Yadda Ma’aikatar Jinƙai ta zaburar da naƙasassu

Daga WAKILINMU

Da ma tun daga farkon kafa Ma’aikatar jinƙai, Kiyaye haɗurra da Walwalar al’umma (FMHADMSD), a ƙarƙashin jagorancin Hajiya Sadiya Umar Farouq, ma’aikatar ta fi karkata akalarta ga fifita tallafa wa mutane masu buƙata ta musamman. A don haka take zaburar da su da ƙara musu ƙwarin gwiwa. 

A yayin da Shuga Muhammadu Buhari ya ƙirƙiro Ma’aikatar ta jin ƙai a ranar 21 ga watan Agustan shekarar 2019, an bayyana ainahin manufar ƙirƙirar tata. Wato don ba da tallafi ga waɗanda ibtila’iya rutsa da su, marasa gata, gajiyayyu, tare da fitar da miliyoyin ‘yan Nijeriya daga ƙangin talauci. 

Bayan naɗin Sadiya Umar Farouq a matsayin Minista ta farko saboda duba da irin tarihi mai kyau da ta kafa da samar da cigaba a matsayinta na tsohuwar Kwamishiniya ta Tarayya, a wannan lokaci aka mayar da hukumar kare ‘yan gudun hijira da makamantansu   (NCFRMI) da sauran wasu hukumomin aka mayar da su ƙarƙashin kulawar ma’aikatar.  

Hukumomin sun haɗa da Hukumar kare ‘yan gudun hijira da makamantansu (NCFRMI); Hukumar ba da agajin gaggawa (NEMA); Hukumar haramta Safarar mutane  (NAPTIP); Hukumar NEDC; Hukumar Kula da mutane masu masu naƙasa (NCPD); da kuma Ofishin Babban mai ba da shawara na musamman ga shugaban ƙasa a kan cimma muradun bunƙasar ƙasa (OSSAP-SDGs).

Shekaru 3 kacal a kan muƙamin, yanzu Ma’aikatar ana kwatancenta a matsayin ɗaya daga cikin ma’aikatu masu muhimmanci a ƙasar nan sakamakon dawwamammiyar mu’amalarta da marasa galihu, waɗanda ibtila’i ya faɗa wa, da tabbatar da rage raɗaɗin talauci musamman ma shigar da naƙasassu cikin shirin ba da tallafi  (NSIP) wanda ma’aikatar take kula da shi. 

Rahotannin binciken da Ƙungiyar lafiya ta Duniya (WHO) ta gudanar a shekarar 2011, sun bayyana cewa, a faɗin Duniya, kusan ƙiyasin mutane biliyan ne aka ce suke fama da lalurar naƙasa.

Sannan a faɗin Nijeriya ma akwai mutane fiye miliyan 15 da suke fama da lalurar naƙasa iri daban-daban.

Wanda suka haɗa da taɓin hankali, matsanancin ciwo da matsananciyar gajiya, rashin idanu da kunnuwa bi-biyu, lalurar ƙwaƙwalwa, Da sauransu. 

Kuma a cikin waɗancan mutane, wasu an haife su da naƙasa, wasu kuma kuma daga baya abin ya same su a rayuwa. A cikin yanayin rayuwa kuma a wajen aiki ko a gida, ko cikin taro, sukan fuskanci tsangwama da kyara a kan abinda ba su suka yi kansu ba. 

Ƙasashe da dama sun rungumin kyautatawa da kulawa da biya wa  waɗannan bayin Allah buƙatunsu ta hanyar kare musu haƙƙoƙinsu, ba su damar kulawar lafiya, ilimi, shi ya sa ita ma gwamnatin Tarayya take ta nanata cewa ba za a bar ta a baya ba a wajen zama ƙasa koma-baya ba wajen kyautata wa naƙasassu ba.  

Ayyukansu sun haɗa da sanya hannu a 23 ga watan Janairun 2019 da Buhari ya yi a dokar haramta cin zarafin naƙasassu. Don cika wa wajibcin Nijeriya na majalisar Dinkin Duniya a kan kare haƙƙin naƙasassu. 

Kuma da ma naƙasassu mutane ne da a kullum suke cikin tausayawar gwamnatin Tarayya. Domin iri tsangwamar da suke fuskanta. Domin kada su zama masu matacciyar zuciya da rashin ƙwarin gwiwa. 

A yunqurinta na fatattakar musu da talauci da rage musu raɗaɗi gwamnatin Tarayyar ta cikin sashenta na masu buƙata ta musamman tana ta ƙoƙarin ganin ta tallafa wa naƙasassu da kayan masarufi da kayan tallafi kuɗi kamar keke guragu, Babur mai ƙafa uku, sandan jagora, sandan guragu, injinan markaɗe, asaken zamani, kekunan ɗinki, balkaneza da sauransu.

Fiye da ƙungiyoyi masu zaman kansu masu kula da naƙasassu guda 750 gwamnatin ta ba wa kayan tallafi naƙasassun. 

Sannan ma’aikatar ta zaɓi naƙasasshe a matsayin mamban majalisarta kuma sakataren zartarwa na naƙasassu mai suna, James Lalu.

Haka zalika, sashen masu buƙatu na musamman ya gudanar da wata horas da masu kula da yara masu naƙasa a jihohin Adamawa, Kaduna, Lagos. Imo, Oyo, da Delta Wannan ya ƙara wa Malaman makaranta 71 masu kula da naƙasassu sun samu ƙarin ƙwarewa.  

Haka sashen ya horas da Makafi 48 dabarun noma a jihar Legas sannan ya biya kuɗaɗen fara sana’arsu. 

Haka zalika, ma’aikatar ta horas da naƙasassu a shirin horaswa na N-Build wanda aka horas da naƙasassu ‘yan Nijeriya 40,000 sana’o’in dogaro da kai. Inda aka koya musu sana’ar kafinta, gyaran mota, fulamba, da sauransu. Wakilinmu na jaridar BLUEPRINT da ya kai ziyarar gano da ido ya shaida cewa, akasari waɗanda suka rabauta da shirin mata ne, yara da manya. 

Minista Hajiya Sadiya ta halarci taron rufe horaswa da aka yi ranar 8 ga watan Yunin shekarar nan. Inda aka rarraba shaidar horaswa da kuma kayan aiki ga waɗanda suka kammala koyon aikin na tsawon watanni shida. 

Haka ma’aikatar tare da haɗin gwiwar ITF ranau 11 ga Oktoba ta tsara bitar horas da yara mata da manya masu kula da naƙasassu a Abuja. Inda naƙasassu 19 ne suka rabauta. Yayin da Mutane 12 aka ba su horo a kan aikin otal da wasu 7 da aka yi wa horo a harkar kwalliya. 

Kamar yadda kowa ya sani, akwai matsin tattalin arzikin da ya mamaye Duniya wanda Nijeriya ma ba ta zama bare ba. Don haka ma’aikatar ta tsara waɗannan shirye-shiryen don ganin ta ƙarfafa musu gwiwa sun tallafi kansu. Musamman mata naƙasasshe da suka fi kowa ƙalubale. Kasancewarsu da rauni matantaka, ga kuma na naƙasa. 

A ɓangaren Arewacin Nijeriya kuma, inda barar masu naƙasa ta zama ruwan dare. Amma ma’aikatar ta yi ƙoƙarin  shirya horaswa ga naƙasassu a jihar Kano ranar 18 ga watan Mayu na shekarar nan.

Inda aka gudanar na tsawon kwanaki 3. Inda ministar ta ce kowanne ɗaya daga cikin waɗanda suka amshi horaswar za a ba shi jarin Naira 100,000 a ƙarshen horaswar.

Akwai labaran nasarori da dama da aka samu daga naƙasassu da suka rabauta da shirye-shiryen ma’aikatar musammanma ta ɓangaren horaswa da tallafi da raba jari. 

Binciken da wakilinmu ya yi ya tabbatar da cewa, Nijeriya tana daga tsirarun ƙasashen Afirka da ta kafa hukumomi don kula da naƙasassu. 

Kodayake, ba kamar ƙasashen da suka cigaba ba, a Nijeriya har yanzu ba a daina muzgunawa da tsangwanar naƙasasshe ba. 

A wata tattaunawar da wakilinmu na Blueprint Manhaja ta ƙarshen mako, Daraktan zartarwa. Na hukumar tilasta dokoki Felicitas Aigbogun-Brai, ya yi tsokaci a kan yadda ake wariyar launin fata ga naƙasasshe kuma a ƙarshe yayi kira da gwamnati ya ɗauki mataki a kan haka.

Sannan ta ƙara faɗaɗa buƙatun naƙasasshe a yayin kasafta kasafin ƙasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *