Yadda jarumai da mawaƙan Kannywood suka yi bajekolin su a taron makarantar Jammaje Academy

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano

Bikin Makarantar Jammaje na wannan shekarar da aka gudanar a karo na farko, wato Jammaje International Day, ya zo da sabon salon da ya ɗauki hankalin mahalarta taron a sakamakon yadda fitattun jarumai da mawaƙan Kannywood suka bajekolin su a wajen.

Taron wanda aka gudanar a ɗakin taro na Meena Event Center dake titin Lodge a cikin garin Kano ya samu halartar fitattun jarumai da mawaƙan Kannywood da suka daɗe a na damawa da su da kuma sabbin jini da tauraruwar su take haskawa a wannan lokacin.

Manufar taron dai na Jammaje International Day kamar yadda shugaban makarantar Malam Kabiru Musa Jammaje ya bayyana a lokacin Jawabin sa ya ce, “manufar shirya taron shi ne, zaburar da matasa wajen ƙoƙarin karatu da kuma nuna musu muhimmanci samar da aikin yi domin su zama masu dogaro da kansu, don haka ne muka gayyaci masana da kuma su kansu ɗaliban daga dukkanin rassanmu na jihohi in da za a bada bayanai kuma muna da burin za mu ci gaba da yin taron duk shekara.”

Ya ci gaba da cewa, “kasancewar samar da ilimi da kuma sana’o’i dogaro da kai ga matasa a yanzu wannan makarantar tana da rassan ta guda 29 a duk faɗin ƙasar nan, musamman a jihohi na Arewa wanda muke koyar da Turanci da kuma ilimi na wasu ɓangarori wanda kuma daga cikin darrusan da muke koyarwa har da harkar fim wadda tuni mun fara yaye ɗaliban da suka samu ilimi a fannin kuma muna ƙara faɗaɗa karatun don koyar da dabarun harkar fim, saboda ci gaban masana’antar finafinai ta Kannywood.”

Bayan kammala Jawaban dai an gabatar da waƙoƙi in da Mudassir Ƙasim ya cashe na tsawon lokaci.

Bayan shi kuma Abdullahi Amdaz Jarumi kuma mawaƙi shi ma ya cashe a wajen, sannan sai Bello Ibrahim Billy ‘o tare da Salisun Fati ‘yar Adamawa su ma suka gudanar da waƙoƙin.

Wani shashe na taron

Cikin jaruman Kannywood da suka haskaka wajen akwai fitaccen jarumi Abba Almustapha, Surayya Aminu Rayya ta ‘Kwana Casa’in’, Darakta Ishak Sidi Ishak. Sai kuma babban Jarumi Abdullahi A Abdullahi Abale wanda ya kasance an naɗa shi a matsayin jakadan makarantar ta Jammaje Academy a saboda kasancewar sa fitaccen jarumi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *