Yadda magidanci ke ƙara rura wutar kishi a gidansa

Daga AMINA YUSUF ALI

Assalamu alaikum. Sannunku da jimirin bibiyar filinku na ‘Zamantakewa’, wanda yake zuwar muku kowanne mako daga jaridarku mai farin jini ta Manhaja.

Idan mai karatu bai manta ba, a makon da ya gabata mun yi magana a kan yadda rashin tausayi ya yawaita a tsakanin kishiyoyi, haka a makon da ya gabace shi, shi ma mun yi magana a kan yadda namiji zai ɗauki matakan samar da zaman lafiya a lokacin da zai ƙara aure. A wannan makon kuma, mun zo mu ku da bayani a kan yadda magidanta ke ƙara assasa kishi a tsakanin matansu. A sha karatu lafiya.

Da farko dai na san da yawa magidanta za su jinjina kanun bayaninmu na wannan mako. Wasu ma ba za su gaskata cewa magidanci yana iya rura wutar kishi tsakanin matansa ba. Amma maganar gaskiya hakan tana faruwa. Magidanta da yawa da saninsu ko ba saninsu suna taimakawa wajen sanya kishi ya ta’azzara tsakanin matansu.

Ba matansa na aure da yake tare da su ba, har ma tsakanin matar da ya aura da wacce yake nema da aure ko kuma wacce ya rabu da ita. Abinda yake faruwa shi ne. Shi namiji zai ga kawai kamar rayuwarsa yake yadda ya kamata. Amma wasu abubuwan da yake yi suna iya sosa wa wata daga cikin matansa zuciya. Misali mata ba wai mugun son haihuwar yara maza suke ba.

Amma irin yadda wani maigidan ko danginsa suke nuna rawar ƙafa idan an haifar musu yara maza, yana sa kowacce ta ji ta fi son haifar maza. Ya kamata a san fa shi zama magidanci ba kawai ka auro mata ka zube ba ne. Sai ka yi amfani da wasu hikimomi don samar da zaman lafiya a tsakaninsu. Rashin yin haka yakan sa su kauce hanya don ganin sun samo ka. Kuma ki kanka ka zama ba kwanciyar hankali. Wasu daga cikin abubuwan sun haɗa da:

  1. Bayyana fifiko ƙarara a tsakaninsu. Wasu mazan suna kuskure wajen nuna fifiko a kan wata matar ko ‘ya’yanta. Hakan yana matukar sosa zuciyar sauran kishiyoyinta. Duk mun san cewa da wuya mutum ya tara mata a ce bai fi son wata a zuciyarsa ba. Amma kuma kamata ya yi kada a nuna fifikon a fili. Wato kada ya nuna a kyautar da za ka yi mata ko ka yi wa yaranka. Hakan zai sa ɗaya matar ta ƙullace ka. Wata ma har karatu za ta yi wa yaranta na rashin adalcin da kake nunawa. Ta sa yaran naka ma su daina girmama ka a zukatansu. Kuma ko girma suka yi suka samu ɗaukaka kai kuma karfinka ya ƙare. Wannan rashin adalcin da ka nuna musu suna yara zai hana su tausaya maka da kai da kishiyar uwarsu har su tallafe ka. Haka kuma za haddasa wutar gaba a tsakanin ‘ya’yan matanka.
  2. Rashin nuna kulawarka gare su bakiɗaya: Ya kamata maza su sani zama da kishiya ba ƙaramin abu ba ne a wajen mata. Mata suna jurewa ne kawai saboda tsoron Allah. Kada ka zama mai kara ta’azzara shi a tsakaninsu. Ka nuna kulawarka ga kowaccensu ba tare da nuna wariya ba. Fifita wata kan wata a wajen kulawa shi zai sa su bazama bin malamai wasu ma har da bokaye don su samu. Ka ga sun kauce hanya kawai saboda kai. Ka zama mai yawan murmushi da tausasawa agare su. Kuma idan ka lura kulawar nan da za ka ba su ba ta da illa a gare ka. Kuma ba za ta ci maka sisin kwabo ba. Abu ma fi muhimmanci ma ita za ta sa soyayya ta ƙaru tsakaninka da matarka da ‘ya’yanta. Har su girma suna tuno kirkinka ga uwarsu. Kuma suna tausayinka tare da yi maka addu’a ko bayan ranka. Ka ga kamar zubin adashi ya zame maka kenan.
  3. Yi wa matarka faɗa da cin mutuncinta a gaban kishiyoyi: Wasu mazan sukan yi wa matansu faɗa kuma su ci mutuncinsu a gaban kishiyoyonsu. Wasu mazan kuma ba sa taka birki idan matansu sun cin mutunci ko wulaƙanta junansu. Wannan matsala takan sa kishiya ta raina ‘yaruwarta ta kasa girmama ta har a zauna lafiya. Ya kamata maza su san wannan girmamawar tsakanin kishiyoyi tana da matuƙar muhimmanci. Kuma tana taimakawa su samu zaman lafiya. Idan wata ta yi maka laifi kada ka wulaƙanta ta ko ba a gaban kishiyoyi ba ne. Ka bincika ka ji dalilinta na aikata haka. Idan kuma ta tabbata ta yi laifin ka yi mata faɗa da girmamawa ba kamar yadda za ka yi wa ‘ya’yanka ba. Kuma ka yi mata ita da kai ba sai wani ya ji ba. Hakan zai ƙara maka ƙima a idonta. Yi mata fa]a a gaban mutane zai sa ta yi maka bore wata rana. Kai kanka ya kake ji idan shugabanka a wajen aiki ko sana’a ya zo ya tozarta ka a gaban mutane? Idan gaban ‘ya’yanku ne ma, hakan zai gurɓata musu tarbiyya da tunaninsu.
  4. Rashin auro matar da ta dace mai ilimi: Maza idan suna neman aure suna mantawa da matsayin ilimin mace ko tarbiyyar gidansu. Sun fi duba kyawunta fiye da komai. Ba sa la’kari da rashin iliminta zai iya tarwatsa masu gida da ma zuri’arsu bakiɗaya. Idan ka auri wacce ba ta da ilimi kullum ka dinga nusasshe ta. Idan da hali ka sa ta koma makaranta domin mace mai ilimi tana da sauƙin kishi a kan wacce ba ta da shi. Kuma ta san iyakcin haƙƙinta. Ba za ta kalli wasu abubuwan da ka aikata a matsayin cin fuska ko rashin adalci a gare ta ba.
  5. Alamanta ta da kishiyarta idan za ka yi mata gyara: Wasu mazan suna da ɗabi’ar idan za su yi wa mace fa]a sai sun kamo sunan kishiyarta sun nuna ta fi ta a komai. Gaskiyar magana hakan na yi wa mata ciwo har su ji tsanar kishiyar tasu ta kama su. Ko kuma su ƙullaci mijin, su dinga ganin gyaran da ya yi musu don cin mutunci ne ba don Allah ba ne. Hakan zai sa ta yi watsi da gyaran da ka yi mata. Hakan kuma zai sa fitina ta kunnu a gidan tsakaninka da ita, da kuma tsakaninta da kishiyar tata. Maza su sani akwai dubban hanyoyi da za ka yi mata gyara ba tare da ka ha]a ta da kishiyarta ba.
  6. Rashin girmama matarka idan ta tsufa: Akwai wasu mazan da idan matansu suka manyanta sai su je su jajibo yarinya su aura. Auren ba laifi ba ne idan za ka yi adalci. Ka daure zuciyarka kada ka yi abinda tsohuwar matarka za ta ji a ranta ta zama gugar yasa a wajenka. Duk da ta manyanta, har yau tana buƙatar kulawarka. Har yau tana buƙatar ka dinga yi mata tuni cewa ita mace ce har yanzu. Idan ka juya mata baya, za ta watsar da kai ta ci gaba da hulɗa da ‘ya’yanta wa]anda sun riga sun kawo ƙarfi. A lokacin ba ta da abokin gaya wa matsalarta sama da ‘ya’yanta. Duk muzgunawar da kake mata yaranta suna gani kuma ita ma za ta faɗa musu don su kwantar mata da hankali. Hakan zai sanya tsanarka a zuciyar ‘ya’yanku da kuma tsanar amaryarka har ma da abinda za ta haifa. Ka ga a kan abu ƙalilan da za ka iya kiyayewa ka jawo hautsini a gidanka. Wata Amaryar ma har da ita da mijin za su ha]e kai a dinga muzguna wa uwargidan.
  7. Ba da ƙofa ga Uwargida ta cutar da Amarya: Wasu mazan da ba su yi ilimi ba suna ganin zarar sun ƙaro aure sun yi wa Uwargida laifi. Sai su yi ta ƙoƙarin ganin ba ta zarge su ba. Eh lashakka an yi mata laifi amma kada ka sa tsoronta sama da na Allah a zuciyarka. Ka auro ‘yar mutane, kada ka ba da ƙofa ga uwargida da ‘ya’yanta su ci zarafinta. Akwai iyayen gida marasa ilimi da imani da idan aka yi musu kishiya za su shiga muzguna mata ta kowacce hanya. Wai don ta gaji ta bar mata gidan. Har ma ta haɗa da ‘ya’yanta wajen ganin haƙanta ya cim ma ruwa. Wasu magidantan ba sa sanin hakan yana faruwa a gidajensu. Wasu kuma sun san da hakan amma sai su ƙyale a yi ta cutar ‘yar mutane. To ɗanuwa ka ji tsoron Allah. Ka tuna idan aka yi wa ‘yarka ko ƙanwarka ba za ka ji daɗi ba. Ka dage ka tashi tsaye ka tabbatar da kowanne ɓangare bai samu citarwa daga ɗaya ɓangaren ba.
  8. Nuna bambanci: Wasu mazan sukan yi wa wacce suke so kyauta ba tare da sun yi wa ɗayar ba. Wasu a abinci ma sai sun banbanta. Musamman idan kowacce girkinta daban. An san dole a banbanta mai ‘ya’ya dole nata ya fi yawa. Amma wasu sukan banbanta har kalar cima, da sutura, ko makarantar yara, da sauransu. Wasu ma har kyautar gidaje ko filaye yakan yi ga matar da yake so ko ‘ya’yanta. Hakan zalunci ne ko a musulunce, ko a al’adance. Kuma wadanda kake banbantawa kullum tsanarka da rashin tausaya maka ne kai da kishiyar uwarsu da ‘ya’yanta ne yake ƙaruwa a zukatansu.