Yadda gasar karatun Alƙur’ani ta gudana a Legas

Daga DAUDA USMAN a Legas

Wata ƙungiya mai suna, Lajnatul Musabuƙatul Ƙur’anil Kareem a ƙarƙashin ƙungiyar jama’atul Izalatul bidi’a reshen jihar Legas, ta gudanar da gasar karatun Al-Ƙura’ani Mai tsarki a jihar Legas.

 Taron musbaƙar ya gudana ne a unguwar Agege ta jihar Legas. Hakazalika, taron ya samu halartar waɗansu daga cikin Makarantun Islamiyyoyi na cikin garin legas da kewayenta bakiɗaya. Ɗaliban sun kasu kashi-kashi. Akwai waɗanda za su yi gasar karatun izifi sittin, da masu gasar karanta Izifi ashirin, da sauransu.  

Maƙasudin taron shi ne, don a ƙara zaburar da ɗaliban a wajen neman ilimin addinin musulunci da Kuma fafatawa a tsakaninsu, domin nemo zakara wanda zai samu matsayi ma fi daraja a  gasar karatun.

 Taron ya samu tubarrakin, Shugaban kwamitin gudanar da Taron karatun musabaƙar, Imam Isma’il Umar Limamin masallacin jumma’a na unguwar  Apapa; da Imam Sulaiman Ibrahim, babban limamin masallacin jumma’a na rukunin gidajen unguwar 1004, a tsibirin Victoria Island, wanda Kuma shi ne shugaban ƙungiyar Izala na jihar Legas; da kuma uban qungiyar Izala a legas bakiɗaya, Alhaji sani sambo Agege; da Alhaji Bashir Abdulsalam Toron Bade, Gashuwa ta Jihar Yobe; da Alhaji Ibrahim Garba Tafida Sarkin Samarin Agege waɗanda su ne suka haɗa hannuwa suka gabatar da Taron.

An gudanar da taron a  a ranar Lahadin ƙarshen makon jiya.

Da yake gudanar da jawabinsa a wajen taron, Uban ƙungiyar  Izala a Legas, Alhaji Sani Sambo Agege, ya  yi wa manyan baƙin da suka samu zuwa, maraba. Sannan ya ƙara da cewa, daman ƙungiyar Izala a Legas tana shirya irin wannan taron na gasar karatun Al-Ƙura’ani mai tsarki, kuma take  gudanar da shi a dukkan ƙarshen shekara. A cewar sa, wannan karon ne aka fara kawo taron unguwar Agege domin su zaburar da Iyayen yara domin su dage da sa ‘ya’yansu a Makarantun Islamiyya. Sannan kuma a kuma ƙara wa su kansu yaran ƙwarin gwiwar tsayawa su yi karatu. 

Alhaji Sambo Agege ya ƙara da cewa, a kan haka yake ƙara shawartar al’ummar musulmin Agege da Legas da ma Nijeriya bakiɗaya da su ƙara ƙoƙari wajen sanya ‘ya’yansu a makarantun Islamiyya da ma na Bokon bakiɗaya.
Shi ma a nasa tsokacin a wajan

Shugaban majalisar malamai na ƙungiyar Izala a Legas, Sheikh Malam Abubakar Mohammed Argungu,  ya bayyana jinjinawarsa ga ‘yan kwamitin ƙungiyar ta Izala a Legas waɗanda suka shirya wannan taro. Domin a cewar sa sun yi  amfani da kaifin hankalin da Allah ya ba su wajen shirya gasar karatun. inda ya yi fatan Allah ubangiji ya ƙara masu basira gabaɗaya.

 Haka shi ma Shugaban ƙungiyar Izala a Legas, Imam Sulaiman Ibrahim, shi ma ya yi wa manyan baƙi barka da zuwa, sannan ya ƙara da nuna godiyarsa ga al’ummar musulmin unguwar Agege da na jihar Legas saboda rawar da suka wajen gudanar da taron  gasar karatun Al-Ƙura’ani Mai tsarki. Da fatan Allah ya saka wa kowa da Alheri. 

Amiru Idiris Dan asalin ƙaramar hukumar Kafur kuma mazaunin unguwar Ajegulle a Legas shi ne ya samu nasarar lashe gasar a cikin jerin waɗanda suka yi gasar karanta izifi sittin.

Jama’a da dama sun yi jawabi  da sanya albarka ga al’ummar musulmin jihar Legas tare da kira ga iyayen yara da su cigaba da sanya yaransu a makarantun Islamiyya da Bokon bakiɗaya.