Yadda IBB ya soke zaɓen shugaban ƙasa na MKO Abiola 1993: Amsar tambayar Mijinyawa Lawan

Daga SALIADEEN SICEY

Moshood Kashimawo Olawale Abiola GCFR, wanda aka fi sani da MKO Abiola ɗan kasuwar Nijeriya ne, mawallafi ne, kuma ɗan siyasa. A ɓangaren sarautar gargajiya kuma, shi ne Aare Ona Kankafo XIV na ƙasar Yarbawa.

Abiola sunan Najeriya ne na asalin Yarbawa. Ma’anar Abiola Shi ne “An haife shi cikin daraja/arziki’.

Marigayi Cif MKO Abiola na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) ya lashe zaɓen shugabancin qasa da aka yi a ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993.

An gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya a ranar 12 ga watan Yunin 1993, wanda shi ne na farko tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a 1983 ya kawo ƙarshen Jamhuriyya ta biyu a ƙasar. Zaɓen dai ya samo asali ne daga tsarin miqa mulki ga farar hula wanda shugaban mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya jagoranta.

Sakamakon zaɓen da ba a hukumance ba. Kodayake, hukumar zave ta ƙasa (NEC) ba ta bayyana ba. Ya nuna nasara ga Moshood Kashimawo Olawale Abiola na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), wanda ya doke Bashir Tofa na National Republican Convention (NRC).

Don haka, ba a tava bayyana wanda ya lashe zaɓen ba, domin kuwa IBB ya soke zaɓen, saboda kura-kuran da Gwamnatinsa ta ce an yi a zaɓen. Rushewar ya haifar da zanga-zanga da tashe-tashen hankula na siyasa, ciki har da murabus na IBB da kuma kafa gwamnatin riƙon ƙwarya ƙarƙashin jagorancin Ernest Shonekan, mai rauni. Hakan kuma ya kai ga cigaba da mulkin soja a ƙasar, inda Sani Abacha ya hau ƙaragar mulki a matsayin shugaban ƙasa na soja, ta hanyar juyin mulki ba tare da jini ba daga baya a cikin shekarar.

Masu sharhi a kan siyasa da al’umma da dama suna ganin babu wani zaɓe a tarihin Najeriya da ta ɗara wannan sahihanci. Sai dai tsohon shugaban ƙasan soji, Ibrahim Badamasi Babangida ya soke zaɓen a shekarar 1994. Abiola ya bayyana kansa a matsayin shugaban ƙasa. Hakan ya sa gwamnatin Janar Abacha ta garƙame. Marigayi MKO Abiola ya rasu a ranar 7 ga watan Yulin 1998 cikin wata yanayi mai ɗaure kai .

An haifi marigayi Cif Moshood Kashimawo Olawale Abiola ne a ranar 24 ga watan Augustan shekarar 1937, a garin Abeokuta. Kuma shi ne ɗa na 23 a wajen mahaifinsa. Abiola ya fara sayar da itace, daga nan ya koma tallan biredi. Sannan shi da wasu abokansa suka fara waƙa ana biyansu kuɗi. Wanda ya yi amfani da kuɗin don biyan kuɗin makarantarsa ta sakandire a Baptist Boys High School da ke Abeokuta.

Ya shiga siyasa yana da shekaru 19 a duniya, inda ya yi rajista da jam’iyyar National Council of Nigeria and the Cameroons (NCNC). A wannan lokacin kuma ya fara aiki a matsayin akawu a Bankin Barclays da ke Ibadan. Bayan ya yi ayyuka a wasu wuraren, ya garzaya ƙasar Scotland inda ya yi digiri a fannin Akanta kuma ya kammala da daraja ta farko wato (1st Class).

Ya dawo Najeriya ya yi aiki da kamfanoni da dama kuma ya rike manyan muƙamai a gida Najeriya da ma wasu ƙasashen Afirka. Abiola mutum ne mai kishin ƙasarsa sosai, hakan ya sa daga baya ya kafa kamfanoni da yawa tare da bayar da taimako ga marasa galihu wanda hakan ya sa ya yi farin jini sosai a tsakanin al’ummar ƙabilu da addinai daban-daban.

Kasancewarsa mai sha’awar siyasa, Abiola ya shiga jam’iyyar National Party of Nigeria (NPN) a shekarar 1980 kuma aka zave shi ciyaman din jiha aa jam’iyyarsa. An sake yin zaɓe a jam’iyyar a 1983. Hakan ya sa Abiola ya ƙara sanya rai cewa shi ne zai zama shugaban ƙasa. Sai dai kwatsam! Soji suka yi juyin mulki a Ranar 31 ga watan Disamba a shekarar 1983, wanda hakan ya hamɓarar da shugaban ƙasar demokraɗiyya Alhaji Shehu Aliyu Shagari.

Bayan kimanin shekaru 10 yana mulki, tursasawar da ake yi wa Janar Ibrahim Babangida na mayar da mulki ga farar hula ta yi tasiri. Abiola ya doke Ambasada Baba Gana Kingibe da Atiku Abubakar a zaɓen sharar fage, inda ya zama ɗan takarar jam’iyyar (SDP) a zaɓen 12 ga watan Yunin 1993. Saboda irin farin jini da yake da shi tsakanin al’umma wanda ta ratsa ko ina a Najeriya, kowa a Najeriya ya yi imanin cewa Abiola ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa da aka yi a 1993, inda ya doke abokin karawarsa, Bashir Tofa na jam’iyyar National Republican Convention (NRC).

Sai dai duk da cewa masu sanya idanu kan zaɓe na ƙasa da ƙasa da al’ummar ƙasa sun yi imanin cewa ba a taɓa sahihin zaɓe irin wannan ba a tarihin Nijeriya. Shugaban mulkin soji, Ibrahim Badamasi Babangida ya soke zaɓen ba tare da faɗin sakamakon zaɓen ba! inda ya yi ikirarin cewa an yi maguɗi da rashawa wajen gudanar da zaɓen. Hakan ya janyo rikice-rikicen siyasa, kuma bayan shekara ɗaya, Janar Sani Abacha ya karɓi mulki daga Shugaban rikon ƙwarya, Cif Enerst Shonikan. Duk da wannan hayaniya da ake yi, a shekarar 1994 Moshood Abiola ya yi gaban kansa ya ayyana kansa a matsayin halastaccen shugaban ƙasan Nijeriya bayan dawowarsa daga ƙasashen waje, inda yake neman haɗin kan ƙasashen don tabbatar masa da nasararsa.

Bayan ayyana kansa a matsayin shugaban ƙasa, Janar Abacha ya bayar da umurnin a kamo shi bisa laifin cin amanar ƙasa. An tsare Abiola a kurkuku da tsawon shekaru huɗu inda abokan hirarsa kawai sune Ƙur’ani da Bible, sai kuma masu gadinsa guda 14. Shugabanin addinai da shugabanin ƙasashen Duniya sun yi ƙoƙarin ganin Abacha ya sake shi, amma hakan bai yiwu ba. Gwamnatin sojin ta ce dole ya janye maganar da ya yi na ayyana kansa a matsayin shugaban ƙasa amma ya tsaya kan bakansa. Har ma an yi masa alƙawarin mayar masa da kuɗaɗen da ya kashe wajen kamfe.

Abiola ya rasu jim kaɗan bayan rasuwar Janar Abacha a ranar 7 ga watan Yulin 1998 da ake shirin sako shi a wani yanayi da mutane ke ganin kashe shi aka yi. Duk da cewa, binciken da gwamnati ta fitar ya nuna cewa ba kashe shi aka yi ba. Babban jami’in tsaron Abacha, Manjo Al-Mustapha ya yi ikirarin cewa, yana da faifan bidiyo da zai nuna cewa duka aka yi wa Abiola har ya mutu. Bayan mutuwar sa, an yi ta yi masa karramawa da bashi lambobin yabo kuma gwamnatin jihar Legas da Ogun tuni sun tsayar da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin hutu don tunawa da shi. Shi ma shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da canja ranar demokraɗiyya zuwa 12 ga watan Yunin da karrama marigayin tare da bashi lambar karramawa mafi daraja a Najeriya ta GCFR.

Saliadeen Sicey ɗan ƙasa ne mai sharhin a kan tarihi da al’amuran yau da kullum.