Yadda gobara ta kaƙume gidan mai a Legas

Daga BASHIR ISAH

A ranar Laraba aka samu tashin gobara a gidan man Mobil da ke Alakara, Idi Oro, Mushin a birnin Legas.

Bayanai sun nuna gobarar ta tashi ne da tsakar rana daidai lokacin da ake ƙoƙarin sauke fetur da aka kawo wa gidan man.

An ce gobarar ta faɗaɗa har zuwa wani bene mai hawa uku da ke kusa da gidan man.

A cewar Hukumar Bada Agajin Gaggawa (NEMA), babu wanda ya ji ciwo, haka ma babu hasarar rai sakamakon gobarar.

Ya zuwa haɗa wannan labari, an ga jami’an kwana-kwana suna ta ƙoƙarin kashe gobarar a nan gidan man da kuma ginin bene ukun da gobarar ta taɓa.

Sai dai jami’an sashen kula da iftila’i na rundunar ‘yan sandan Legas sun killace gidan man da lamarin ya shafa.

Bayanai sun nuna cewa cikin ramuka 4 da tankar man ke da su masu ɗauke da litar fetur 33,000, gobar ta soma ne a daidai lokacin da ake ƙoƙarin sauke rami guda daga cikin ramuka huɗun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *