Yadda Majalisar Dattawa ta jijjiga tebur kan batun ciwo bashin Naira tiriliyan 12.41

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kwamitin Harkokin Kuɗaɗe na Majalisar Dattawa ya nuna cewa ba zai yiwu a zura wa Gwamnatin Tarayya ido ta ciwo bashin Naira tiriliyan 12.41 don a antaya su cikin Kasafin 2023 ba.

Shugaban Kwamitin ne Sanata Solomon Adeola daga Jihar Legas ya nuna haka a lokacin gabatar da rahoton Kintacen Kasafin 2023-2025.

Ya ce batun sai an ciwo bashin Naira tiriliyan 12.41 abin firgitarwa ne matuƙa. Ya ce ba zai yiwu ba, sai dai a lalubo wasu hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ga gwamnatin tarayya.

Ya ce Gwamnatin Tarayya ta ƙara azamar nemo kuɗaɗen shiga, sannan kuma a rage duk abin da ba shi da tasiri ko muhimmanci a cikin kasafin.

Abu na uku kuma a cewarsa shi ne a liƙe duk wata ƙofa ko hudar da maƙudan kuɗaɗen gwamnati ke salwanta.

Wannan cinikin biri a sama dai ya taso ne tun a ƙarshen watan Agusta, lokacin da Gwamnatin Nijeriya ce za ta ciwo bashin Naira tiriliyan 11 domin yin watandar ayyukan kasafin 2023.

Idan za a iya tunawa Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed ta bayyana cewa babu tsimi ba dabara Gwamnomatin Tarayya za ta ciwo wani sabon bashi na Naira tiriliyan 11 cur domin antaya kuɗaɗen ciki kasafin kuɗin 2023.

Ba a nan lamarin ya tsaya ba, Zainab ta ce kuma Gwamnatin Tarayya za ta sayar da wasu kadarorin gwamnati duk don a samu kuɗaɗen da za a yi ayyukan kasafin 2023 da su.

“Idan gwamnatin tarayya ta ci gaba da biyan tallafin fetur daga farko har zuwa ƙarshen 2023, to za a samu giɓin Naira tiriliyan 12.42 a cikin kasafin kenan.

Zainab ta yi wannan magana yayin da ta bayyana a gaban Kwamitin Harkokin Kuɗaɗe na Majalisar Tarayya, lokacin da ta ke kare hassshen kuɗaɗen da gwamnati za ta kashe cikin shekarun 2023-2025, (MTEF).

Zainab ta je wa ‘yan Majalisa zaɓi guda biyu, kuma kowane babu mai sauƙi a cikin su.

Na ɗaya ta ce ki dai a ci gaba da biyan kuɗaɗen tallafin fetur, amma kuma a ƙarshen shekara ta 2023 a yi asarar naira tiriliyan 12.41 da za a samu giɓin su a cikin kasafin kuɗi, saboda za ta biya tallafin fetur har Naira tiriliyan 6.72.

Zainab ta ce zaɓi na biyu kuma shi ne a ci gaba da biyan tallafin fetur har zuwa cikin watan Yuni, 2023, wanda hakan zai haifar da giɓin Naira tiriliyan 11:30, saboda Naira tiriliyan 3.3 kenan duk a biyan tallafi za su zurare.

Ta ce shawara ta farko ba lallai ba ne ta yi aiki, domin wahalar da ke tattare da tsarin. Na biyu kuma zai iya yiwuwa, amma sai gwamnati ta tsuke aljihu, kuma ta matsa ƙaimi kan kamfanoni da masana’antu na gwamnatin tarayya a cikin 2023.