Yadda littafin ‘Marubuciya’ ya ƙalubalanci durƙushewar Adabin Kasuwar Kano

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Ga duk wanda yake da masaniya kan irin muhawarar da masana harshen Hausa da adabi suka tafka a farkon shekarun 1990, musamman ta cikin tsohuwar jaridar Nasiha da ake bugawa kowane mako, game abin da a lokacin aka kira, ‘Adabin Kasuwar Kano’. A lokacin ina iya tunawa ina ɗalibi amma na bibiyi muhawarar da aka yi tsakanin Farfesa Ibrahim Malumfashi, Farfesa Abdallah Uba Adamu, Farfesa Yusuf Muhammad Adamu, Ado Ahmad Gidan Dabino, Ibrahim Sheme, Muhammad Bashir Yahuza Malumfashi da sauransu, inda suka riƙa baje baiwar ilimi da basira dangane da tasirin littattafan soyayya na Hausa da suka fara buwayar Arewacin Nijeriya. Matasa, a wancan lokacin sun yi ta yayin karatun littattafai irin su ‘In Da So Da ƙauna’, ‘Idan So Cuta Ne’, ‘So Marururun Zuciya’, ‘Furucin Soyayya’, ‘Budurwar Zuciya’, da sauran ire-iren su, waɗanda akasari littattafai ne da aka buga su da jigo na soyayya domin isar da saƙon gyara kayanka ga matasa. 

Sai dai yadda aka riƙa buga littattafan daga baya ya zo ya buwayi masu nazari da masana harkokin adabi, da suke ganin marubuta na lokacin na neman sauka a layi, saboda salon rubuce-rubucen da suke yi yana tasiri a rayuwar matasa, har wasu daga cikin malamai na ganin wani salo ne na gurɓata tarbiyya. A ɓangaren marubutan kuma sai aka riƙa samun wasu da ke ganin kasuwanci suke yi da nishaɗantarwa, ba gyara al’ada ko tarbiyya ba. Wannan ne ya ja hankalin manazarta da har suka laƙabawa littattafan da muhawarar da ake yi a kansu da sunan, Adabin Kasuwar Kano. 

Ko da bayan an fitar da kashi na biyu na muhawarar da aka kira da, ‘Jana’izar Adabin Kasuwar Kano’, littattafan soyayya na Hausa sun cigaba da fitowa, duk da alamun durƙushewar da sha’anin kasuwancin littattafan ya fara nunawa. Marubuta irinsu Bilkisu Salisu Funtuwa, Balaraba Ramatu Yakubu, Hafsat Chindo Sodangi, Zuwaira Isa, Sadiya Garba Yakasai, Fauziyya D. Sulaiman da sauran su, sun fitar da sabon salo a littattafan da ake bugawa, waɗanda suka mayar da hankali ga tattauna matsalolin iyali da rayuwar mata. 

Marubuciya, Shamsuna S. Shamsuddin na daga cikin marubutan da suka yi shuhura a wannan lokacin, wajen rubuce-rubucen littattafai masu kare muradun mata da wayar musu da kai, kamar yadda marubuci Rufa’i Abubakar Adam yake so mu yarda kan cewa, an taɓa yin wata marubuciya haka daga Jihar Gombe da mata suka yi yayin karanta littattafanta. 

Labari ne da ya ɗauke mu shekarun baya, kimanin shekaru 20 da suka gabata, lokacin kasuwar littattafan Hausa na Adabin Kasuwar Kano ba ta gama mutuwa ba. A littafin mun ga yadda Sufeto Arewa da abokin aikinsa Kofur Barde suka yi ta zaga rumfuna da kasuwanni suna neman inda za su samu littafin ‘Auren Mijin Wata’ da marubuciyar ta buga, wanda suke sa ran samun amsoshin da suke nema wajen gano wanda ya yi mata kisan gilla a gidanta. Sai dai sakamakon mutuwar kasuwancin littattafan Hausa, sun sha wahala kafin a yi musu kwatancen shagon wani tsohon mai sayar da littattafai da ke bayan kasuwar Gombe, wanda a wajensa ne aka yi dacen samu. 

Littafin ‘Marubuciya’, wanda Rufa’i Abubakar Adam ya rubuta shi ne ya samu nasarar zama Gwarzon Shekara na 2024 a Gasar Tsangayar Gusau, kuma yana daga cikin littattafan da ake sa ran za su samu karɓuwa sosai wajen masu karatu cikin wannan shekara. Littafi ne da ya samu kyakkyawan tsari da salo mai jan hankali irin na ƙwararrun marubuta.

Labari ne game da wata marubuciya da ke soyayya da mijin wata, wanda harwayau tsohon saurayinta ne, tun kafin auren ta da tsohon mijinta na farko da Allah Ya yi wa rasuwa. Sai dai kasancewarta mace mai tsananin kishi, duk ƙoƙarin da ta yi na komawa wajen tsohon saurayin nata da dawo da soyayyarsu ta baya, haƙarta ba ta cimma ruwa ba, saboda ta kasa sassauta zafin kishin da take da shi na ƙin son zama da kishiya. Duk kuwa da basajan da matar tsohon saurayin nata ta yi mata don ganin ta shawo kanta ta amince ta auri mijinta, ko wani mai mata, a maimakon cigaba da zaman zawarci. Biyewa son zuciya da ruɗin shaiɗan ya sa wannan marubuciya yin alaƙa da wani maƙwafcinta, har kuma suka ƙulla haramtacciyar soyayya da ta yi sanadin yi mata ciki. Gano hakan da tsohon saurayinta ya yi ya sa shi fasa aurenta, abin da ya yi matuƙar girgiza rayuwarta, musamman bayan ta gano cewa duk saƙonnin da take aikawa masoyinta da ya je ƙarin karatu ƙasar Rasha, suna shiga wayar matarsa ne, wacce take tsananin tsana a zuciyarta. A ƙarshe dai zafin kishi ya rinjayeta ta je gidan tsohon saurayin ta tayar musu da gobara da nufin hallaka shi da iyalinsa bakiɗaya, a lokacin da shi kuma yake can ƙofar gidanta don fayyace mata manufarsa a kanta, amma matarsa da ɗanta sun rasu. 

Labarin dai ya saɓa da salon labarai da aka saba karantawa masu kyakkyawan ƙarshe. Littafin ‘Marubuciya’ bai zo da haka ba, domin kuwa ita kanta marubuciyar ba ta yi ƙarshe mai kyau ba. A ƙarshen labarin an gano gaskiyar abin da ya wakana da rayuwarta, kamar yadda ta rubuta cikin littafinta ‘Auren Mijin Wata,’ kuma aka gano wanda ya yi sanadiyyar kasheta.

Babu shakka labarin ‘Marubuciya’ ya tsaru sosai, kuma ya ƙayatar. Babu mamaki ma shi ya sa ya zama na ɗaya a Gasar Gusau wacce ake wa kallo gasar da ba duk marubuci ba, saboda tsaurin da take da shi. Na yabawa marubucin ƙwarai ganin yadda ya yi amfani da hikima da basira wajen warware duk ƙullin da ya yi wa labarin, wanda a farko mutum zai yi zaton za a samu kufcewar salo wajen kalmashe labarin, amma kuma a nazarina ban ga hakan ba. Duk yadda mai karatu yake tunanin ƙarshen littafin zai kasance, sai ga shi marubucin ya shammaci shi. 

Littafin mai shafuka 126 ya fara ne da gajeren babi da aka sa wa suna, Farkon Fari, aka kuma kammala da wani gajeren babin mai taken, ƙarshen ƙarshe. Sannan ga bakiɗaya littafin na da babi 9 ne, kuma a kowanne babi an masa take na musamman, wanda ba kasafai ake gani a sauran littattafan Hausa na yanzu ba.

Marubucin littafin ya yi ƙoƙari sosai wajen kiyaye ƙa’idojin rubutun Hausa, in ka ɗauke ýan kurakurai nan da can da ya shafi, sanya waƙafi ko aya. Ko kuma haɗewa da raba wata kalma, wanda za a iya cewa kuskuren rubutu ne na na’ura duba da kyakkyawan tsarin da aka yi wa littafin.

Littafin ya taɓo wasu muhimman batutuwa na rayuwa a matsayin darussa da ya kamata masu karatu su yi aiki da su, da suka shafi illar zafin kishi, biyewa zugar shaiɗan, illar aikata zina, kuskuren barin babbar mace ta zauna ita kaɗai ba tare da, wani muharraminta a kusa ba. Sannan littafin ya koya mana sanin muhimmancin rubutu wajen adana bayanai da ilimantarwa, ƙalubalen durƙushewar kasuwar adabi da talifin littattafai, da kuma muhimmancin nazarin harshen Hausa a matakin jami’a, saɓanin yadda wasu ke yi wa ɗaliban Harshen Hausa kallon ƙasƙanci.

Kodayake duk da waɗannan nasarori da labarin ya samu, ba za a rasa wasu kurakurai ba, nan da can. Dama kuma babu wani littafi da aka rubuta shi da zama cikakke ɗari bisa ɗari. Akwai alamun an yi amfani da Hausar Gombe ko kuma tasirin Hausar Baka ya nuna a cikin rubutu, kamar yadda a shafi na 103 a sakin layi na ƙarshe aka rubuta. 

Sifeta Arewa ya yi murmushi, “Idan na 

zama malamin jami’a waye kuma zai ke kama muku masu laifin.” An yi amfani da ‘zai ke’ a maimakon ‘zai riƙa wacce ta fi sauƙi wajen faɗa. 

A shafi na 55 an rubuta, “Don Allah ki tura mini Whatsapp mana nawa ya yi eɗpiry.” A maimakon ‘eɗpire’. Sannan a shafi na 106 an yi amfani da kalmar ‘sauƙo’ a maimakon ‘sauko’.

A yayin da ake samun ƙarin cigaba a harkar kasuwancin littattafan Hausa, musamman gane da bayyanar manhajojin sayar da littattafai na yanar gizo. Marubucin ya bayyana muhimmancin dawo da talifin littattafai na takarda, da rubutu mai inganci, domin raya adabi da cigaban harshen Hausa.