
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Laraba, 26 ga watan Maris, 2025 ne aka gudanar da taron ƙaddamar da bugu na uku na fim ɗin raya manufofin shirin samar da ayyukan ci-gaba masu ɗorewa (SDG’s) a Nijeriya da kuma karrama jaruman da suka yi aikin fitar da shi.
Taron, wanda aka gudanar da a ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) na Nijeriya da ke Abuja, ya samu wakilci daga Fadar Shugaban ƙasa, jaruman finafinan Nollywood, Ministan Ma’aikatar Masana’antu masu Ƙirƙira, ƴan jaridu da sauran su.
A lokacin da ya ke jawabi a taron, Kodinetan MƊD a Nijeriya, Mohamed Malick Fall ya yaba da shirin tare da yin jinjina ga jaruman da suka yi aikinsa, inda ya ce ire-iren sa za su taimaka wajen isar da saƙon neman ci-gaba mai ɗorewa a ƙasa.
Ya ce, sun nuna yadda za a magance matsalolin rashin adalci, ƙarfafa wa al’umma gwiwa gami da faɗaɗa ayyukan tausayi da taimakekeniya acikin su.
Malick Fall ya bayyana cewa, yayin da ake ƙara kusanto gaɓar ƙarshe ta cimma manufofin SDGs a nan da shekarar 2030, ire-iren waɗannan shirye-shirye za su taimaka sosai wajen kai ga hakan.
Ya ƙara da cewa, finafinai suna da iko na musamman wajen fassara ƙalubalen da ke cikin al’umma masu tsauri ta yadda za a wayar da kansu da ilimantar da su, ya na mai yaba wa Nollywood a matsayinta na ɗaya daga cikin manyan masana’antu a duniya da ke kai wa ga miliyoyin mutane a Afirka da ma wasu nahiyoyi.
Har’ilayau, Kodinetan ya ce MƊD tana aikin inganta matasa a harkar wajen samar da shirye-shirye da za su isar da gamsassun saƙonnin akan fannonim da suka shafi rashin daidaito tsakanin jinsi, sauyin yanayi da talauci a mahanga ta samar masu da mafita ta dindindin.
A nata jawabin, mai taimaka wa Shugaban Ƙasa ta musamman akan harkokin SDGs, Princess Adejoke Orelope-Adefulire, ta jinjina wa tawagar shirya gajeren fim ɗin mai zangon mintina 15 da ke bayyana yadda harkokin ci-gaba ke fuskantar ƙalubale tare da samar masu da mafita.
Ta yi kira ga ƴan shirya fim masu tasowa, da su riƙa shirya finafinai akan kowane ɗaya daga cikin manufofin SDGs, inda ta ce ta hanyoyin nazari da haɗin-gwiwa da ƙirƙira ne za a samu damawa da kowa a yayin gina ƙasa.
Kazalika, ta jinjina wa ɗaukacin masu-ruwa-da-tsaki da suka taimaka wajen fitar da shirin inda ta ce ta haka ne za a samar da ci-gaba mai ɗorewa da gobe mai kyau a Nijeriya.