Yadda harin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna ya rikita Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIDA a Abuja

A cikin ‘yan kwanakin nan Jihar Kaduna na fuskantar matsanancin kai hare-hare daga ‘yan fashin daji, inda suka addabi wasu yankunan jihar. ‘Yan bindigar sun fito da sabon salon kai hare-hare a tashar jirgin sama da kuma hanyar titin jirgin ƙasa, kamar yadda ‘yan bindigar suka kai wa jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna cikin satin nan.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutane takwas, yayin da mutane 26 suka samu raunika, wasu kuma aka neme su sama ko ƙasa babu labari, a harin jirgin ƙasan mai ɗauke da fasinjoji kusan 1000 a daren Litinin.

Jirgin wanda ya bar Abuja da misalin ƙarfe 6:00 na yamma, kuma aka kai masa hari a tsakanin Kateri da Rijana, inda ‘yan bindigar suka dasa wani abu da ake kyautata zaton bam ne, sannan suka buɗe wa jirgin wuta.

Kwamishina Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar Kaduna, Mista Samuel Aruwan, a jawabin da ya yi Talata, ya ce: “Gwamnatin Jihar Kaduna ta karɓi sunaye da bayanan fasinjojin da suka hau jirgin daga Abuja zuwa Kaduna a ranar daga Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa ta Nijeriya (NRC), wanda ‘yan bindiga suka kai wa hari Litinin.

“A bayanan da muka samu, fasinjoji 398 ne suka sayi tikitin tafiya, amma fasinjoji 362 ne kawai suka shiga jirgin yadda yake a ƙa’ida. Amma sai dai fansinjojin da harin ya shafa ban da ma’aikatan Hukumar NRC da kuma jami’an tsaron da ke cikin jirgin.
“Jami’an tsaro sun bada rahoton mutuwar fasinjoji takwas, yayin da mutane 26 suka samu raunika yayin harin. Har yanzu ana cigaba da gudanar da bincike don gano tabbacin adadin fasinjojin da suka hau jirgin don ganin an ceto rayukan su.

“Kowane ɗan ƙasa zai iya tuntuɓar Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna akan lambar waya 09088923398 domin tuntuva ko bada bayanin wani fasinja da harin jirgin Abuja zuwa Kaduna ya rutsa da shi,” cewar Aruwan.

Mutanen da suka mutu da waɗanda suka samu rauni:
A cikin harin da ‘yan bindigar suka kai, ya rutsa da Babban Sakatare na Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa ta Ƙasa (TUC), Kwamared Musa Lawal Ozigi da kuma shugaban ƙungiyar reshen Jihar Kwara, Kwamared Akin Akinsola, wanda dukkan su ya yi sanadiyyar rasa rayukansu.

A jawabinsa, shugaban TUC, Kwamared Quadri Olaleye ya ce mamatan suna kan hanyar su ne ta zuwa Kaduna domin gudanar da aikin ƙungiyar su ranar Talata 29 ga Maris, 2022.

Da yake nuna damuwarsa kan lamarin, Olaleye ya roqi gwamnati a dukkan matakai da ta tashi tsaye wajen kare rayukan ‘yan Nijeriya.

“Muna kira ga gwamnati a dukkan matakai, musamman Gwamnatin Tarayya da ta tashi tsaye wajen magance kashe-kashen ‘yan Nijeriyan da ba su ji ba, ba su gani ba. Kamar dai yanzu, babu wani wuri a Nijeriya da za ka iya zama lami lafiya, ba a iya tafiya ta jirgin sama ko ta hanyar mota, ga kuma ta jirgin ƙasan ita ma. Shin Nijeriya ta gaza? Wannan ba ƙaramin abin kunya ba ne.

“Ƙungiyar mu tana yi wa iyalai da abokan ‘yan uwan mu Kwamared da kuma al’ummar Jihar Kogi ta’aziyyar wannan babban rashi. Allah ya gafarta musu.”

Haka kuma a cikin waɗanda harin ya rutsa da su kuma ya yi ajalinsu, akwai wata ƙwararriyar likita Chinelo Megafu da ke aiki a asibitin St Gerald.
Haka zalika, harin ya rutsa da Darakta a Ma’aikatar Kula da Ilimin Fasaha ta Ƙasa (NBTE), Abdu Isa Ƙofar Mata, wanda wani ɗan uwansa ya ce ya rasu ne sakamakon harbin da ‘yan ta’addan su ka yi masa.

A cewar sa, tuni an yi masa jana’iza a Kano kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Ɗan uwan nasa ya ce marigayin, ɗan shekara 55, ya rasu ya bar mata ɗaya da ‘ya’ya 4.

Har wa yau, cikin waɗanda harin ya shafa, akwai Manajan Darakta na Bankin Manoma (BOA), Alwan Hassan da ɗan uwansa duk suna daga cikin waɗanda aka nema sama ko ƙasa aka rasa, inda shi kuma tsohon mataimakin gwamnan Jihar Zamfara, Malam Ibrahim Wakkala ‘yan bindigar suka harbe shi a ƙafa wanda yanzu haka yake cigaba da samun kulawa a asibiti.

Hassan, wanda aka dinga kiran wayar sa a kashe, ana kyautata zaton yana ɗaya daga cikin waɗanda maharan suka yi awon gaba da su.

Shi ma kwamishinan lafiya na Jihar Katsina, Injiniya Yakubu Nuhu Ɗanja na daga cikin mutanen da harin ‘yan bindigar ya rutsa da su, inda majiyoyi daga asibitin sojoji na 44 da ke Kaduna suke tabbatar da hakan.

Hafsan Sojin Ƙasa ya ziyarci inda aka kai harin:
Babban Hafsan Sojin Nijeriya (COAS), Laftanar-Janar Faruq Yahaya, ranar Talata ya ziyarci wajen da aka kai harin, kuma ya umarci rundunar soji da su kakkaɓe dukkan ‘yan bindigar da ke yankin

Ya samu rakiyar wasu manyan sojoji daga hedikwatar sojoji ta ƙasa da kuma babban kwamandan runduna ta 1.
Bayan dudduba irin ɓarnar da maharan suka yi, Hafsan Sojin ya kuma umarci rundunar sojin Nijeriya da sauran jami’an tsaro da su tsananta bincike da gudanar da aikin su domin kamo ‘yan ta’addan da kuma ceto rayukan waɗanda aka yi garkuwa da su.

Martanin Jam’iyyar PDP:
A cikin martanin da Jam’iyyar adawa ta PDP ta yi, ta bayyana kaɗuwarta da tagwayen hare-haren da ‘yan bindigar suka kai wa jirgin ƙasa, inda ta ta bayyana hakan da ‘abin da bai taɓa faruwa ba a tarihin Nijeriya’.

A jawabin sa, Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Kaduna, Hon. Felix Hassan Hyat, ya ce “Jam’iyyar PDP ta kaɗu da jin wannan mummunan labari na harin da ‘yan bindiga suka kai wa fasinjojin ranar Litinin. Wannan na zuwa ne kusan awa 24 bayan da ‘yan bindiga suka kai hari a filin sauka da tashin jiragen sama na qasa da ke Kaduna, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wani ma’aikacin Kula Da Zirga-zirgar Jiragen Sama (NAMA).

“An kai lokacin da ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda sun karve duk wani iko na ƙauyuka, manyan tituna, sai kuma yanzu da suka cin karen su babu babbaka a a hanyar jirgin sama da na qasa, abinda bai taɓa faruwa ba a tarihin Jihar Kaduna. Ana cigaba da karkashe rayukan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba, suna ta yin hijira suna barin ƙauyukan su ganin yadda ‘yan bindiga ke faɗa musu ba dare ba rana, kuma babu wata alama da ke nuna ‘yan bindigar sun fara rage ƙaddamar da kai hare-haren su, ko kuma abinda zai tabbatar da gwamnatin APC a jihar tana yin wani abu da zai nuna tana son kawo ƙarshen ‘yan bindigar.

“Matsalar tsaron da jihar ke fuskanta yanzu ba shi ne al’ummar Jihar Kaduna suka yi zato ba. Babu wanda ba zai yi mamaki ba, shekaru bakwai da suka wuce, babu wanda zai ce ‘yan bindiga za su mamaye garuruwa da manyan hanyoyi, bare kuma titin jirgin ƙasa. Wannan babbar gazawa ce ga gwamnatin da ya kamata ta kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Ba za mu yarda da wannan ba.”

Me Buhari ya ce wa hafsoshin tsaro?
Da yake nuna takaicin sa, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da harin da ‘yan bindigar suka kai wa jirgin ƙasan, inda ya umarci a ɗauki dukkan matakan da suka dace wajen ganin an tsaurara tsaro tare da sanya ido don ganin an kawo gyara mai ma’ana akan titin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna

Haka kuma, ya bada umarnin a yi amfani da tsarin wajen ganin ita hanyar jirgin ƙasan Legas zuwa Ibadan ta samu kyakkyawan tsaro kamar yadda sanarwar da Kakakin sa, Malam Garba Shehu ya fitar.

Shugaban ƙasa ya bada wannan umarnin ne a Abuja ranar Talata, a lokacin da yake jin ba’asi daga Hafsoshin sojin ƙasar nan, wanda Babban Hafsan Tsaron ƙasa, Janar Lucky Irabor da Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar-Janar Faruq Yahaya da Babban Hafsan Sojin Sama, Air Mashal Isiaka Amao suka jagoranta.

Taron wanda ya gudana a Fadar Shugaban Ƙasa, ya samu halartar Sufeto-Janar na Ƙasa, Usman Alkali Baba da CDI, Manjo-Janar Samuel Adebayo da kuma Darakta Janar na Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS), Yusuf Magaji Bichi.

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, a cikin jawabinsa, ya umarci hafsoshin sojin da su yi duk mai yiwuwa wajen ganin an ceto dukkan fasinjojin da aka yi garkuwa da su da kuma farauto ‘yan bindigar da suka kai mummunan harin don fuskantar matakin shari’a.

Duk a cikin takardar da Kakakin nasa ya wallafa, Buhari ya yi Allah wadai da jefa wa fasinjoji bom a cikin jirgin, inda ya bayyana hakan da “kabari kai tsaye.”

“Kamar kowane ɗan Nijeriya, Ni ma ina tsananin jin zafi da damuwa akan wannan al’amari, na biyu kenan irin sa, wanda kuma ya yi sanadiyyar rasa rayukan fasinjojin da har yanzu ba a ƙididdige ba, tare kuma da raunata wasu.

“Harin jirgin ƙasan wanda shi ne hanya mafi kwanciyar hankali ga mutane da dama abin takaici ne da Allah wadai ƙwarai da gaske, muna jajantawa iyalan waɗanda suka rasu da kuma yi wa waɗanda suka samu raunika addu’ar samun sauƙi,” ya ce.

Yadda Majalisar Dattawa ta nuna damuwa kan harin:
Haka zalika, Majaljsar Ƙasa ta nuna matuƙar damuwarta akan abinda ta kira da ‘ƙamarin matsalar tsaro da ya dabaibaye ƙasar.

Majalisar ta yi kira ga sojoji da sauran jami’an tsaro na Nijeriya da su ɗaura ɗamarar yaqi da ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane don kawo ƙarshen kashe-kashen al’umma da ake yi babu gaira babu dalili.

Sun yi kira musamman ga sojojin ƙasa da na sama, da su haɗe kai don ganin sun kawar da duk wasu shaiɗanun ‘yan ta’adda a ƙasar nan
Kiran ya zo ne daidai lokacin da ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Uba Sani ya gabatar da ƙudirin gaggawa akan matsalar tsaron da ke addabar jihar sa.

Sanata Uba Sani wanda ya yi amfani da doka ta 41 da 51 ta dokokin majalisar dattawa an yi muhawara akan ƙudirin kuma an yi kira ga jami’an tsaro da su shawo kan matsalar tsaron jihar Kaduna, inda ya ce abin damuwa ne a kowace rana da ake kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Ya ce: “A cikin satin da ya gabata, ‘yan ta’adda ko ‘yan bindiga sun kai hari a jihar inda suka kashe mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a kayan gwamnati, sai na kwanan nan wanda suka kai hari kan jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna ranar Litinin cikin dare, inda suka yi garkuwa da fasinjoji da dama tare da hallaka wasu. 

“Akwai kuma wasu hare-haren kwanan nan da ‘yan bindigar suka kai wasu ƙauyuka a Ƙaramar Hukumar Giwa, irin su Unguwar Sarki Yahya, Tashar Shari, Bare-bari, Tsaunin Natal, Dillalai, Durumi da kuma Hayin Kanwa, duk a cikin gundumar Yakawada.

“Sauran yankunan da harin ya shafa sun haɗa da: Kaya, Mai Kyauro da kuma Fatika. Sun kashe aƙalla mutane 50 da yin garkuwa da sama da 100.

“Sheɗancin su bai tsaya nan ba, haka suka yi yunƙurin kai hari a filin sauka da tashin jiragen sama na ƙasa da ke Kaduna. Duk da jami’an tsaro sun yi nasarar daƙile harin amma sun kashe mutun guda,” inji Sani.

Sanata Suleiman Abdu Kwari (APC Kaduna ta Arewa) da Sanata Ɗanjuma La’ah (PDP Kaduna ta Kudu) sun bayyana cewa hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa a wasu yankunan Jihar Kaduna a kullum rana ya zama kamar ruwan dare game duniya.

Shugaban Ƙungiyar Giwa Youth Concern, da ke taimaka wa jami’an tsaro da ‘yan gudun hijira, Kwamared Nuhu Haruna Al-Kurkawee, ya bayyana cewa Ƙaramar Hukumar Giwa ta zama tamkar masha jinin ‘yan ta’adda, inda suke cin karen su ba babbaka.

Al-Kurkawee ya lisaafa ƙauyuka irin su: Barebari da Dillalai da Durumi da Fatika da Ƙaya da Hayin Kanwa da Tsaunin Mayau da Zangon Tama 1 da Zangon Tama 2 da Kufan Ƙaura da Na’ikko a matsayin ƙauyukan da suka zama kufayi a yankunan.

Ya kuma ƙiyasta mutane sama da 300 waɗanda suka bar ƙauyukan su, suka fantsama biranen Giwa da Zariya da Funtuwa don yin gudun hijira.

 “Wasu an kashe musu iyaye da ‘yan uwa, an ƙona musu gidaje da hatsi, sun bar garuruwan su babu shiri.

“Zuwa yanzu akwai ƙiyasin mutane sama da 300 da suka yi gudun hijira. Saboda haka ne ma ƙungiyar mu take taimaka musu da kayan abinci da kuma tufafin sawa,” inji Al-Kurkawee.

Matakin Majalisar Wakilai ta Tarayya
Kamar yadda aka gwabza muhawara a Zauren Majalisar Tarayya kan ƙalubalen tsaron da ke addabar Nijeriya a ranar Talata, majalisar ta ce za ta zauna da shuwagabbin tsaro domin tattauna yanayin tsaron ƙasar nan.

Waɗanda majalisar ta ce za su zo gabanta akwai: Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Manjo-Janar Babagana Monguno (ritaya); Ministan Tsaro, Manjo-Janar Bashir Magashi (ritaya); Hafsan Sojin Sama, Air Mashal Isiaka Amao; Darakta Janar na Hukumar Tsaron Farin Kaya DG DSS, Yusuf Bichi; Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Usman Alkali Baba; Ministan Sufuri, Mista Rotimi Ameachi; Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika; Darakta Janar NCAA, Musa Nuhu,; Manajan Darakta, FAAN , Rabi’u Yadudu; Manajan Darakta, NAMA, Mathew Pwajok da kuma Janar-Manaja na Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa, Fidet Okhiria.

Mataimakin Kakakin Majalisa, Ahmed Wase wanda ya jagoranci zaman majalisar, ya ce Kwamitin Kula da Harkokin Jiragen Sama a majalisa da na Humar NSI da kwamitin kula da harkokin ‘yan sanda da na sojoji da na sojin sama da na tsaro da kuma na zirga-zirgar ƙasa su ne za su gudanar da zaman.

Wannan ya zo ne a daidai lokacin da shugaban kwamitin kula zirga-zirgar jiragen sama a majalisa, Nnolim Nnaji ya gabatar da wani ƙuri mai taken ‘Buƙatar gaggawa ga Gwamnatin Tarayya ta yi binciken harin da ‘yan bindiga suka kai a filin jirgin Kaduna da kuma ƙara tsaurara tsaro da sa ido a dukkanin filin jiragen ƙasar.’

A cikin ƙudirin nasa, Nanji ya tuno yadda ‘yan bindiga suka kai hari a gidajen ma’aikatan Hukumar Zirga-Zirgar Jiragen Sama (FAAN) da ke Kaduna, inda suka yi garkuwa da aƙalla mutane 12.

Me Jam’iyyar APC ta ce dangane da hare-haren?
Ɓangaren Jam’iyyar APC kuwa, sabon shugaban jam’iyyar  na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da a haɗe kai wuri guda sannan a yaƙi ‘yan ta’adda da ta’addancinsu a faɗin ƙasa.

Sanata Adamu ya yi wannan kiran ne biyo bayan harin da ‘yan bindiga suka kai wa jirgin qasan Abuja zuwa Kaduna.

 Cikin sanarwar da ya fitar Laraba, Shugaban APCn ya ce lokaci ya yi da ya kamata ‘yan ƙasa su haɗa kai wajen yaƙar maƙiyan ƙasa.

Daga nan, ya nuna alhininsa dangane da rashe-rashen da kuma raunukan da aka samu yayin harin tare da miqa ta’aziyyarsa ga ahalin marigayan.

A cewar Sanata Adamu, “Na yi Alla-wadai da wannan harin. Lamarin ya munana, kuma harin ya nuna yadda maƙiya za su yi dukkan mai yiwuwa wajen lalata ƙoƙarin da gwamanati ke yi wajen tabbatar da Nijeriya a matsayin ƙasa mai cikakken tsaro.

“Ina kira ga ‘yan Nijeriya su kalli wannan hari a matsayin aikin ‘yan ta’adda, mavarnata waɗanda ba su ƙaunar zaman lafiyar ƙasar nan.

“Dole ne mu dunƙule mu yaƙi waɗanda ke lalata cigaban ƙasa da kuma dimukraɗiyyarmu.”

‘Yan bindigar sun fara kiran iyalan waɗanda ak yi garkuwa da su
Yayin haɗa wannan rahoto, mun samu rahotanni da ke cewa ‘yan ta’addan sun fara tuntuɓar iyalan fasinjojin jirgin ƙasa da su kai garkuwa da su.

Iyalin wani daga cikin fasinjojin da ya ke hannun ‘yan ta’addan, mai suna Abdullahi, sun ce ‘yan fashin dajin sun tuntuɓe su ta wayar salula kuma sun ce musu su shirya biyan kuɗin fansa.

Punch ta rawaito cewa, wani Jibreel Khalil, ɗan uwan Abdullahi ɗin ya ce duk da ba su faɗi nawa za a ba su ba, amma dai ‘yan ta’addar sun kira sun kuma ce yana hannunsu, sannan a shirya biyan kuɗaɗen fansa.