiga gasar, amma daga ciki guda 15 ne aka tantance, waɗanda suka cika sharuɗɗan da aka sanya wa masu shiga gasar. Daga ciki ne kuma aka ware fitattun labarai guda uku, ‘Garar Biki’, ‘Haihuwar Guzuma’, da ‘Al’ummata’. Waɗanda a cikin su ne aka fitar da gwarzuwar farko, ta biyu da ta uku, da aka gayyace su Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja don karvar shaidar karramawa da wasu maƙudan kuɗaɗe, albarkacin nasarar da labaran su suka samu, a wani ƙayataccen buki da aka shirya. Sauran labarai 12 da ba su samu damar hayewa matakin farko ba, an ba su shaidar shiga gasar Hikayata su ma.

Amira Souley Malam Salifou daga Jihar Maraɗi a Jamhuriyar Nijar, marubuciyar littafin ‘Ma’aurata’, ita ce ta zama Gwarzuwa a gasar Hikayata ta wannan shekara ta kuma bayyana cewa, “Gasar BBC Hausa ta bambanta da sauran gasanni, tsari da dokokinta kawai abin burgewa ne, musamman yadda alƙalan gasar suka yi bayanin yadda ake tafiyar da tsarin alƙalancin, wanda shi ma kawai ya isa ya tabbatar da akwai adalci a ciki. Sannan zavar ƙwararru yayin alƙalancin shi kansa adalci ne, yadda BBC ta haramtawa ‘yan uwan ma’aikatanta shiga gasar shi ma adalci ne, sai kuma abu mafi kyautatawa, burgewa haɗe da mutumta rubutu da marubuci shi ne kyautar da suke bayar wa ga gwaraza ukun farko, bayan ɗaukaka da suka samu.”

Ita kuwa Gwarzuwa ta biyu a wannan gasa, kuma marubuciyar littafin ‘Mayafin Sharri’, Hassana Labaran Ɗanlarabawa daga Jihar Kano a Nijeriya cewa ta yi,”Gasar BBC Hausa Hikayata uwa ce ga kowacce gasa, musamman ga marubuta mata, saboda tana bayar da dama ga mata suna fito wa da batutuwan da ke danƙare a zukatansu. Sannan tana ɗaga darajar marubuta mata a idon mutanen da suke ganin marubuta mata ba su da basira ko fikra. BBC Hausa ta karrama su da ingantattun labaran da duk shekara marubuta mata ke rubutawa su shiga da su.”

A ganin Maryam Muhammad Sani da aka fi sani da Mum Amnash, marubuciyar littafin ‘Yan Matana’, wacce ta zama Gwarzuwa a mataki na uku a Gasar Hikayata ta 2022, daga Jihar Kano, “Babu gasar da ta kai gasar BBC Hausa duk da dai ta mata ce zalla, duba da yadda ake bai wa mata damar zaƙulo matsalolin da ke ci musu tuwo a ƙwarya.”

Bayan yabawa da tsarin gasar, waɗannan gwarazan marubuta har wa yau sun bayyana jin daɗin su game da kyautar tallafin kuɗi da karramawa da BBC Hausa ta yi musu.”Wani abu da ya ke ƙara wa gasar kwarjini shi ne, yadda BBC Hausa ke mutumta rubutu da marubuci, ta dalilin kyautar da suke bai wa gwaraza ukun da suka yi nasara, bayan ɗaukaka da suka samu, kuma hakan ya kan zaburar da marubuta mata sosai.” Cewar Amira Souley.

Ita ma Hassana ɗan Larabawa ta jinjina wa wannan gagarumin tukwuici da BBC Hausa ke bayarwa, inda ta ce.”Babu wata gasa da a yanzu ta ke bayar da tukwicin da ya zarce na BBC, sai dai ƙasa da ita. Muna fatan a samu waɗanda za su yi koyi da BBC Hausa, ko ma su zarta ta, wajen shirya gasannin rubutu don hidimta wa Adabi, da saka tukwici mai tsoka, ta yadda marubuta da dama za su kasance sun rabauta da tagomashin wata Awalaja, domin kuwa rubutu ba abu ne mai sauƙi ba. A saboda haka nake ganin ya kamata marubuta su dangwali arziƙin rubutu.”

Wani abu da ke kaɗa hantar cikin marubuta mata, musamman sabbin marubuta masu tasowa da ke sha’awar shiga gasar Hikayata shi ne gindaya sharuɗɗan bin ƙa’idojin rubutu da ake buƙata daga kowacce marubuciya da samar da jigon labari mai muhimmanci da tasiri ga rayuwar al’umma. Yaya waɗannan marubuta mata suka samu kansu kafin shiga gasar da bayanta? Waɗanne ƙalubale suka fuskanta?

Amira Souley wacce mamba ce a ƙungiyar marubuta ta Nagarta da ke da tushenta a Nijeriya, bayan ƙungiyar da ta kafa ta marubutan adabi a Ƙasar Nijar, wato Madubi. Ta ce, sau biyu tana shiga Gasar Hikayata ta BBC Hausa, a 2021 da kuma 2022, wanda shi ne ya ba ta nasarar zama ta farko, da labarin ta na ‘Garar Buki’.

Hassana

Ta qara da cewa, “Ubangiji ne ya amshi roƙona ba wayona ko dubarata ba. Ni dai na san na natsu na yi rubutu mai kyau tare da kiyaye dokokin da BBC Hausa suka gindaya a kan gasar, sannan na yi ta addu’a, idan na ce addu’a ba fa addu’a ýar kaɗan ba. Har azumi da ƙiyamul laili duk sai da na yi cike da yaƙini, kuma Alhamdulillah, kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

“Ba zan taɓa mantawa da wata ranar Alhamis ba, na farka daga barcin rana kenan sai ga kiran waya, ina dubawa sai na ga kod ɗin Nijeriya, a nan aka mini albishir ɗin kasancewa cikin gwarazan Hikayata na 2022. A gaskiya na shiga cikin maɗaukakin farin ciki, kuma ranar ta shiga cikin ranakun farin ciki da ba zan manta ba a rayuwata.”

A nata ɓangaren, Hassana Ɗanlarabawa, wacce ita ma ta shiga gasar sau biyu cewa ta yi, “na fara shiga gasar BBC Hikayata a shekarar 2021, amma gaskiya a wancan lokacin ban san ƙa’idojin shiga gasar ba, kawai na yi rubutu ne na bayar aka duba mini, sai na shiga. Sai dai Allah bai nufa na samu nasara ba. Sai a wannan shekarar na sake yunƙurin shiga, amma a wannan karon na shirya mata sosai. Saboda na yi ƙoƙari na nemi sanin ƙa’idojin rubutu yadda ya kamata, don na iya rubutu bisa ƙa’idar da ake buƙata a gasar.

A wannan shekarar na yi rubutu mai kyau fiye da wancan lokacin, na kuma jima da yin rubutun yana ajiye, kullum Ina dubawa Ina sake yin gyare-gyare. Bayan an yi sanarwar fitar da wata gasar marubuta a bana, sai na ɗauki labarin na ba wa wani marubuci ya duba mini, bayan ya duba kawai sai ya jinjina min, ya ce labarin ya yi sosai, kuma ya ba ni wasu shawarwari kan labari.

Bayan hakan da wasu kwanaki sai na ga sanarwar sabuwar gasar Hikayata ta BBC Hausa da aka fito da ita, kamar ma ba zan shiga ba, sai aka ba ni shawara kan na shiga. Ana saura kwana ɗaya a rufe gasar na zauna cikin awa ɗaya da rabi na rubuta labarin gasar, na saka masa suna ‘Haihuwar Guzuma’. Har zan tura, sai na dakata na sake ɗaukar labarin na bai wa wani babban marubuci don ya duba mini, don shi na ba wa wancan labarin ya duba min, bayan ya karanta wannan din sai ya ce: “Wallahi Ina jin ba ki taɓa rubutun labari mai daɗi irin wannan ba, shawarata ki shiga gasar Hikayata da shi, in sha Allahu za a dace.”

“Na yi matuƙar mamaki da na ji hakan daga gare shi, a ganina wancan labarin da na kwashe kusan wata takwas da rubuta shi, kullum Ina duba shi Ina yi masa gyara, amma wannan cikin awa ɗaya da rabi da na rubuta har ya zarta wancan komai? Bayan shi, kusan mutum biyu suka sake duba labaran, kuma duk suka nuna ‘Haihuwar Guzuma’ ya fi cancanta fiye da wancan. Ni ma sai na yi amanna tun da mutum ba ya ƙin ta mutane, na shiga da shi, sai ga shi kuma an dace cikin ikon Allah.”

Labarin Maryam, Mum Amnash, da ta zama Gwarzuwa ta uku abin mamaki ne, domin kamar yadda ta faɗa ta sha shiga gasar gajerun labarai na marubuta, amma ba ta tava samun nasara ba, duk ƙoƙarinta na bin ƙa’idojin rubutu. Sai a wata gasa da ƙungiyar marubuta ta Jarumai ta shirya, albarkacin cika shekaru biyu da kafuwar ƙungiyar.

Ta ce, “Ban da gasar Hikayata sau ɗaya na taɓa samun nasara a gasar rubutu ta Ƙungiyar Jarumai Writers Association. Amma kafin nan na shiga gasanni da dama da ba za su ƙirgu ba daga ciki akwai gasar da ake gabatarwa a zauren ‘Marubuta’ wadda Bamai Dabuwa yake ɗaukar nauyi, Nana Aicha ta ja ragamar kula da ita, na shiga ya kai sau goma duk wata ban tava fashi ba, kuma ban samu nasara ba. Hasali ma akwai watan da wadda ta yi nasara da maki ɗaya ta fi ni. Amma abin da na saka a raina shi ne, idan da rai da rabo.”

“Na samu labarin buɗe wannan gasa a kafafen yanar gizo da zaurukan WhatsApp. Tun daga lokacin da na samu labarin za a gudanar da wannan gasa ta Hikayata a wannan shekarar, sai na fara tunanin labarin da zan ƙirƙira na rubuta, amma ban samu damar rubutawa ba sai a ƙasa da awa ashirin da huɗu a rufe gasar.

Sai da na kammala rubuta labarin, na gano na haure adadin kalmomin da suka ƙayyade, sai na rage sannan na turawa malamata Nana Aicha Hamissou jikina a sanyaye, a lokacin har Ina tunanin goge shi na sake wani. Kalaman da ta rubuto min, su ne suka ƙarfafa min gwiwa har na tura labarin tare da fatan na kasance cikin mutane 12 da za su rabauta da samun takardar karramawa daga BBC Hausa.

“Lokacin da suka fitar da labarai 25 na farko, labarina mai taken ‘Al’ummata’ shi ne ya zo na uku a jerin sunayen labaran, amma ban iya gane shi ba, hasali ma ko sunansa ban kula da shi ba, sai da malamata Aicha da Amira suka tuna min. A tsawon kwanakin da aka ɗauka na yi su ne cikin fargaba da addu’ar neman zavin Allah. Kwatsam! Na samu kira daga wani ma’aikacin BBC wanda ya sanar da ni labarina na daga cikin uku da aka zaɓa. Na yi godiya ga Allah, na yi farin ciki matuƙa gaya da wannan nasarar a lokacin da ban taɓa zato ko tsammani ba a matsayina na ƙaramar marubuciyar da yanzu ne nake rarrafawa.”

Wannan nasara da waɗannan marubuta mata suka samu ta zama musu sanadin ƙara samun ɗaukaka, kuma babban abin alheri a rayuwar su. Ganin yadda ba ma jama’ar ƙasa ba, waɗanda ke bibiyar al’amuran yau da kullum, hatta masu karatu da masharhanta harkokin adabi sun nuna jin daɗin su da farin cikin su da wannan nasara da gwarazan marubuta Nijeriya da Nijar suka samu, babu ma kamar su kansu marubuta da suka riƙa tururuwar gaisawa da ɗaukar hoto da su.

Marubuci Mukhtar Musa Ƙarami da aka fi sani da Abu Hisham ya yi wani rubutu a shafin sa na WhatsApp inda ya bayyana mamakin sa da irin yadda dandazon marubuta da masoya suka yi dogon layi suna jiran damar su ta zo ta yin hoto da gwarazan Hikayata da suka halarci wani taron marubuta, jim kaɗan da komawar su Kano, bayan taron ba da shaidar karramawa da nasarar da suka samu, wanda BBC Hausa ta shirya a Abuja. Kai ka ce ba su ne marubutan da aka saba ganin su a tarukan marubuta, makaranta da gidan buki ba!

Ya rubuta cewa, “Na fi mintuna 10 Ina bin layin ɗaukar hoto da gwarazan gasar BBC Hausa ta Hikayata da ƙyar na samu aka ɗauka da ni. Lallai nasara aba ce ta musamman da kowa ke kwaɗayin a danganta shi da ita!”

Sai dai duk da wannan turmutsitsi da cinkoso da aka riƙa gani a Kano don yin ido biyu da waɗannan gwarazan marubuta, sai da jama’a suka sha mamaki da ta’ajibin irin tarbar da gwamnati, masarauta da jama’ar Nijar suka nuna a lokacin komawar Gwarzuwar shekarar 2022 ta BBC Hausa, Amira Souley gida Maraɗi. Domin kuwa Gwamnan Jihar da Magajin Garin Maraɗi da sauran dandazon jama’a masoya da suka je tarbar ta. Duk kuwa da kasancewar ba ita ce kaɗai ýar Nijar da ta tava samun irin wannan nasara ba. Domin kuwa, a shekarar da ta gabata ma 2021 wata ýar Nijar ce wacce kuma ita ma ýar Jihar Maraɗi ce, Nana Aicha Hamissou, ta zama Gwarzuwa ta biyu a gasar Hikayata ta BBC Hausa.

“Ba zan tava mantawa da irin tarba ta girmamawa da gwamnan jiharmu tare da Magajin Gari suka shirya domin tarba ta ba, tun daga wani ƙauye kafin shigowa Maraɗi. Bayan an karrama ni kuma aka sa jami’an tsaro suka raka ni har cikin gida. Wannan abu ya yi matuƙar faranta min rai sosai.”

Wannan abin alfahari da burgewa da al’ummar Nijar suka yi wa wannan baiwar Allah ya ja hankalin mashahurin malamin adabin nan, marubuci kuma ɗan jarida, Farfesa Ibrahim Malumfashi wanda har ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa,” Wallahi ba ka ji daɗin da na ji ba ganin hukuma da sauran al’ummar Jihar Maraɗi sun rungumi wannan Gwarzuwar da kuma aikin da ta yi wa adabin Hausa, hannu bibiyu. Ban tava ji ko ganin inda wata jiha ko al’umma ta karrama wata da ta taɓa zama Gwarzuwa a irin wannan gasar ba tun da aka fara ta a 2016. Mutanen Nijar kun burge ni, adabin Hausa na godiya!”

A Nijeriya ma marubuta sun nuna kara da yabawa ta hanyar nuna farin cikinsu da jin daɗi ga abin alherin da ya sake samun wasu daga cikin su. Hassana Ɗanlarabawa ta faɗa cewa,”Ba zan manta da irin tarin ƙauna da soyayya da na gani daga wurin jama’a, iyaye, dangi, ƙawaye, marubuta, da masoya ba. Na ga abin mamaki daga gare su wanda baki ba zai iya furtawa ba, hannu ba zai iya rubutawa ba, hasashe ba zai iya kintace ba. Sau da dama idan na tuna sai dai na ji hawayen farin ciki ya zubo mini, sai kawai na furta kalmar, ‘AlhamduLillah!'”

Daga ɓangaren Mum Amnash kuwa wani abu ne na tarihi da ya zama kamar mabuɗin alheri da cigaban rayuwa. “A sanadinta na taɓa zuwa Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja. A sanadinta na tava hawa jirgin sama. A sanadinta na fara samun dunƙulalliyar kyauta mai girma. Amma duk waɗannan ba su kai farin cikin da na ji da tarin fatan alkhairi da soyayyar da masoya, makaranta, marubuta, ‘yan uwa da ƙawaye suka nuna min ba. Lamari ne da ba zai tava goguwa a tarihin rayuwata ba.”

A yayin haɗa wannan nazari, Gamayyar ƙungiyoyin Marubuta ta Jihar Kano wato GAMJIK, na can na shirye shiryen wani gagarumin taro na taya murna ga marubutan da suka samu wannan nasara, a mataki na biyu da na uku, Hassana da Maryam, waɗanda duk ýan Jihar Kano ne. Shugaban ƙungiyar Mubarak Abubakar Idris ya bayyana cewa, an shirya taron ne domin taya su murna da karrama su bisa nasarar da suka samu, a matsayin su na ýan uwa marubuta kuma mambobin su, da ake gudanar da harkokin rubuce rubucen adabi tare.

Maryam

Ga sauran mata marubuta da ke da burin su ma su shiga cikin wannan gasa kuma su samu nasara. Amira dai cewa ta yi, “Su yi ƙoƙarin bin dokokin da BBC Hausa suka gindaya a kan gasar, su yi rubutu mai inganci da yake daidai da rayuwa, sannan su yi addu’a.”

“A dage da neman ilimin rubutu, domin a rubuta abu mai kyau, a naƙalci ginin gajeren labari tun daga farko, tsakiya da ƙarshe, a zaɓi jigo mai kyau da ɗaukar hankali idan gasar ta kasance babu tsayayyen jigo. Idan kuma da jigo sai a yi ƙoƙarin tsayawa ga jigon kar a bauɗe. A ƙawata labari da salo da azanci, irin su Karin Magana da Adon Harshe, a kiyaye da ƙa’idojin rubutu, da kuma ganɗoki don labari ya yi armashi ga alƙalan da za su nazarce shi.

“A tabbatar an bibiyi ƙa’idojin shiga gasar sosai kafin a shiga, domin kuskure ɗaya yana iya kawar maka da nasara. Sannan kafin ka tura labarin ka ba wa wani masani ya duba maka, ko akwai wani gyara da zai hango wanda kai da ka rubuta labarin qila ba ka hango ba.” Cewar Hassana.

Ita kuwa Maryam fatan alheri ta yi wa sauran marubuta mata, inda ta ce, “Shawarar da zan bai wa ‘yan uwana mata ita ce, su nutsu su fara gane su wanene su? Daga ina suke? Ina za su a duniyar rubutu? Su daure su nemi ilimin rubutu, su girmama ma’abota ilimin, don su kwashi romon ilimi. Sannan su dage da addu’a, su yi aiki tuƙuru in sha Allahu za su dace!”