Yadda maganin gargajiya ya yi sanadin mutuwar mutum 10 ‘yan gida ɗaya a Kwara

Daga WAKILINMU

Al’ummar ƙauyen Biogberu da ke yankin ƙaramar hukumar Baruten a jihar Kwara, sun faɗa wani hali na tashin hankali biyo bayan wasu ‘yan gida ɗaya su goma da suka kwanta dama ɗaya bayan ɗaya a ƙauyen sakamakon wani maganin gargajiya da suka kwankwaɗa.

Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna wannan al’amari mai gigitarwa ya faru ne ran Juma’a ta makon jiya.

Wata majiya mai tushe ta bayyana yadda lamarin ya faru, inda ta ce wasu ‘yan ƙauyen su biyu, Okosi Musa da Worugura Julin, su ne suka bai wa wata mata mai suna Pennia Bonnie maganin gargajiya a kan ta yi amfani da shi saboda da ciwon sawun da take fama da shi.

Aka ce daga nan sai su biyun suka umarci matar da cewa bayan ta yi amfani da maganin, ta tabbatar kuma ta bai wa sauran mutanen gida su ma su sha don hana cutar yaɗuwa a tsakaninsu.

Amma ko da suka yi amfani da maganin, baki ɗaya mutum goma da suka kwankwaɗi maganin haka suka yi ta mutuwa ɗaya bayan ɗaya.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da faruwar wannan lamari. Tare da cewa wani mai suna Ibrahim Bonnie ne ya kai wa ‘yan sanda labarin aukuwar hakan a Talatar da ta  gabata.

Okasanmi ya ƙara da cewa, tuni Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Mohammed Bagega, ya ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.

Ya ce a halin da ake ciki wasu mutum biyu da ake zargi kan badaƙalar sun shiga hannu kuma suna taimaka wa ‘yan sanda wajen bincike.

Okasanmi ya ce Bagega ya shawarci marasa lafiya a cikin al’umma da su riƙa  zuwa sanannun cibiyo a faɗin jihar don neman magani a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso don kauce wa aukuwar irin haka a gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *